Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alƙawura 6 da ƴansiyasar Najeriya suka gaza cikawa tun daga 1999
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Tun lokacin da Najeriya ta koma tsarin dimokraɗiyya a shekarar 1999, an samu shugabanni da dama da suka yi mulki, kuma an ga kamun ludayinsu. Kusan kowane shugaba idan yana neman a zaɓe shi, yana da alƙawuran da ya ke yi wa ƴan ƙasar.
Ko da yake kowanne ɗansiyasa yana da nashi manufofin, amma akwai wasu muhimman alƙawuran da kowane ɗantakara ke shan alwashin zai magance da zarar an ba shi damar.
Sai dai duk da an shafe shekaru 26 a tsarin dimokraɗiyyar ƙasar, akwai wasu manyan alƙawura da aka jima ana jin su daga bakunan ƴansiyasa a duk lokacin da kakar zaɓe ta zo.
Shugabanni biyar suka mulki ƙasar, kuma duk sun yi irin waɗannan alƙawura.
Haka nan an yi gwamnoni akalla uku-uku a kowacce daga cikin jihohin kasar 36.
A yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, an fara jin amon waɗannan alƙawura daga bakunan ƴan siyasar da suka kasa cika su, duk da matsalolin sun daɗe suna damun ƙasar.
Farfesa Babayo Sule na sashen nazarin tafiyar da harkokin al'umma da siyasa a jami'ar Namibia, ya ce an daɗe ana yi wa ƴan Najeriya irin waɗannan alƙawura ne saboda shugabannin sun gano lagon ƴan ƙasar da yadda za su ja hankalinsu.
"Abin da su ƴansiyasa suke yi shi ne, suna nuna wa mutane cewa waɗanda suke kai sun gagara kuma sun gaza, idan kuka zaɓe mu za mu cika," in ji shi.
Farfesan ya lissafo wasu muhimman alƙawuran da aka saba jin su kuma har yanzu ana gidan jiya.
Wutar lantarki
Najeriya ta daɗe tana fama matsalar wutar lantarki, inda gwamnatoci daban-daban suka sha ware maƙudan kuɗaɗe domin ganin an inganta ta, amma har yanzu ƴanƙasar na ƙorafi kan lamarin.
A shekarar 2005 ne aka cefanar da kamfanin wutar lantarkin ƙasar da aka fi sani da PHCN, wanda daga baya kuma ya koma NEPA, inda a shekarar 2013 aka kammala miƙa shi hannun ƴan kasuwa a hukumance.
Gwamnati ce ke kula da kamfanin rarraba wutar lantarkin ƙasar wato TCN.
Kamfanoni da ƙananan sana'o'i da dama sun dogara ne da injin janareta domin gudanar da harkokinsu, inda aka yi ƙiyasin ƙasar na asarar kusan Naira tiriliyan 40 a kowace shekara saboda rashin wutar lantarki.
Farfesa Babayo ya ce shugabannin sun mayar da lamarin "abin wasa da hankali", inda ya buga misali da cewa ko a baya-bayan nan shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin idan har bai samar wa ƴan ƙasar wutar lantarkin awa 24 ba, kada su zabe shi idan ya nemi a sake zaɓenshi a 2027, amma kuma bai cika ba.
Duk da makudan kudin da aka dade ana narkarwa a harkar ta lantarki, har yanzu kasar mai yawan mutane sama da miliyan 200 na samar da kargin lantarki ne kimanin megawatt 4000.
Tun daga shekarar 1999 bangaren na lantarki ya yi fama da munanan badakalar kudade, inda a ranar 13 ga watan Mayun 2026 wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki na kasar Saleh Mamman hukuncin dauri na shekara 73 bayan samun shi da laifi kan badakalar kudi akalla naira biliyan 22 da aka ware domin ayyukan wasu manyan tashoshin samar da lantarki a kasar.
Haka nan a shekara ta 2017, wani rahoto na kungiyar tabbatar da adalci a harkokin tattalin arziki da na yau da kullum (Serap), mai taken ‘From Darkness to Darkness…’ ya zargi gwamnatocin shugabannin kasar uku da suka gabata - Olusegun Obasanjo, Umaru Yar’adua da Goodluck Jonathan - da salwantar da kudi kimanin naira tiriliyan 11 kan batun lantarki a kasar, ba tare da bangaren lantarkin ya inganta ba.
Ilimi
Yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya sun kai aƙalla miliyan 20, a cewar Hukumar kula da ilimi da al’adu ta MDD (UNESCO), kusan kashi 7.3 zuwa 20 cikin 100 na yaran da ba su zuwa makaranta a duniya.
Dr Babayo ya koka game da yanayin da ilimi da makarantun ƙasar ke ciki musamman a yankunan karkara. Ya kuma ce malamai a ƙasar na cikin yanayi mara kyau, alal misali yadda suke yawan shiga yajin aiki.
Malaman makaranta na kokawa kan ƙarancin albashi da rashin ingantaccen tsarin da ilimi ke ciki a Najeriya.
Kusan kowane shugaban ƙasar, ya sha alwashin inganta fannin ilimi, sai dai "har yanzu lamarin na ci baya", in ji masanin.
Ko a kasafin kuɗin ƙasar, ba a cika ware wa fannin ilimi kaso mai tsoka ba, inda a shekarar 2026, aka ware Naira tiriliyan 3.52 (kashi 6.1) ga fannin.
Hukumar kula da yara ta MDD ta bukaci kasashe su rika ware kashi 15-20% na kasafin kudin su ma kowace shekara ga bangaren ilimi, sai dai har yanzu Najeriya ta gaza cimma hakan.
Karatu da makarantu a yankunan karkara sun tabarbare, musamman na gwamnati, inda mafi yawan iyaye masu hannu da shuni suka raja’a wajen kai yaransu makarantu masu zaman kansu, wadanda kuma ba a kowane lokaci ne ake samun sahihin ilimin da yara ke bukata ba.
A cikin wani rahotonta a 2022, Unicef ta ce ”miliyoyin yara a Najeriya ba su taba shiga aji da sunan neman ilimi ba”.
Tsaro
Lamarin tsaro a Najeriya na daga cikin abubuwan da suka addabi ƙasar, inda take matsayi na 147 daga cikin kasashe 163 da ke da zaman lafiya a duniya a 2025, inda ta zama ɗaya daga cikin ƙasashe mafi ƙarancin zaman lafiya da aikata manyan laifuka a duniya.
Ƴansiyasa kan mayar da hankalinsu wajen shan alwashin magance matsalolin tsaron da suka addabi sassa daban-daban. Daga cikin matsalolin tsaron da suka daɗe suna damun Najeriya akwai ƴan Boko Haram, ISWAP, Ƴanbindiga, Ƴan'awaren IPOB da na Neja-Delta da sauran su..
Matsalar tsaro a ƙasar ta raba mutane da dama da muhallansu, inda gwamnatoci daban-daban suke jaddada cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu na ganin bayan matsalar.
Ƴan adawa a ƙasar na matsa wa gwamnatoci lamba kan taɓarɓarewar tsaro a Najeriyar.
Farfesa Babayo ya ce a baya-bayan nan, matsalar tsaro na daga cikin manyan alwashin da ƴan siyasa ke ɗauka da nuna cewa za su iya magance ta cikin ƙanƙanin lokaci amma sun kasa cikawa.
A baya gwamnatin Umaru ‘Yar’adua ta yi kokari wajen shawo kan matsalar ‘yan fafutika na yankin Neja-Delta masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, sai dai bullar kungiyar Boko Haram ta masu ikirarin jihadi a shekarar 2002 a arewa maso gabashin kasar ya mayar da hannun agogo baya.
Kungiyar Amnesty International ta ce rikicin ya tarwatsa mutane sama da miliyan biyu lamarin da ya haifar da gagarumar matsalar jin-kai.
Haka nan bullar ayyukan kungiyoyin ‘yan bindiga a arewa maso yammacin kasar da kuma rikicin manoma da makiyaya a arewa ta tsakiyar kasar na ci gaba da haifar da asarar dimbin rayuka.
Yaƙi da cin hanci
Najeriya ce ƙasa ta 142 cikin 182 da ke fama da cin hanci, kamar yadda alƙaluman ƙungiyar Transparency International suka bayyana.
Cin hanci da rashawa na daga cikin matsalolin da suka yi wa Najeriya dabaibayi, kuma shugabanni da dama a Najeriya sun sha nanata cewa za su yaƙi cin hanci da rashawa, tare da tsaftace aikin gwamnati.
Sai dai an sha kama ƴansiyasar ƙasar da zargin almundahanar kuɗaɗen al'umma, inda aka yanke wa wasu hukunci yayin da ake ci gaba da bincikar wasu. An kuma sha ƙwato wasu kuɗaɗe da aka kai su ƙasashen waje.
Cikin matakan da shugabannin ƙasar suka ɗauka wajen yaƙi da cin hanci, har da kafa hukumomin EFCC da ICPC da ke yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta'annuti.
To sai dai masana na ganin cewa har yanzu lamarin ya zama tamkar jiya-i-yau.
Hanyoyi
Najeriya ta fi kowace ƙasa faɗin hanyoyi a Afirka ta Yamma, inda take da kusan kilomita 195,000, amma duk da haka ma'aikatar ayyuka ta ƙiyasta cewa kashi 15% zuwa 20% na waɗannan hanyoyin ne kawai suke cikin yanayi mai kyau.
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasar ta na danganta yawan hatsarin da ake samu da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da yanayin mara kyau da hanyoyin ke ciki inda direbobi ke haifar da asarar rayuka a ƙoƙarin kauce wa ramuka.
A lokuta da dama, shugabanni sukan tsara kammala hanyoyi ko buɗe ayyukan tituna a daidai da lokacin yaƙin neman zaɓe ya kusa.
Ƴantakara ma sukan yi alƙawuran samar da hanyoyi a wuraren da ba su da su, domin saka wa waɗanda suka zaɓe su.
Lafiya
Rahoton da hukumar Unicef ta fitar a 2025 ya ce Najeriya ce kasar da ta fi yawan yara ‘yan kasa da shekara 5 da suka mutu a shekarar 2023 a tsakanin kasashen yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka.
Haka nan ma cibiyar tabbatar da ka’idoji da dokokin kiwon aikin kiwon lafiya (Ched) ta ce Najeriya na cikin kasashe mafiya hadari ga mata masu juna biyu, a cikin wani rahotonta mai taken ‘Maternal Health and Reproductive Justice…’
Yanayin kiwon lafiya a Najeriya na cikin yanayi mara kyau, kama daga matakin farko da kuma manyan asibitocin ƙasar saboda rashin kyakkyawan yanayi ko ingantattun kayan aiki.
A wasu lokutan, ƴan siyasa na kai gudummuwar magunguna asibitoci ko kuma taimakon gaggawa ga marasa lafiya, domin nuna tausayinsu a lokacin da suke neman a zaɓe su.
Yawancin ƴan adawa na sukar gwamnati mai ci da yanayin da fannin lafiyar ƙasar ke ciki, tare da alƙawarin inganta komai idan aka ba su dama.
A mafi yawan lokuta shugabannin kasar da kuma masu kudi kan fita kasashen waje ne domin neman lafiya yayin da talakawa ke amfani da abin da ya samu a asibitocin kasar.
Me ya sa aka kasa cika alawuran?
A cewar Farfesa Babayo Sule na sashen nazarin tafiyar da harkokin al'umma da siyasa a jami'ar Namibia, shugabannin sun ƙi yin azama wajen cika alƙawarin ne saboda rashin dacewar waɗanda ake zaɓa da kuma yadda al'umma suke da rashin sanin matakan hukunta wanda ya saɓa musu alƙawari.
Ya ƙara da cewa amfani da siyasar kuɗi, addini, ƙabilanci da ɓangaranci na daga cikin dalilan da ƴan siyasar ke ganin za su iya amfani da su a duk lokacin zaɓe wajen jan hankalin masu zaɓen.
Farfesan ya ce rashin bin diddigi daga wajen al'umma da tabbatar da cewa kowane ɗan siyasa ya yi abin da ya faɗa, ya sa ba a maida hankali wajen yin abin da ya dace.
"Mutane har yanzu ba su da wayewar siyasa, ta yadda idan mutum ya yi alƙawari ya gaza za su kayar da shi domin ya zama darasi ga na baya," in ji shi.
Wasu alƙawuran da aka saba ji
Farfesa Babayo ya ce akwai wasu ƙarin alƙawuran da sun zama al'ada a wajen ƴan siyasa, kuma ba su da wata dabarar yadda za su cika su. Ya lissafo alƙawura irin su, inganta harkar noma, bunƙasa tattalin arziki, da masana'antu.
"To kullum dai a iya waɗannan ake, ƴan siyasa ba su da niyyar cika su".
Bugu da ƙari Farfesan ya ce ƴan siyasa na cika bakin samar da ayyukan yi ga matasa, domin jan hankalinsu su kaɗa musu ƙuri'a sakamakon yawan da suke da shi da tasiri a zaɓukan Najeriya.