Dadasare: Macen da ta fara aikin jarida da asibiti a arewacin Najeriya

Dadasare

Asalin hoton, Aliyah Adamu Ahmad

Bayanan hoto, .
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Babu tabbacin ranar da aka haifa Hajiya Maimunatu Abdullahi, wadda ake kira da suna Dadasare.

Amma a littafin rayuwarta, wanda Farfesa Aliya Adamu Ahmad ta Jami'ar Jihar Sokoto ta jagoranci wallafa, marigayiyar ta bayyana cewa tana hasahen an haife ta ne a tsakankanin shekarar 1918 a garin Gola da ke arewa maso gabashin lardin Adamawa a arewacin Najeriya.

Domin sanin cikakken tarihinta, BBC ta zanta da Farfesa Aliya, tare da nazartar littafin tarihin marigayiyar, wanda da kanta ta rubuta, amma Aliya tare da gudunmuwar Dr Ibrahim Sheme suka gyara tare da jagorantar wallafawa.

A cikin littafin mai suna 'It can now be told,' an bayyana cewa sunan mahaifin Dadasare Dewa Abdullahi da Inna Demmo, sunan mahaifiyarta kuma Inna Demmo, sannan su bakwai ne aka haifa a gidan - maza uku, mata huɗu, kuma dukansu Fulani ne.

Littafin ya bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta wajen zama jigo, kuma wadda ta fara wasu ayyuka da suka canja tarihi da yanayin rayuwa a arewacin Najeriya.

Daga cikin ayyukan da ta koya daga wajen Turawan mulkin mallaka, kuma ta fara a matsayin ta farko daga arewacin ƙasar akwai aikin jarida da aikin asibiti da koyar da yaƙi da jahilci na mata da sauran su.

Haɗuwarta da Bature

Dadasare

Asalin hoton, Aliyah Adamu Ahmad

Bayanan hoto, Dadasare tare da Turawa a Ingila

Dadasare ce ta biyar a gidan su. Babbar yarsu ita ce Bulo Aisha sai Uratu Adama ke biye da ita, sai Muhammadu sai Dawuda sai Dadasare da aka haifa tana bakwani sai Baba Salamatu sai Salihi.

Dadasare ta ce jim kaɗan bayan rasuwar mahaifinsu ne, mahaifiyarsu ta kira su, ta tambaye su ko su ci gaba da zama a Gola ko koma su Jambutu. Sai suka bayar da shawarar su Jambutu da zama.

Bayan komawarsu Jambutu ne wani ɗan uwan mahaifinta ya auri mahaifiyarsu, sannan ita ma Dadasare a lokacin tana da shekara 9, sai aka fara yi mata tayin aure.

Dadasare na ƴar shekara 12 ne aka kai ta Gola ziyarar dangi, ziyarar da ta canja rayuwarta.

A lokacin ne aka zo da labarin cewa wani Bature na nemam Bafulatana da zai "aura" su zauna tare. Sai wani ɗan uwan Dadasare ya saka sunanta a ciki, amma aka ɓoye mata abin da aka shirya.

Da aka jera su, sai Baturen ya zaɓe ta, sannan ya haɗa ta wani mai gadi mai suna Sadiƙi domin ya riƙa kula da ita.

Dadasare ta taɓa yunƙurin tserewa daga baturen, amma ba ta yi nisa ba, aka tura mutane a dawakai suka kama ta suka mayar da ita, sannan ba da daɗewa ba sai aka mayar da baturen aiki a lardin Ibbi da ke jihar Benuwei a yanzu, inda kuma ya tafi da ita.

A Ibbi ne Dadasare ta fara sabawa da zama tare da baturen, har ta saba da wani abokinsa wanda ta sanya wa suna Jaumusare.

Rayuwar Dadasare a Jaumusare

Jaumusare asalin sunansa Dr Rupert M. East, wanda Dadasare ta bayyana da mutum dogo, mai kyau.

Ba da daɗewa ba ne Dadasare ta haihu da baturenta na farko sannan sai ya kasance zai tafi gida hutu. Don haka ne sai ya ce ta koma gida Gola ta huta kafin ya dawo, ashe rabuwarsu ke nan.

Bayan ɗanta ya rasu ne Jaumusare ya aiko mata wasiƙa cewa tunda 'mijinta' ba zai koma Najeriya ba, ta same shi a Zaria su cigaba da rayuwa. Kuma haka aka yi, da kanta a wannan karon ta tafi Zaria ta fara sabuwar rayuwa da Dr. East.

Wani abu da ya ɗauki hankali a rayuwar Dadasare shi ne yadda ta koma addinin Kirista a lokacin da take Wusasa a Zaria, amma daga baya ta sake komawa addinin Musulunci har ta yi Hajji.

Ta ce da kanta ta zaɓi shiga addinin Kirista, Dr East bai tursasa ta ba, sannan da kanta t zaɓi komawa addinin Musulunci daga baya.

Aikin jarida

A shekarar 1939 ce Dr. East ya assasa jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo a Najeriya a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka.

A zantawar BBC da Farfesa Aliyah, ta ce Dadasare ta fara aiki ne a maɗabba'ar buga jaridar, sannan daga baya ta zama wakiliyar jaridar.

"Ta yi aiki a ɓangaren buga jaridar, sannan ta koma sashen amsa kiran waya da tattara saƙonni. Ta kuma yi aikin nemo labaran kotu, sannan ta zama wakiliyar sayar da jaridar," in ji Farfesa Aliya a zantawarta da BBC Hausa.

A lokacin babban editan jaridar shi ne Dr East, sai Mr Giles ne edita, sai Abubakar Imam Editan Hausa.

Haka kuma ta yi kasance mai rubutu na musamman a kan lafiya da tsafta da sauran hanyoyin kula da jiki da muhalli.

Aikin asibiti

A shekarar 1942 ce ta koma babban asibitin gwamnati na Zaria, inda ta samu horo a kan aikin jinya a wajen Turawan mulkin mallaka, har ta fara ƙwarewa.

Daga baya ta fita zuwa ƙasar Ingila domin samun horo na musamman a kan aikin jinya, kafin daga ta koma Najeriya ta cigaba da aiki.

Ta yi aikin nas a asibitoci da dama ciki har da asibitocin Ingila har ta kai matakin babbar ma'aikaciyar jinya.

Malamar makaranta

A daidai lokacin da take aikin asibiti a Zaria da taimakawa Jaumusare a ayyukansa ta tantance Turawa ta hanyar shirya musu horo da jarabawa a kan Hausa, sai ta yi amfani da damar wajen koyon wasu abubuwa.

A nan ne ta fara sha'awar koyarwa, inda har ta yi aiki a sashen ilimi na gwamnatin arewacin Najeriya.

A zantawar Farfesa Aliyah da BBC, ta ce, "aikin da ta yi a lokacin da take aikin jarida na sayar da jarida a masarauta ya taimaka wajen zama fitacciya. Don haka lokacin da ta fara yunƙurin buɗe ajujuwan yaƙi da jahilci ba ta sha wahala ba," in ji ta.

Farfesa Aliyah ta ce ta fara ne da matan masu riƙe da sarauta, sannan ta faɗaɗa zuwa matan gari, har aka buɗe ajujuwa, sannan ta samu masu taya ta aiki.

Ƙarshen rayuwarta

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A tsakankanin shekarun 1970s ne gwamnatin Najeriya ta karrama Dadasare da lambar yabo ta MON, inda ta kasance cikin matan farko-farko da suka fara samun irin wannan karramawar.

A ranar 6 ga watan Janairun 1977 ta bar Zaria ta koma Gombi, sannan ta ƙarasa Gola, inda mutane da dama suka mata tarba ta musamman, inda cikin ƙanƙanin lokaci ta zama mai faɗa a ji a garin.

Dadasare ba ta da yara, amma ta riƙe yaran wasu. A watan Agustan 1984 ne Dadasare ta kira ƴar da ta riƙe mai suna Hajiya Aisha Dikko, wadda ta yi aure, take zaune a Daura cewa tana son ganinta, kuma lallai ta tafi Gombi washegari.

Sai ta bayyana mata cewa, "idan kin zo ba ki same ni ba, ki duba ƙarƙashin matashin kai, zan ajiye miki saƙo a rubuce a takarda biyu."

Sai Aisha ta tambaye ta ko me take nufi, amma ba ta mata cikakken bayanin abin da take nufi ba.

Haka kuma a daren ranar Dadasare ta faɗa wa wani mai suna Malam Tukur Yola, wanda yake zaune a gidanta yana mata aikace-aikace cewa, "daga gobe ba za ka sake ganina ba."

Washegari Malam Tukur ya shiga gida domin gudanar da aikinsa kamar yadda ya saba. Sai ya ga takalmi da buta da fitila da sallaya a tsakar gidan a bakin rijiya, amma ba ta wajen.

Sai ya ɗauki fitilar ya haske cikin rijiyar, sai ya hango ta a cikin rijiyar ta faɗa ciki. Sai ya nemi taimakon mutane, aka shiga aka ɗauko ta.

Farfesa Aliyah ta ce da ta koma garin Gola, ta gana da mutumin da ya shiga rijiyar, ya goya ta, ya fito da ita.

Aisha Dikko ta isa garin ne bayan kwana uku, inda kawai ta tarar ana zama makokin addu'ar uku, aka faɗa mata cewa Dadasare ta rasu kwana uku da suka gabata.

Ta rasu ne a asibiti bayan Sallar La'asar, inda aka samu gawarta a sallayarta da misalin ƙarfe huɗu bayan ta idar da Sallah.

Sai Aisha Dikko ta shiga daƙin, ta ɗauko wasiƙun guda biyu, inda a ciki Dadasare ta bayyana wasiyar yadda za a raba dukiyarta.

Farfesa Aliyah ta ƙara da cewa, "a lokacin da nake tambayar Aisha Dikko mene ne ke ƙunshe a cikin wasiƙa ta biyun, sai ta fashe da kuka. Sai aka ban sha'awar in haƙura sai wani lokacin in sake tambayarta."

Sai dai Farfesa Aliyah ta ce ko da ta koma Sokoto, ta cigaba da tunanin abin da ke ƙunshe a cikin wasiƙar, tana ta hanƙoron komawa ta sake haɗuwa da Aisha Dikko domin samun bayanan wasiƙar.

Sai dai kuma kafin su sake haɗuwa, ita ma Aisha Dikko ta rasu, "don haka ban san abin da Dadasare ta rubuta a wasiƙa ta biyun ba. Allah Ya jiƙansu baki ɗaya," in ji Farfesa Aliyah.