Man City da Man Utd na hamayya kan Kone, Barca ta haƙura da Alvarez

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na son karɓo ɗanwasan Roma Manu Kone yayin da ake alaƙanta ɗanwasan tsakiyar na Faransa mai shekara 25 da Manchester United a wannan bazara. (Mail)
Aston Villa na son ɗauko ɗanwasan baya na Chelsea da Ingila Tosin Adarabioyo, mai shekara 28, a matsayin wanda zai maye gurbin Ezri Konsa bayan ya koma Arsenal. (Sky Sports)
Benfica ta tuntuɓi Chelsea kan Adarabioyo. (Sun)
Tottenham na tattaunawa domin ɗauko ɗanwasan gaba na Brazil Savinho, mai shekara 22 da kuma ɗanwasan Masar Omar Marmoush daga Manchester City. (Athletic - subscription required)
Barcelona na sa ido kan yadda za ta kaya tsakanin Harry Kane da Bayern Munich, yayin da shekara ɗaya ta rage a yarjejeniyar ɗanwasan gaban na Ingila mai shekara 33. (Mail)
Everton na son ɗanwasan Como da Senegal Assane Diao, mai shekara 20, wanda tsadar sa za ta iya kai wa tsakanin fam miliyan 50 zuwa 60. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus ba ya son zuwa Napoli duk da buƙatar ɗanwasan na Brazil mai shekara 29. (Mirror)
Juventus na hamayya da Napoli kan buƙatar ɗanwasan Manchester United Joshua Zirkzee, amma dukkaninsu sai sun cefanar da wasu ƴanwasan kafin iya ɗauko ɗanwasa gaban na Netherlands mai shekara 25. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Hull City na dab da cimma yarjejeniya da Real Betis kan ɗanwasan gaba na Spain Pablo Garcia. (Sport - in Spanish)
Hull da Ipswich Town da Al-Ittihad na ribibin ɗanwasan tsakiya na Morocco Azzedine Ounahi mai shekara 26 da ke murza leda a Girona. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Arsenal na son ɗauko ɗanwasa Gibraltar James Scanlon, mai shekara 19, da kuma Habeeb Ogunneye na Ingila mai shekara 20 daga Manchester United. (Telegraph - subscription required)
Barcelona ta haƙura da Julian Alvarez, mai shekara 26 daga Atletico Madrid tana diba wasu zaɓin. (ESPN)











