Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa zazzaɓin 'typhoid' ke yawan kama baƙi?
Ana ɗaukar cutar taifod, ta hanyar wata ƙwayar cuta da ake kira Salmonella Typhi, kuma ana kamuwa da ita ne ta hanyar cin abinci da ruwan sha da ya gurɓata da ƙwayar cutar, a cewar hukumar lafiya ta duniya.
Cutar ta fi aukuwa ne a wuraren da ba su da tsafta da rashin tsaftataccen ruwan sha a birane da kuma a yankunan karkara.
Alamomin cutar sun haɗa da:
- Zazzaɓi na dogon lokaci
- Gajiya
- Ciwon kai
- Tashin zuciya
- Ciwon ciki
- Amai
- Kumburin ciki ko gudawa
Wasu mutanen kan samu ƙananan ƙuraje a jiki, yayin da idan cutar ta tsananta ta kan janyo wasu matsalolin kiwon lafiya, da kuma rasa rai.
Ƙananan yara da al'umomin da ba su samun ruwa mai tsafta da yanayi mai tsafta sun fi haɗarin kamuwa da cutar.
WHO ta ce matafiya kan faɗa cikin haɗarin samun cutar zazzabin taifod, saboda wurin da suka baƙunta bai kai tsaftar wuraren da suka saba zama ba.
Matafiya zuwa ƙasashen da ke samun annobar cutar a kudu da hamadar Sahara da wasu ƙasashen da ke nahiyar Asiya na fuskantar barazanar kamuwa da cutar, in ji hukumar.
Wata likitar yara da ke aiki da asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya a jihar Gombe da ke Najeriya, Dakta Fatima Usman ta ce taifod cuta ce mai yaɗuwa a cikin al'umma. Kuma "za ka iya zama ɗauke da cutar ba tare da ta yi maka illa ba. Amma za ka iya ba wani ita kuma ta yi masa illa."
Wasu hanyoyin kamuwa da taifod
Dakta Fatima Usman ta zayyana wasu hanyoyin da zai sa mutum ya kamu da cutar cikin sauri. Wasu daga cikinsu su ne:
- Cin naman dabbar da bai dahu sosai ba
- Cin ƙwai da bai dahu sosai ba
- Madarar shanu
- Ganyayyakin da ba a wanke yadda ya kamata ba
- Kayan marmari ko kayan lambu marasa tsafta
Ta bayyana cewa an tabbatar da cewa cutar na wanzuwa a cikin tsuntsaye da kaji.
Likitar ta ce cutar na fara ɓarna ne daga ciki, tana huda hanji, tana kumbura hanta da saifa, cutar na kuma karya garkuwar jiki.
Sai dai likitar ta jaddada muhimmancin zuwa asibiti domin tabbatar da cutar, saboda wasu alamominta na kama da wasu cututtuka.
Wasu alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2019, aƙalla mutane miliyan tara ne ke kamuwa da cutar, yayin da 110,000 ke rasa rayukansu duk shekara a faɗin duniya.
A shekarar 2017 ne hukumar ta amince da wasu nau'ukan rigakafin cutar guda biyu, waɗanda tuni kasashen da ke samun annobar cutar suka sakata a cikin jerin rigakafin da ake yi na yau da kullum.
Ta bayar da shawarar cewa za a iya yin rigakafin cutar ga yara wadanda suka haura watanni shida a duniya, zuwa manya masu shekara 45 zuwa shekaru 65 a duniya.
Sai dai ta ce matafiya su kiyaye cin abinci ko ruwan da ya gurɓace domin kaucewa kamuwa da cutar ko da kuwa sun yi allurar rigakafin, domin ba ya bayar da kariya dari bisa dari.
Hukumar lafiyar ta bayyana cewa taifod cuta ce da ke da magani, sai dai wani ƙalubalen da ake fuskanta shi ne na bijirewa magunguna da cutar ke yi, musamman kwayar cutar Salmonella Typhi da ta sauya halitta.
Lamarin da ke janyo sarƙakiya da kuma kashe makudan kuɗaɗe wajen neman magani.