Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bambancin yadda ƴan Arewa da ƴan Kudu ke zaɓe a Najeriya
A daidai lokacin da babban zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara matsowa, tuni ƴan ƙasar sun fara lissafi tare da hasashen ƙuri'un da manyan ƴantakara za su samu, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.
A siyasar Najeriya, ɓangaren da dan takara ya fito da kuma addini na taka rawa sosai wajen zaɓe, sai dai babu wani abu ɗaya tilo da za a ce shi ne al'ummar dukkanin ɓangarorin ƙasar za su dogara da shi wajen zaɓen shugaba.
A zaɓen mai zuwa, ana cigaba da tattaunawa ne kan yankin ƙasar da ya fi cancanta da fitar da shugaban ƙasa, inda wasu ke ganin kudancin ƙasar na da sauran wa'adi ɗaya na shekara huɗu.
Sai dai wasu na ganin bai kamata yanki ya zama jigo ba wajen zaɓe, inda suke da ra'ayin cewa kowane ɗan Najeriya na da ƴancin tsayawa takara a kowane lokaci kamar yadda kundin tsarin mulki ya nuna.
Sai dai a tarihin Najeriya, yawancin zaɓukan da suka gabata ba a cika samun ɗantakara daga wani yanki da ya samu nasara ba tare da haɗaka da wani yankin ba.
Akalar zaɓen manyan ƙabilu
A Najeriya akwai manyan ƙabilu guda uku, waɗanda suke matuƙar tasiri a zaɓukan Najeriya tun gabanin samun ƴancin kan ƙasar.
Sai dai kowace ƙabila akwai abubuwan da tarihi ya nuna suna tasiri kan yadda ƙuri'arsu ke kasancewa.
Farfesa Kari ya ce tun a zamanin Jamhuriya ta 1 zuwa yanzu, ba a taɓa samun lokacin da yankin arewa ta ɗunke wuri guda ba domin yin zaɓe sai a lokacin zaɓen 2015 da marigayi Muhammadu Buhari ya yi nasara a jam'iyyar APC.
Arewa
Masanin siyasar, Farfesa Abubakar Kari ya ce "Sassa daban-daban na Arewa suna zaɓen jam'iyyar daban-daban ne. Misali a Jamhuriya ta ɗaya, yankin Sokoto da Katsina da Bauchi sun yi jam'iyyar NPC ce ta su Sardauna, sai wasu sassan Kaduna da Kano suka yi NEPU," in ji shi.
Ya ƙara da cewa haka aka yi a Jamhuriya ta biyu, inda a cewarsa tsohuwar Sokoto da Bauchi da Neja suka yi jam'iyyar NPN, sai Kano da Kaduna suka zaɓi PRP.
Sai dai duk da haka, Farfesa Kari ya ce a arewacin Najeriya, addini yana tasiri, amma ya ƙara da cewa ƙabilanci bai cika wani tasiri ba wajen sauya akalar zaɓuka, saboda a cewarsa an sha zaɓar wanda ba Bahaushe ba ya yi gwamna.
"Misali ka ga an zaɓi Malam Ibrahim Shekarau a matsayin gwamnan Kano, kuma ba Bahaushe ba ne, kuma ba Fulani ba ne. An zaɓi Malam Yahaya Abdulkarim a tsohuwar jihar Sokoto a matsayin gwamna, kuma idan aka bi diddigi asali ba ɗan arewa ba ne," in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa an taɓa zaɓen Ɗahiru Muhammad Deba a matsayin gwamnan Bauchi.
"Kuma ko a tsohuwar Bauchi ma ƴan ƙabilarsu ba su da yawa. Amma duk da haka ya zama gwamna."
Wannan ya sa masanin siyasar ya bayyana cewa ƙabilanci ba shi da tasiri sosai a arewacin ƙasar, amma ya nanata cewa addini na taka rawa.
Kari ya ƙara da cewa arewacin Najeriya aƙida ma na taka yawa wajen zaɓe, inda ya ce akwai yankunan da suka fi zaɓen jam'iyyun da suke da alaƙa da gwamnati ko sarakuna.
"Haka kuma akwai waɗanda su jam'iyyun hamayya kawai suke zaɓa a duk lokutan zaɓe saboda aƙida," in ji shi.
Kudu
A ɓangare daya kuwa masanin ya ƙara da cewa a kudancin Najeriya, musamman manyan ƙabilu na Yarbawa da Ibo, ƙabilanci na da tasiri.
"Yarbawa ƙabilanci ya fi tasiri. Idan aka yi la'akari da sakamakon zaɓen baya, tun daga Jamhuriya ta ɗaya zuwa yanzu, za a ga sun fi karkata zuwa ɗan takara ɗaya, kuma ƙabilanci ne ke tasiri," in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan ba ɗan ƙabilarsu ba ne yake takara, "yawancin lokuta inda shugabaninsu suka karkata, su ma masu zaɓen can suke karkata," in ji Farfesa Kari.
Masanin siyasar ya ƙara da cewa su ma ƙabilar Ibo ƙabilanci ne ke tasiri, sannan ya ƙara da cewa akwai kuma addini na tasiri a yankin su.
"Sai dai su ba su cika ɗaukar zaɓen da muhimmanci ba idan aka yi la'akari da alƙaluman sakamakon zaɓukan da aka yi," in ji shi.
Sauran ƙabilu
Farfesa Kari ya ce sauran ƙananan ƙabilu haɗaka suke yi da babbar ƙabila a duk lokacin zaɓe, duk da ya ƙara da cewa ba lallai ba ne haɗakar ta cigaba da wanzuwa har zuwa lokacin zaɓen.
"A Jamhuriya ta ɗaya da ta biyu akwai alaƙa mai kyau tsakanin yankin Neja Delta da Arewa, amma sannu a hankali alaƙar ta rushe," in ji shi.
'Mabambantan salailai'
A nasa jawabin, Dr Kabiru Sufi, mai sharhi kan harkokin siyasa, kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ya ce ƙabilanci da addini suna taka rawa sosai wajen sauya akalar zaɓen Najeriya.
Sai dai ya ce kowace kakar zaɓe na zuwa da nata salon, wanda ke sauya irin tunanin da mutane ke da shi kan zaɓen.
"Yawanci yana dangantaka ne da abin da ƴansiyasar suka bayyana musu wajen neman ƙuri'a, amma yawanci a kan yi la'akari da ayyukan ɗansiyasar da ƙabilanci da addini da kuma ɓangaranci, sannan wasu lokutan sukan duba yanayin ɗantakarar," in ji shi.
Masanin harkoki siyasar ya ce ko a lokacin zaɓen 2007, Atiku Abubakar ya yi amfani da taken naka sai naka, wanda a lokacin aka yi zargin lamarin ya ɗan tayar da hazo.
"Ko a zaɓen 2023 ana ganin Ibo sun yi amfani da ƙabilanci a duk faɗin ƙasar. Misali ko a Kano a yankin Sabon Gari da suke da yawa, sun yi zaɓen ƙabilanci."