Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa sauro ya fi son shan jinin wasu mutanen?
- Marubuci, Katherine Wang
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC.com
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A duk lokacin da na je hutu, musamman a lokacin bazara, abu ɗaya da na saba fuskanta shi ne cizon sauro. Sau da yawa sauro kan cije ni fiye da kowa, har ya haddasa min ƙaiƙayi mai tsanani da kuma tabon da ke ɗaukar lokaci kafin ya gushe.
Abin mamaki kuwa shi ne sauran mutanen da muke tare ba su fama da wannan matsala ko kaɗan. Ko cizo ɗaya sauro ba ya yi masu. Kuma ko da ya cije su, yana ɗan nuna alama ne kawai wajen ya yi ja. Wannan ya sa abokaina ke yi mini shaguɓen cewa ''jinina mai daɗi ne.''
Da alama maganar su na iya zama gaskiya. Akwai wasu ɗabi'u da jikin mu ke da su, waɗanda ake iya cewa na halitta ne, daga ciki akwai numfashi da warin ƙashi waɗanda kuma su ne ke tantance wjikin da sauro zai ji daɗin cizo.
Ga wasu hanyoyi uku da mashayin jinin zai iya bi domin maƙale maku.
Sinadarin Carbon-dioxide da mutum ke fitarwa na iya sa sauro ya fi cizonsa
Jinsin mata na sauro ne kaɗai ke cizon mutane. Suna buƙatar jinin ɗan'adam domin samar da sinadaran da ke taimaka musu wajen gina musu ƙwayar ƙwai da kuma haifar da 'ya'yansu. Sauro mata na amfani da ƙrfin da suka da shi ta jin ƙamshi da kuma hangen nesa wajen gano mutum. Haka kuma suna son ruwan da muke fitarwa yayin numfashi, da kuma zufar da ke fita daga jikinmu.
Numfashin ɗan Adam na fitar da sinafarin CO2 wanda ke ɗauke da ruwa da iska, kuma wannan yanayi yana janyo hankalin sauro domin ya zo tsotsar jini. Saboda haka sauro ya fi bibiyar manya a kan ƙananan yara domin manya ne suka fi fitar da wannan sinadari.
Wannan na nufin sauro na bibiyar duk wani abu mai ɗauke da sinadarin carbon dioxide (CO2) ko da kuwa ba mutum bane.
Zafin jiki na janyo sauro
Bincike ya nuna cewa sauro na son zafi da damshi (don haka suna bin duk abin da zai basu wannan)
Saboda haka sauro ya fi bin mata masu juna biyu idan aka kwatanta da yadda ya ke bin waɗanda ba su da shi. Dalili shi ne mata masu juna biyu suna samun ɗumamar jiki da saurin numfashi, lamarrin da ke sanya wa su fitar da sinadarin carbon dioxide (CO₂) sosai.
"Mace na ɗaukar ciki jikinta zai ƙara zafi," in ji Steve Lindsay, farfesa a fannin nazarin ƙwari da alaƙarsu da muhalli a jami'ar Durham da ke Birtaniya.
Mutane masu motsa jiki sun fi barazanar cizon sauro musamman a lokacin da suke motsa jikin da kuma bayan sun kammala saboda a lokacin jiki na zafi kuma sinadarin CO2 na ƙaruwa.
Akwai kuma alamar mutane masu ƙiba za su fi marasa ƙiba ɗaukar hankalin sauro saboda sun fi saurin numfashi da zafin jini.
Yanayin fata na da tasiri wajen janyo sauro
Idan sauro ya yi kusa da jikin mutum, yana gane wanda ya ke buƙata ne ta hanyar tantance yanayin fata da kuma warin numfashi.
"Warin ne ke tantance wanda sauro zai ciza, domin sauro yana son sinadarai" inji Lindsay.
Lindsay da sauran ƙwararru sun musanta hasashen da wasu ke yi cewa sauro na bibiyar mutane masu ''jini mai daɗi''
Masu bincike a jami'ar Rockefeller ta Amurka sun yi nazari kan warin jikin mutane 64 da suka sanya riguna na tsawon sa'oi shida. Sauron da aka yi gwajin da su sun riƙa tantance rigar da za su bi ta hanyar mayar da hankali ga rigunan da mutane masu tsananin sinadarin CO2.
Ƙwararrun sun tattara makin da kowanne mutum ya samu kuma sun gano cewa wanda ya fi samun maki ya zarci wanda yake na ƙarshe da tazarar maki fiye da 100. Wannan sakamako ya kasance a haka na tsawon shekaru duk da sauyin tsarin rayuwa da mutanen suka yi a tsakanin lokacin.
Binciken da aka yi ya nuna cewa ƴan biyu masu kama ɗaya na fuskantar barazanar sauro iri ɗaya, yayin da waɗanda ba su kama ɗaya kuma kowanne ke da nauyi na daban na jikin da sauro ke bi. Bincike daban-daban sun nuna cewa ana gadon irin warin jiki da sauro ke bi a jikin mutane.
Akwai bambanci a cizon da sauro ke yi?
Akwai bambanci a yadda jikin mutane ke amsawa bayan sauro ya cije su. Wani bincike ya nuna cewa ƙwayoyin halittar ɗan Adam na taka muhimmiyar rawa wajen ƙayyade irin tasirin da cizon sauro zai yi a jikin mutum. Saboda haka, alamomin da ke bayyana bayan cizon sauro na iya bambanta daga mutum zuwa mutum.
Masana sun gano cewa yadda cizon sauro ke bayyana a jikin mutum na iya nuna irin yadda jikinsa ke ɗauke da abubuwan da ke jan hankalin sauro. Wasu kan yi zaton sauro ya fi cizon su saboda alamomin cizon suna fitowa a fili a jikinsu, yayin da a wasu mutane kuma sauro na iya cizonsu ba tare da an ga wata alama mai yawa ba.
Sai dai masana sun jaddada cewa ko mutum yana ganin alamun cizon sauro a jikinsa ko a'a, hakan ba ya rage haɗarin da cizon ke tattare da shi. Don haka kowa na buƙatar ɗaukar matakan kariya daga cizon sauro, domin ko da ƙananan sauro na iya yaɗa cututtuka masu haɗari ga lafiyar ɗan Adam.