Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/053/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 25 ga watan Mayun 2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Shugaban majalisar dokokin Senegal El Malick ya yi murabus

    Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Senegal, El Malick Ndiaye ya yi murabus daga muƙaminsa kwana biyu bayan korar firaminista Ousmane Sonko, lamarin da ya tayar da zargin cewa ana shirin ba Sonko damar komawa cikin majalisa da kuma neman sabon muƙami.

    A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Ndiaye ya ce matakin nasa ya samo asali ne daga “zurfin tunani” da kuma “la’akarin kishin ƙasa,” yana mai cewa akwai lokuta da muradin ƙasa ke bukatar fifikon gaskiya kan komai.

    Bayan murabus ɗinsa, an kira zaman majalisar dokoki da za a yi a ranar Talata domin shirya mayar da Sonko kujerarsa ta majalisa tare da zaɓen sabon Shugaban Majalisar.

    Sonko, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PASTEF, ya riga ya lashe kujera a zaɓen 2024 amma ya ajiye ta lokacin da ya zama Firaminista.

    Ƙasar Senegal na fuskantar sabon yanayin siyasa, inda ake ganin dangantaka tsakanin Shugaba Bassirou Diomaye Faye da Sonko na iya kawo canji ga ikon gwamnati, musamman ganin jam’iyyar PASTEF na da rinjaye a majalisa, abin da ke ƙara haifar da rashin tabbas kan yadda sabuwar gwamnati za ta gudanar da mulki.

  2. 'Sama da mutum 125,000 sun kamu da matsalolin fata a Gaza'

    Hukumar agajin ’yan gudun hijira ta Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce ta gano fiye da mutum 125,000 da ke fama da cututtukan fata da suka samo asali daga cizon ɓeraye da ƙwari a yankin da ke fama da rikici a zirin Gaza

    Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce tawagogin lafiyarta na ci gaba da feshin magungunan kashe ƙwari tare da tsabtace wuraren da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaune.

    UNRWA ta ce ƙarancin man fetur da magungunan feshi da tantuna da magunguna na ƙara tauye ƙoƙarin shawo kan matsalar.

    Ta kuma jaddada cewa yankin na buƙatar samun damar kai kayan lafiya da magunguna ba tare da takura ba domin rage yaɗuwar cututtuka.

    A halin yanzu, dubban Falasɗinawa da suka rasa gidajensu na ci gaba da rayuwa cikin tantuna, yayin da ake fargabar cewa rashin tsafta da cunkoso na ƙara haifar da yaɗuwar cututtuka.

  3. FRSC ta buƙaci matafiya su kauce wa hanyar Abuja-Kaduna saboda cunkoso

    Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps ta shawarci direbobin da ke tafiya ta hanyar Abuja zuwa Kaduna da su yi amfani da wasu hanyoyi domin kauce wa cunkoson da ke addabar babban titin a wannan lokaci na bukukuwan Babbar Sallah.

    Hukumar ta ce ana samun taruwar ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon yawan masu tafiya Sallah da kuma ayyukan gyaran hanya da ke gudana a wasu sassa na titin. Wannan hali ya sa motsin ababen hawa ya ragu musamman a yankin Katari zuwa Jere.

    A dalilin haka ne FRSC ta shawarci matafiya su yi amfani da wasu hanyoyi, kamar hanyar Kaduna–Kachia–Maraban Kubacha–Jere–Bwari–Dutse Abuja zuwa Abuja ko Kaduna saboda ƙaurace wa cunkoso.

    Ta ce waɗannan hanyoyi za su taimaka wajen guje wa cunkoso da rage shi da kuma inganta tafiyar ababen hawa a lokacin bukukuwa.

    Hukumar ta kuma bukaci direbobi su ci gaba da bin dokokin hanya, su guji tukin ganganci da satar hannu/hanya, tare da bin umarnin jami’an kula da hanya.

  4. An sauya masu tsaron shugaban ƙasar Kenya bayan kutsen wani matashi

    Hukumomin ’yan sanda a Kenya sun sanar da yi wa manyan masu tsaron Shugaban ƙasar William Ruto garambawul bayan wani mutum ya tsallake matakan tsaro inda ya kusta ya kai ga kusa da shugaban yayin taron jama’a a gundumar Kilifi.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Bamba, inda Shugaba Ruto ke yi wa jama’a jawabi daga kan dandali.

    Bidiyon da ya yaɗu ya nuna wani matashi riƙe da Littafi Mai Tsarki yana kutsa kai cikin jama’a kafin ya kai ga kusa da shugaban na ɗan lokaci kafin aka kama shi.

    Babban Sufeton ’yan sanda Douglas Kanja ya ce wannan lamari ne mai matuƙar muhimmanci kuma ba za a amince da shi ba, inda ya umarci a binciki yadda aka samu wannan gibi a tsarin tsaro.

    Hukumomi sun kuma amince cewa akwai matsala a daidaiton aiki da kula da taron jama’a.

    Bayan faruwan lamarin ne aka sauya shugabannin wasu rukunin tsaro na musamman ciki har da masu gadin shugaban ƙasa, sannan an kafa kwamitin bincike domin gano yadda aka samu wannan gazawa a tsaron taron.

  5. Ƙasashen DR Congo, Uganda da Sudan sun haɗa kai kan yaƙi da cutar Ebola

    Ministocin lafiya na ƙasashen DR Congo da Uganda da Sudan ta Kudu sun gana a Uganda a ranar Asabar domin ƙarfafa haɗin gwiwa kan dabarun daƙile cutar Ebola a iyakokin ƙasashen.

    Sun amince da haɗin kai wajen sa ido kan cutar da binciken masu ɗauke da ita da kuma musayar bayanai, yayin da aka saka Sudan a shirin duk da cewa ba ta sanar da ɓarkewar cutar a hukumance ba.

    A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, tawagogin agaji na ci gaba da aiki, inda aka kafa ɗakin gwaje-gwaje a Bunia da babban birnin lardin Ituri, lamarin da ya rage jinkiri wajen gwaje-gwaje.

    Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin tabbacin cewa mutum 101 sun kamu da cutar, yayin da aka gano kusan mutane 904 na cikin haɗarin kamuwa da cutar inda ake sa musu ido. Haka kuma, akwai wasu 1,817 da ake zargin sun yi mu’amala da masu dauke da cutar a cikin iyalai da al’umma.

    Haka kuma, ana zargin waɗanda suka mutu sakamakon cutar sun kai 119 zuwa ranar 23 ga Mayu, 2026.

    A halin da ake ciki, cutar ta bazu daga yankuna uku zuwa yankunan lafiya 11 a gabashin Kongo, yankin da ke fama da rikici da gudun hijira.

  6. Ba a kammala cimma yarjejeniya da Amurka ba - Iran

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Iran, Esmail Baghaei, ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi kan wasu batutuwa, amma har yanzu ba za a iya cewa an kammala cimma cikakkiyar yarjejeniya ba.

    Baqaei ya yi wannan bayani ne a martani ga maganganun jami’an ƙasar Amurka da ke cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar.

    Ya ce ɓangarorin biyu sun cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa, amma har yanzu akwai sauran abubuwa da ba a kammala ba.

    Ya kuma danganta rashin tabbas ɗin da ake ciki da saɓanin matsayi daga Washington da kuma tarihin rikice-rikice da ke faruwa a lokacin tattaunawa.

    Wannan na zuwa ne yayin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce tattaunawar tana ci gaba kuma ba ta tsaya ba.

    Shi ma shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an kusan cimma yarjejeniya,

  7. Ana fargabar farashin gas na girki zai ci gaba da tashi a Najeriya

    Ana fargabar farashin gas na girki zai ci gaba da tashi a Najeriya, yayin da ’yan kasuwa da masu amfani da shi ke fuskantar matsin lamba daga ƙarin tsadar kaya a sassan ƙasar.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar ’yan kasuwar iskar gas ta Najeriya (NALPGAM) ta bayyana damuwa kan ƙarancin gas na girki da kuma tashin farashinta a faɗin ƙasar, inda ya kai har naira 1,500 kan kilo guda daga naira 1,300 a wasu yankuna.

    Ƙungiyar ta ce matsalar ta samo asali ne daga ƙarancin wadata da tsadar farashin iskar gas ɗin a tashoshi da matsalolin sufuri, da kuma ƙarin kuɗaɗen gudanar da kasuwanci da ke ƙara tsananta yanayin.

    A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce ’yan kasuwa suna sayen tan 20 na gas kan sama da naira miliyan 25 zuwa miliyan 26, lamarin da ke haifar da hauhawar farashi ga masu saye a kasuwa.

    Ta kuma yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya ƙara jefa gidaje da ƙananan kasuwanci cikin wahala, tare da haifar da hauhawar farashin abinci da koma-baya ga manufofin makamashi a Najeriya.

  8. Yau ake fara aikin Hajjin shekarar 2026

    A yau ne aka fara aikin Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya a daidai lokacin da yankin ke fama da tashin hankali sakamakon yaƙin Iran.

    Hukumomin Saudiyya sun ce sama da mahajjata miliyan ɗaya da rabi daga ƙasashen waje ne suka isa ƙasar domin gudanar da ibadar bana, adadin da ya zarce na shekarar da ta gabata duk da rikice-rikicen a ke ci gaba a yankin.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa Saudiyya ta fuskanci wasu hare-hare tun bayan fara yaƙi tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila, abin da ya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin.

    Domin kwantar da hankulan mahajjata, ma’aikatar tsaron Saudiyya ta fitar da bidiyo da ke nuna na’urorin kariya na sararin samaniya da aka girke a kewayen birnin Makka.

  9. An kashe sojan Isra'ila a Kudancin Lebanon

    Sojojin Isra’ila sun ce an kashe wani sojansu yayin fafatawa a kudancin Lebanon.

    Isra’ilar ta kuma sanar da cewa wasu sojojin sun samu munanan raunuka inda aka kai su asibiti domin samun kulawar likita.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka kashe sojan ko kuma inda arangamar ta faru ba.

  10. Farashin mai ya faɗi saboda fatan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

    Farashin ɗanyen mai ya faɗi sosai yayin da kasuwannin hannayen jari na Asiya suka samu ƙaruwa, sakamakon fatan cimma yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce a ranar Asabar ana ci gaba da tattaunawa sosai kan yarjejeniya da Tehran, yana mai cewa za a bayyana cikakkun bayanai nan ba da jimawa ba.

    Sai dai washegari ya gargaɗi tawagar masu tattaunawarsa da kada su yi gaggawar cimma yarjejeniya.

    A safiyar Litinin a kasuwannin Asiya, farashin ɗanyen man Brent ya sauka da kashi biyar cikin ɗari zuwa dala 98.36 kan ganga guda, yayin da ɗanyen man Amurka ya ragu da kashi 3.5 cikin ɗari zuwa dala 91.50 kan ganga.

    Trump ya taɓa cewa yarjejeniyar za ta haɗa da sake buɗe mashigar Hormuz, amma bai bayyana ƙarin bayani ba.

    Mashigin ruwan, wanda ake bi wajen jigilar kusan kashi ɗaya cikin biyar na man duniya da iskar gas ya kusa daina aiki tun bayan fara faɗan a ranar 28 ga Fabrairu.

  11. Majalisar Iran ta fara zamanta na farko tun bayan fara yaƙi

    Majalisar dokokin Iran ta fara zamanta tun bayan fara yaƙi, inda ’yan majalisar suka halarci zaman a zauren majalisa karo na farko cikin fiye da kwanaki 80.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an gudanar da zaɓen shugabancin majalisar ne a yayin zaman.

    Tun bayan fara yaƙin Isra’ila da Amurka da Iran ne aka dakatar da zaman majalisar, inda aka gudanar da zama guda ɗaya kacal ta hanyar intanet

  12. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.