Za mu ci gaba da girmama ƴancin gudanar da addini a Najeriya - Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa na ba da fifiko wajen tabbatar fahimtar juna a tsakanin addinai da kuma inganta zaman lafiyar ƙasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Archbishop Paul R. Gallagher, sakataren hulɗa da ƙasashe da ƙungiyoyi na Vatican, wanda ya ziyarci shugaban tare da rakiyar ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Bianca Ojukwu.
Shugaba Tinubu ya ce tattaunawa domin fahimta juna a tsakanin addinai ita ce hanya mafi dacewa wajen magance ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Ya shaida wa Archbishop ɗin cewa yana da dadaddiyar kyakkyawar alaƙa da Cocin Katolika tun lokacin da yake gwamnan Jihar Legas. Ya ce yana matuƙar alfahari da gudummawar da Cocin ke bayarwa a fannonin ilimi da kiwon lafiya.
Tinubu ya kuma shaida wa baƙon cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a baya-bayan nan, sannan ya ƙara da cewa za su ci gaba da ƙoƙari domin tabbatar da nasarar.
A nasa jawabin, Archbishop Gallagher ya ce ya ziyarci Najeriya ne domin bikin cika shekara 50 da ƙulla hulɗar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Cocin Katolika, sannan ya ce Najeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci ga Cocin saboda yawan mabiya da kuma ƙarfinta.
Ya kuma isar da godiyar Paparoma Leo XIV ga Shugaba Tinubu bisa halartar bikin rantsar da shi. Haka kuma ya bayyana jin daɗinsa da irin ci gaban da Jami'ar Veritas, wadda Cocin Katolika ta kafa a Abuja, ta samu.