Abin da BBC ta gani a makarantar da aka kashe ɗalibai 120 a Iran

- Marubuci, Nawal Al-Maghafi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior international investigations correspondent
- Aiko rahoto daga, Minab, southern Iran
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
GARGAƊI: Wannan rahoton na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali game da mutuwar ƙananan yara.
Amaineh Nademi na tafiya a hankali cikin abin da ya rage na tsohuwar makarantarta.
Manyan ɓuraguzan siminti suna reto daga saman benen da ya lalace. Har yanzu akwai wasu azuzuwa da ba su lalace ba tare da bangon da aka yi wa ado da zanen balan-balan da furanni masu launuka.
Malamar mai shekaru 33 ta san yadda makarantar take a baya – azuzuwan 'yan mata akan bene, na yara maza a ƙasa, da kuma ofishin shugaban makaranta da ɗakin ibada.
Yanzu kuwa, tarkace ne kawai suka rage a ajin nata, inda take koyar da 'yan mata ƴan aji ɗaya a makarantar firamare ta Shajareh Tayyebeh da ke Minab, wani ƙaramin birni a kudancin Iran.
A ranar 28 ga Fabarairu, a farkon sa'o'in yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran, wani hari da aka kai makarantar ya zama mafi munin bala'o'in yaƙin – kuma mafi muni ga fararen hula.
A cewar ofishin mai gabatar da ƙara na Minab, an tabbatar da mutuwar mutum 156, ciki har da yara 120, da wata mata mai juna biyu tare da jaririnta da ke cikinta.
Masana sun ce shaidu na nuna cewa sojojin Amurka ne suka kai harin makarantar, wadda ke kusa da wani sansanin IRGC (Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci), wanda hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna an kai masa hare-hare sau da dama.
Amurka ba ta amince da alhakin harin ba, duk da cewa wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa masu binciken soji sun yi hasashen cewa sojojin Amurka ne suka kai harin ba da gangan ba.

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
Raɗaɗin abin da ya faru har yanzu yana ran jama'a. Malamai sun ce suna zuwa wurin suna yin addu'a a kullum. Masu ceto kuma har yanzu suna ci gaba da neman ragowar gawawwakin waɗanda aka kashe.
Mafi yawan benaye sun rushe.
"Ba za ka kira wannan makaranta ba," in ji Amaineh. "Katangu ne kawai da ke warin matattu, tare da damuwar jinin da aka zubar a nan."
Mahukuntan Iran sun nuna sha'awa BBC ta ziyarci makarantar, suna cewa hujja ce da ke nuna cewa abin da Washington ta bayyana a matsayin hari kan cibiyoyin soja da tsaro na Iran ya haifar da mummunan sakamako ga fararen hula.

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
'An watsar da mu zuwa sama'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amaineh ta ce an bude makaranta ranar kamar yadda aka saba.
Saboda watan Ramadan ne, yaran sun taru a ɗakin ibada domin karatun Alƙur'ani kafin ta fara koya musu sabon darasin haruffan Farisanci.
Amma yayin da hare-haren farko na yaƙin suka fara a faɗin Iran, shugaban makaranta ya sanar da cewa za a rufe makarantar, kuma malamai suka fara kira ga iyaye su zo su ɗauki yaransu.
Daga cikin ɗalibanta 15 na aji ɗaya, biyar ne kawai suka rage a ajinta da ke kan bene lokacin da ta fara jin ƙarar fashewa kusa da makarantar.
Ta ce tana hanya da ke tsakanin azuzuwa lokacin da ta ji ƙarar, sai ta koma cikin aji domin ɗauko yaran.
"Yayin da nake shirin fita, wani makami mai linzami ya bugi makarantar," in ji Amaineh. "Wani abu ya bugi kaina da kawunan ɗalibaina, kuma dukanmu muka yi sama."
Daga nan kuma wani baƙin hayaƙi mai kauri ya cika ajin.
"Ba na ma iya ganin yaran da nake riƙe da su a hannu. Ba ma iya numfashi."
Ta ce tana tuna wata ƙara ta biyu ta fashewa, kururuwar yara da kukansu, sannan makarantar ta rushe gaba ɗaya.
"Jini yana ta zuba daga jikina da na ɗalibaina," in ji ta.

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
Lokacin da hayaƙin ya ɗan lafa, ta ce ta miƙa yaran da suka ji rauni ga mutanen da ke ƙasa kafin ta yi yunkurin fita ta cikin wuta da tarkace zuwa ƙofar makarantar, inda ta tarar da iyaye da yawa.
Ta ce wasu daga cikinsu ma sun zo ba takalmi saboda gaggawa.
A firgice, ta yi tunanin kowa ya tsira daga ginin.
"Ban san cewa duk suna ƙarƙashin tarkace ba," in ji ta.
Amaineh ta yi shekara shida tana koyar da aji ɗaya a makarantar.
Ta lissafa sunayen ɗalibai da abokan aikinta da suka mutu a ranar, ciki har da Adrina daga ajinta, Fatemeh daga aji biyu, da wasu da dama, tare da shugaban makaranta da mataimakiyarsa da malamin motsa jiki da kuma malamin Alƙur'ani.
'Ku nemo mini ɗana'
Cikin mintuna kaɗan, jami'an agaji suka isa wurin.
Reza Besharati, ma'aikacin Kungiyar Agajin Gaggawa ta Red Crescent ta Iran, ya ce yana cikin masu ceton farko da suka isa.
Ya tarar da hanyoyin da ke kusa da makarantar sun cika da motoci yayin da iyalai ke neman yaransu.
Minab ƙaramin birni ne, kuma yayin da Reza yake kutsawa cikin taron mutane zuwa wurin da lamarin ya faru, ya gano wasu daga cikin waɗanda ya sani har da danginsa.
"Mun fara neman mutane muna tunanin wataƙila akwai wanda yake raye," in ji shi. "Amma abin takaici babu ko ɗaya."

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
Ya ce gawarwakin sun lalace sosai.
"Wataƙila hannu kawai za ka gani, ko ƙafa kawai... Babu wanda jikinsa ya cika."
Ya ƙara da cewa iyalai da yawa sun gane yaransu ne ta hanyar takalma ko tufafinsu.
Wata daga cikin 'yan uwansa tana ta roƙo tana cewa:
"Don Allah ku nemo mini ɗana."
"Ba zan iya gaya mata cewa ɗanta ya mutu ba. Kowa kuka yake yi," in ji Reza.
Ya ce abubuwan da ya gani ba su bar shi ba.
"Na kasa yin barci a tsawon kwanaki. Duk lokacin da na rufe idona, waɗannan abubuwan nake gani."
Ana binciken harin
Bayan bayanai game da harin sun fara bayyana, Shugaban Amurka Donald Trump ya fara zargin Iran ba tare da gabatar da wata hujja ba.
Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya ce ana gudanar da bincike, kuma "sojojin Amurka ba sa kai hari kan fararen hula."
Daga bisani ya sanar da wani babban bincike ƙarƙashin wani jami'i daga wajen CENTCOM.
Har yanzu gwamnatin Trump ba ta fitar da sakamakon binciken ba.
Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa binciken farko ya nuna yiyuwar tsoffin bayanan sirri daga Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Amurka ne suka sa aka ɗauki makarantar a matsayin wani ɓangare na wurin soja.
Binciken masana kan bidiyo ya nuna cewa an kai hari sansanin IRGC da ke kusa da makarantar da makamin Tomahawk mai sarrafa kansa, wani nau'in makamin da ba a san Isra'ila ko Iran suna da shi ba.
Hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa makarantar da wasu gine-gine a sansanin sun samu hare-hare.

Binciken bidiyo da masana suka gudanar ya nuna cewa an kai hari sansanin IRGC da ke kusa da makarantar da makamin Tomahawk mai sarrafa kansa, wani nau'in makamin linzami mai shawagi wanda ba a san Isra'ila ko Iran suna da shi ba.
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna cewa makarantar da wasu gine-gine a cikin sansanin sun fuskanci hare-hare, yayin da bidiyoyin da aka tantance suka tabbatar da cewa an kai jerin hare-hare a yankin.
Taswirorin sojojin Amurka ma sun tabbatar da cewa a lokacin, Amurka na gudanar da ayyukan soja a kudancin Iran, ciki har da yankin Minab.
Tsofaffin hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna cewa yankin makarantar ya kasance wani ɓangare na sansanin IRGC a baya, amma tun shekarar 2016 an kewaye shi da katanga kuma yana da ƙofofi da harabobinsa na kansa.
Har ila yau, bayanan da ke nuna cewa wurin makaranta ce sun kasance a fili a intanet.
Littafin da aka adana na shafukan yanar gizon sashen 'yan mata da na yara maza na makarantar – da aka ɗauka watanni kaɗan kafin harin – sun ƙunshi adireshin wurin.
Shugaban CENTCOM ya shaida wa wani kwamitin majalisar dokokin Amurka a watan Mayu cewa binciken yana da "sarƙaƙiya", saboda makarantar tana "kan wani sansanin makaman linzami mai shawagi na IRGC da ke aiki".
Bai bayar da ƙarin bayani ba. Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da wannan zargi, tana mai kiran sa "ƙirƙira marar tushe."
Bayan manyan ayyukanta na soja, tsaro da tattalin arziƙi, IRGC tana kuma gudanar da wasu cibiyoyin al'umma da na lafiya.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC Persian cewa wurin ya taba zama sansanin rundunar ruwa ta IRGC, amma sun yi imanin cewa an daina amfani da shi wajen harkokin soja shekaru da dama da suka gabata.
Hotuna sun nuna cewa daga cikin gine-ginen da ke wurin akwai asibiti da wurin wanke motoci.
BBC ta tuntubi Ma'aikatar Tsaron Amurka da rundunar sojin Amurka domin jin ta bakinsu. Jami'ai sun bayyana cewa binciken har yanzu yana gudana, kuma ba su da wani sabon bayani da za su bayar a halin yanzu.
'An gane ta ne da safa'
Ba da nisa ba daga makarantar da ta lalace, akwai maƙabarta inda aka binne yawancin ɗalibai da malamai.
A kowane maraice iyalai sukan taru a kusa da ƙaburbura.
Iyaye mata suna share ƙura daga hotunan 'ya'yansu, yayin da wasu ke zaune suna addu'a har dare ya yi.

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
Masoumeh Mehran Shekhabadi kan ziyarci kabarin 'yarta Setayesh mai shekaru tara a kullum.
Ita ma tana cikin iyayen da suka ruga zuwa makarantar bayan harin.
"Babu makaranta," in ji ta cikin kuka. "Hayaƙi ne kawai, gashin yara, hannu a gefe guda, ƙafa na can. An tarwatsa su gaba ɗaya."
Ta ce ta yi ta kira:
"Yara, ina kuke?"
Iyalan Setayesh ba su sami tabbacin mutuwarta ba sai da asubahin washegari.
Masoumeh ta ce an dinga tambayarta launin safa da yarinyar tasa.
Ta saka safa mai launi
"An gane Setayesh ne ta hanyar safarta."
Ta ƙara da cewa 'yarta na mafarkin zama malama.
"Ta kan jera ƴar tsananta a kan kujera tana cewa: 'Ni malamarku ce. Ina makarantar firamare yanzu, don haka ni malama ce.'"

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
'Sun tafi ne domin koyo'
Gwamnatin Iran ta sha ambaton Minab a jawabai da tarukan ƙasa da ƙasa, har ma ta sanya wa wani jirgin da ya ɗauki masu tattaunawa suna "Minab-168", bisa adadin waɗanda aka ce sun mutu a baya.
Har ila yau, harin ya ba gwamnatin Iran damar ƙarfafa hujjarta kan cewa farmakin ya shafi fararen hula.

Asalin hoton, JACK GARLAND / BBC
Yaƙin ya raba kan Iraniyawa. Wasu sun yi murna lokacin da hare-haren sama suka fara, saboda sun fusata da tarihin gwamnati na kama masu adawa da ita da kuma amfani da ƙarfin da ke kashe mutane yayin zanga-zanga.
Sun yi fatan cewa matsin lambar soja daga waje zai iya raunana gwamnati ko ma ya kawo ƙarshenta.
Wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin sun shaida wa BBC cewa sun ɗauki harin da aka kai a Minab a matsayin babban koma baya.
A cewarsu, hakan ya sa ba zai yiwu a ci gaba da kallon yaƙin a matsayin wanda aka tsara daidai ba tare da shafar fararen hula ba, kuma ya bai wa mahukunta damar gabatar da kansu a matsayin masu kare al'ummar Iran daga hare-haren ƙasashen waje.
A Minab, Amaineh kan ziyarci makabarta, tana yawo tsakanin kaburburan tsoffin ɗalibanta.
A wani bangon tunawa da ke kusa, an rataye hotunan yara, ma'aikata da iyayen da suka fita daga gidajensu a safiyar Asabar amma ba su sake dawowa ba.
Har yanzu mahaifiyar Setayesh tana zama a gefen kabarin ƙaramar 'yarta.
"Menene laifin waɗannan yara? Sun ɗauki makamai ne? Alƙalami, littafi, takardu da jakar makaranta ne kawai suka mallaka. Ba su da makami ko kaɗan... Sun tafi ne domin su yi karatu," in ji ta.









