Ko za a iya raba siyasar Najeriya da dabanci?

....

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

An kwashe kwanaki ana ci gaba da faɗan daba a unguwannin Fagge da Mayanka da IBB a tsakiyar birnin Kano - jiha mafiya yawan al’umma a arewacin Najeriya - lamarin da rahotonni ke cewa ya yi ajalin wani babban jami'in tsaro a yankin.

A tsawon shekaru matsalar daba ta gagari kundila a jihar Kano, saboda yadda a kowace rana batun ke ƙara zama babbar barazana.

A farkon wannan watan ma an samu rahotonnin faɗan daban da ya yi sanadin kashe wasu mutum biyar a birnin na Kano a lokacin wani taron siyasa a jihar.

To sai dai lamarin ya fi kamari a duk lokacin da aka kaɗa kugen siyasa a Najeriya, inda ƴandaban kan riƙa cin karensu babu babbaka da sunan kare iyayen gidansu na siyasa.

A shekarar 2025 an samu rahoton yadda wasu ƴandaban siyasa suka auka wani wurin da jam'iyyar ADC ke gudanar da taronta a jihar Kaduna tare da tarwatsa al’umma.

Haka ma a jihar Jigawa wasu da ake zargin ƴandaban siyasa ne sun tarwatsa wani taron siyasa a garin Kafin Hausa na jihar Jigawa a shekarar ta 2025.

'Wasu ƴansiyasa na naɗa ƴandaba muƙamai'

Wasu ƴandabar siyasa

Asalin hoton, Getty Images

Daba - wani yanayi ne da gungun matasa kan dauki miyagun makamai suna far wa juna, ko kuma su rika far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Hakan na haifar da asarar rayuka da dukiya, kuma abu ne da ya zamo alakakai a yawancin jihohin arewacin Najeriya, kamar yadda matsalar ‘yan kungiyar asiri ya zamo alakakai a jihohin kudancin kasar.

Ana dai zargin wasu ƴansiyasar Najeriya da amfani da ƴandabar siyasar domin cimma burinsu na siyasa.

Matasa ne majiya ƙarfi da suka yi fice a aikata laifuka da shan miyagun ƙwayoyi da ba sa tsoron aikata kowane irin laifi ko da kuwa kisan kai ne.

Akan zargi ƴansiyasar da bai wa ƴandabar kuɗaɗe domin yi musu duk abin da suke so a harkarsu ta siyasa.

Akwai wasu zarge-zarge da ake yi cewa idan an kafa gwamnati wasu gwamnatocin musamman a matakan jihohi da ƙananan hukumomi, kan ware ofishi na musamman da zai riƙa kula da yandabar siyasar.

Sai dai a mafiya yawan lokuta ‘yan siyasa da gwamnatoci na musanta tallafa wa irin wadannan ‘yan daban, har ma wasu sukan yi ikirarin fito da tsare-tsaren tallafa wa irin wadannan matasa domin samar musu ayyukan yi.

Me ya sa siyasar Najeriya ta kasa rabuwa da dabanci?

Captain Abdullahi Bakoji Adamu, mai ritaya, Mai Sharhi Kan Harkokin Tsaro a Tarayyar Najeriya ya ce siyasar ƙasar ta cukaɗa da harkar dabanci, musamman yadda ƴansiyasa ke amfani da su wajen cimma muradunsu.

''A zahirin gaskiya akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ƴansiyasa da ƴandaba a Najeriya'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ƴansiyasar na amfani da ƴandabar a lokuta da dama domin samun abin da suke so a siyasarsu.

''Sukan yi mafani da su wajen tarwartsa taron abokan hamayya ko razana masu kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓe, musamman in suna tunanin ba za su yi nasara ba, ko ba su da karɓuwa wajen masu kaɗa ƙuri'a'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ƙara da cewa ƴansiyasar na amfani da ƴandabar wajen nuna ƙarfin iko, yana mai cewa hakan ne ma ya sa ake yawaitar samun rahotonnin tashe-tashen hankula a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Illar amfani da ƴandaba a siyasa

Bakoji ya ce illar amfani da ƴandaba a harkar siyasa ba ta misaltuwa, domin kuwa matsalar na shafar rayuwar al'ummar da ba su ji ba su gani ba.

''Idan siyasar ta wuce aka daina ɗaukar nauyin ƴandabar, sai kuma su fara aikata miyagun laifuka domin ɗaukar ɗawainiyar kansu'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa daga ƙarshe sai su ɓuge da sace-sace da sayar da miyagun ƙwayoyi ko ƙwacen waya, saboda ƴansiyasa sun daina ɗaukar ɗawainiyarsu.

Masanin tsaron ya ce babban kuskure ne idan aka kalli daba a matsayin ƙaramar matsalar.

''Harkar daba ce ke rikiɗewa zuwa ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma ƙungiyoyin ta'addanci'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ta yaya za a raba siyasar Najeriya da dabanci?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Capt. Bakoji mai ritaya ya ce cakuɗuwar siyasa da dabanci a Najeriya, ta kai matakin da raba su sai an yi da gaske.

''Za a iya raba su amma sai an yi da gaske wajen ɓullo da sabbin dokokin da za su magance hakan'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole sai an ɓullo da wata dokar da za ta haramta ko hukunta duk wani ɗansiyasa da aka samu da hannu ko alaƙa da ƴandaba.

''Sannan kuma a hana yawo da makamai a cikin gari, musammam lokacin tarukan siyasa'', In ji Capt. Bakoji mai rityaya.

Masanin tsaron ya ci gaba da cewa yana da kyau a ƙarfafa hanyoyin leƙen asiri domin gano masu ɗaukar nauyin ƴandabar domin hukunta su.

''A kuma samar wa matasa ayyukan yi a horas da su da kuma inganta tarbiyyar da kafa kotunan musamman domin hukunta masu aikata wannan laifi'', in ji shi.

Ya kuma ce yana da kyau jam'iyyun siyasa su daina amfani da matasa wajen cimma muradunsu.

''Su ma kansu jami'an tsaro su daina ɗaukar matsalar daba da cewa siyasa ce ke kawo ta, su ɗauki matsalar da muhimmanci, domin kawar da ita'', in ji shi.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa babbar hanyar maganace daba ita ce maganance ta’ammali da kuma safarar migayun kwayoyi.

Wani rahoton da jaridar PR Nigeria ta wallafa a watan Afrilun 2026 ya ambato wani rahoton hukumar ‘yansanda a jihar Kano na cewa kashi 70% na manyan ayyukan laifi da ake aikatawa a jihar, musamman fadan daba, na da alaka da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Rahoton ya ce shan miyagun kwayoyi ya kasance babban silar munanan fadace-fadacen matasa da ake samu a unguwannanin jihar ta Kano.

Hikumar ‘yansandan Najeriya reshen jihar ta sha nanata wa BBC cewa tana bakin kokarinta wajen maganace matsalar, to sai dai har yanzu lamarin na ci gaba da haifar da asarar rayuka