'Yadda man bilicin ya ɓata fuskokin ƴaƴana'

    • Marubuci, Madina Maishanu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Kano state, Nigeria
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Fatima, zaune tana kallon ɗanta mai shekara biyu cikin takaici saboda yadda fuskarsa ta zamo launuka biyu.

Fatima mai shekara 32, ta kasance tana shafa wa ƴaƴanta guda shida man bilicin, saboda ta canja yadda ake nuna musu wariya a gida saboda rashin haskensu, amma yanzu take cike da da-na-sanin matakin da ta ɗauka.

Akwai yarinyarta da dole take rufe fuska a duk lokacin da za ta fita, saboda ba ta so ana ganin yadda fuskar ta caɓe.

Wata kuma maimakon ta ƙara hasken, sai ta ƙara zama baƙa, ga kuma wani ciwo a kusa da idonta.

Fatima ta ce akwai wani kuma wanda wasu fararen manyan ƙuraje suka fashe masa a leɓe da gwiwa.

"Ƴar’uwata ta kasance tana haihuwar ƴaƴa farare, ni kuma nawa baƙaƙe. Sai na lura mahaifiyarmu ta fi son yaran ƴar’uwata sama da nawa saboda launin fatarsu, wanda hakan ya sa nake jin ba daɗi," in ji Fatima.

Ta ce ta yi musu amfani da man bilicin ne da take saya a kasuwa, ba tare da neman shawarar likita ba.

Da farko da ta fara musu bilicin ɗin, mayukan sun fara karɓar su, har kakarsu ta fara nuna musu ƙauna. Amma kwatsam sai fuskokinsu da jikinsu suka fara caɓewa.

Haskaka fata, ko kuma bilicin kamar yadda aka san shi a Najeriya, ana amfani da shi ne a wasu sassan duniya domin gyara jiki.

Matan Najeriya sun fi na ƙowace ƙasa a Afirka amfani da man bilicin - kashi 77 na matan Najeriya suna amfani da man bilicin kamar yadda alƙaluman Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna.

A ƙasar Congo-Brazaville, mata kashi 66 ne suke bilicin, sannan a Senegal kashi 50, sai Ghana mai kashi 39.

Mayukan bilicin ɗin sukan kasance suna ɗauke da sinadarin corticosteroids ko hydroquinone, waɗanda za su iya cutar da jikin mutum idan aka yawaita amfani da su, sannan a wasu ƙasashen ba a sayar da mayukan sai da takardar likita. Wasu sinadaran da ke cikin mayukan sun haɗa da mercury da kojic acid, waɗanda suke da illa.

Abubuwan da za su iya haifarwa sun hada da ciwukan fata da ƙaikayi da canjawar launin fata, sannan za a iya fama da kumburi da gurɓacewar ciki da cutar ƙoda. Haka fatar takan iya yin yaushi, lamarin da hukumar lafiya ta duniya ta ce yana sa cutuka su ƙi warkewa da sauri, da kuma saurin kamuwa da ciwuka.

Yawaitar bilicin a Najeriya ya ja hankalin hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato Nafdac, wadda ta ayyana dokar ta-ɓaci kan amfani da mayukan a shekarar 2023.

Haka kuma yadda iyaye kamar Fatima suke yi wa ƴaƴansu bilicin ya fara zama ruwan dare.

Zainab Bashir Ya’u, wata mai shagon gyara jiki a Abuja ta ce mutane suna haskaka fata ne domin ana alaƙanta masu hasken fata da arziki, kuma an fi kallon su da daraja.

Ta ƙiyasta cewa kashi 80 na matan da ta haɗu da su suna yi wa yaransu bilicin, ko kuma suna shirin yi. Ta ce wasu ma an musu bilicin ɗin a lokacin da suke yara, don haka kawai ci gaba da yi kawai suka yi a yanzu.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake gane mutum yana bilicin a Najeriya shi ne za a ga gwiwoyin yatsunsa sun yi baƙi. Za ka ga duk yadda sauran jikin mutun ya yi haske, gabban gwiwoyin yatsun suna nan da duhu.

Sannan kuma a ɗaya ɓangaren masu shaye-shaye ma gwiwowin yatsunsu kan zama baƙi saboda hayaƙi. Hakan ya sa wasu suke yi wa masu bilicin kallon masu shaye-shaye.

Fatima ta faɗa a game da ƴaƴanta mata masu shekara 16 da 14 cewa "suna fuskantar kyara daga al'umma - ana musu kallon masu shaye-shaye," in ji ta.

Sun kuma rasa masoya saboda maza da dama suna fargabar ƙulla soyayya da waɗanda ake wa kallon ƴan maye.

Na ziyarci wata babbar kasuwa a Kano, inda mutane suke hada-hadar haɗa mayukan haskaka jiki.

Na lura da mayukan bilicin da dama da aka rubuta cewa na ƙananan yara ne, amma kuma ake amfani da wasu sinadarai da aka ƙayyade amfani da su.

Wasu sun bayyana cewa suna amfani da sinadarai irin su kojic acid da hydroquinone da da hodar glutathione, wadda ke jawo ƙuraje da ƙaiƙayi da wasu illolin.

Na kuma ga yadda ƴanmata suke rububin sayen mayukan, domin amfanin kansu, da ma waɗanda suke sari.

Wata mata, wadda launin hannunta ya canja, ta ce masu haɗa mayukan suna ƙara sinadarin hydroquinone a mayukan da take shafa wa yaranta, duk da cewa akwai ƙa'idojin amfani da shi ga manya, sannan an haramta ga ƙananan yara.

"Duk da cewa launin hannuna ya canja, na zo in saya wa yarana domin su yi haske. Na yi kuskure ne wajen shafawa, amma zan kiyaye wajen yarana, don haka babu abin da zai faru da su," in ji ta.

Wani mai sayar da mayukan ya ce yawancin kwastomominsa suna sayen mayukan da za su sa fatar yaransu ta riƙa ƙyalli ne.

Sai dai yawancinsu ba su san adadin da ya kamata su yi amfani da shi ba wajen haɗa mayukan.

Wani mai shagon ya ce suna amfani da "kojic mai yawa ne" idan mutum na son fata mai laushi sosai, "sai kuma ƙaramin cokali," idan haske kaɗan suke so.

Adadin kojic da aka amince a yi amfani da shi a Najeriya shi ne kashi 1, kamar yadda Nafdac ta ƙayyade.

Na kuma ga wani mai shagon yana yi wa mata allura.

Dokta Leonard Omokpariola, darakta ne a Nafdac, ya ce suna ƙoƙarin ilimantar da mutane illolin bilicin. Ya ce sun kai samame a kasuwanni, sannan suna ƙoƙarin ƙwace mayukan da aka shiga da su ƙasar a bakin iyakokin ƙasar.

Sai dai ya ce jami'ansu na shan wahala wajen gane irin sinadaran saboda, "ana shigo da wasu ne a kwalayen da ba a rubuta bayanai ba, don haka idan ba an kai ɗakin gwaji ba, ba za a gane ba."

Fatima ta ce za ta cigaba da zama cikin damuwa saboda abin da ta aikata, musamman idan ciwukan jikin yaranta ba su warke ba.

"Lokacin da na faɗa wa mahaifiyata abin da na yi saboda abin da ta yi a baya, sannan ta ji labarin illolin bilicin, da ma kyarar da ake yi wa jikokinta, sai ta shiga damuwa, har ta ban haƙuri," in ji ta.

Yanzu a shirye take da taimaka wa sauran iyaye domin gudun faɗawa abin da take ciki.

"Duk da cewa na daina, har yanzu akwai gurabunsa. Ina roƙon sauran iyaye su daina."

* An canza sunan Fatima domin kare iyalanta.