KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 25 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. An umarci jami’an ƴansanda su ɗauki mataki kan masu riƙe da makamai ba bisa ƙa’ida ba

    ....

    Asalin hoton, @PoliceNG

    Sufeto Janar na ƴanSandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci jami’an ‘yan sanda a faɗin ƙasar su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu da makamai ba bisa ƙa’ida ba.

    Ya ce jami’an su yi amfani da tanadin dokar aiki ta Force Order 327 wajen tunkarar masu laifi domin daƙile hare-hare da kuma dawo da zaman lafiya musamman a Jihar Benue.

    Disu ya bayar da umarnin ne a wani taron tattaunawa da ya yi da Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, a Makurdi, yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar sakamakon yawaitar kashe-kashe da hare-haren da ake fuskanta.

    Mahalarta taron sun bayyana damuwa kan hare-haren da ake kai wa tare da tambayar dalilin da ya sa wasu barazanar tsaro ke ci gaba duk da bayanan sirri da ake bai wa hukumomi.

    Sufeto Janar ɗin ya kuma buƙaci matasan jihar Benue su ƙara haɗa kai da ‘yansanda wajen tattara bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka.

    A nasa ɓangaren, Gwamna Alia ya sake kira da a kafa ‘yan sandan jihohi domin taimakawa wajen magance matsalar tsaro.

  2. Tinubu ya buƙaci likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje su dawo gida

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga likitocin Najeriya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke aiki a ƙasashen waje da su dawo gida domin bayar da gudunmawarsu wajen inganta harkokin lafiya a ƙasar.

    Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Ƙungiyar Likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje tare da shugaban Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a Abuja.

    Ya ce Najeriya na buƙatar ilimi, ƙwarewa da gogewar ‘yan ƙasar da suka yi fice a ƙetare domin gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai amfani kowa da kowa.

    Shugaban ya yaba wa likitoci ƙasar bisa ayyukan jin ƙai da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka samar da ayyukan jinya, tiyata, shawarwari kan lafiya da sauran tallafin ceton rayuka.

    Ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren lafiya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙwararrun ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje domin rage ƙaurar ƙwararru da bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya.

  3. Iran ta fitar da gangar ɗanyen mai miliyan 73 a wata ɗaya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta samu damar fitar da kusan gangar danyen mai miliyan 73 daga yankin da takunkuman Amurka suka yi wa katanga cikin kusan wata guda, bayan da Washington ta ɗan sassauta wasu takunkumai da ƙuntatawar da ta sanya kan sayar da man ƙasar.

    Daga ƙarshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, jiragen dakon mai na Iran da dama sun fara bayyana a ruwan gabashin Malaysia suna kan hanyarsu zuwa kasuwannin Asiya.

    Kamfanin Kepler mai bibiyar jigilar makamashi ya shaida wa BBC cewa man da aka fitar a wannan lokacin na iya kai wa darajar kusan dala biliyan shida.

    Sai dai duk da wannan gagarumar fitar da mai, rahotanni sun nuna cewa manyan masu sayen man Iran a China sun rage sayayyarsu.

    Sai dai Amurka ta janye sassaucin takunkuman da ta yi wa Iran a ranar 7 ga Yuli, bayan ta amince na ɗan lokaci da sayar da ɗanyen man ƙasar tun daga 21 ga Yuni."

  4. Iran ta ce za ta kare kanta daga barazanar Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta bayyana cewa ta ƙuduri aniyar kare muradunta da tsaron ƙasarta tare da hana Amurka amfani da Mashigar Hormuz wajen yin barazana ga tsaronta.

    Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a gefen taron Majalisar Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO) da ake gudanarwa a Kyrgyzstan.

    A cewar kafofin watsa labaran Iran, Araghchi ya ce rashin tsaron da ake fuskanta a yanzu a Mashigar Hormuz “sakamako ne kai tsaye na karya alƙawarin da Amurka ta yi.”

    Ya ƙara da cewa Iran ta nuna muhimmancin diflomasiyya a harkokin ƙasa da ƙasa, amma a lokaci guda za ta ci gaba da kare muradunta da tsaron ƙasarta daga duk wata barazana.

    A wani ɓangaren kuma, Araghchi ya tattauna ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen Masar da Oman a ranar Alhamis kan abubuwan da suka shafi yankin.

  5. Assalamu alaikum

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Asabar.

    Aisha Babangida ke sake fatan kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za kuma ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.