Kurakuran da suka kamata a kaucewa lokacin layya

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Musulmai a faɗin duniya na bikin sallah sau biyu a shekara kuma babbar sallah ce ta biyu wadda aka fi sani da sallar layya.

Ana bikin sallar a watan Musulunci na Dhul Hijjah kuma yayin bukukuwan, akan yanka dabbobi domin yin koyi da Annabi Ibrahim.

Layya dai wajibi ne idan har mutum yana da halin yin ta.

Sai dai a kan samu kura-kurai yayin wanzar da wannan ibada ta layya a don haka ne muka ji ta bakin malamai game da sharuɗɗa da kuma ladubban yin layya.

Sharuɗɗan yin layya

Sheikh Dakta Idris Muhammad Muhammad, Limamin Masallacin Hanyar Kara a birnin Lafiya na jihar Nassarawa ya shaida wa BBC cewa daga cikin ƙa'idojin da aka gindaya akwai;

  • Dabbar ta kasance daga cikin dabbobi na gida kamar raƙumi ko saniya ko rago, tunkiya ko bunsuru ko kuma akuya. Sai dai malamin ya ce dabbar da aka fi son a yi layya da ita shi ne rago. "Wanda yake aikin Hajji kuma an fi son ya yi da raƙumi," in ji shi.
  • Dole dabbar ta kai shekarun da ake buƙata. Raƙumi shekara biyar ya shiga ta shida, saniya shekara biyu ta shiga ta uku, akuya ta cika shekara ɗaya ta shiga shekara biyu sannan rago ko tunkiya su cika wata shida. "Duk mutumin da ya yi layya da dabbar da take ƙasa da shekarun nan, layyarsa ba ta yi ba."
  • Dabba ta zama mai cikakkiyar lafiya. Ya ce Annabi Muhammad SAW ya ce a guji yin layya da wadda rashin lafiyarta ya bayyana ko wadda take ɗingisawa ko dabba mai ido ɗaya, ko ramammiyar dabba.
  • Ba a yin layya kafin sallar Idi. "Duk mutumin da ya yi layya kafin sallar idi ya tabbatar cewa nama kawai ya samu amma bai samu ladan layya ba." in ji malamin. Sai limami ya yi sallah, ya idar da sallah sannan a yi layya.
  • Dole dabba ta fuskanci alƙibla idan za a yi layya
  • A kyautata yankan ta hanyar amfani da wuƙa mai kaifi
  • A hutar da dabba, rai ya gama ficewa daga jikinta kafin a fara feɗewa.
  • Mai yin layya ya yanka dabbar da kan sa.

Me ya kamata a yi bayan layya?

A wata hira da BBC ta yi da Sheikh Mu'azzam Sulaiman Khalid, malamin addinin Musulunci a Kano ya ce bai kamata a ajiye naman layya ya wuce tsawon kwanakin shagulgulan sallar ba.

Ya ƙara da cewa yana daga cikin ladubban Sallar Layya a halarci Idi, sannan da zarar an sauko to a gaggauta yanka dabbar layya.

Sheikh Hussaini Zakariya, malamin addinin Musulunci a Abuja, babban birnin Najeiya ya ce wajen raba naman layyar, wasu malamai sun haɗu kan cewa a raba naman gida uku - ɗaya na iyali, ɗaya na ƴan'uwa da abokanan arziki sannan kashin ƙarshe sai a bai wa mabuƙata.

Sai dai kuma bai wa mabuƙata duka naman ko ma mutum ya ajiye naman da ya yi layya da shi duk abu ne da aka yarda a yi idan har ba a yi hakan don haɗama ko ƙin kyautatawa abokan zama.