Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 17/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 17/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Abin da ya sa hukumar tace fina-finan Kano ta dakatar da jarumanta biyu

    Hukumar tace fina-finan Kano ta yi ƙarin haske da dalilan da ya sa ta dakatar da wasu jarumanta biyu har na tsawo shekara guda.

    Da safiya yau ne hukumar ta sanar da dakatar da Adam Garba da aka fi sani da Raba-gardama da kuma Amina Uba Hassan da ka fi sani da Jamila a cikin Labarina.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan ganinsu a wani bidiyo da ta yi zargin ya saɓa wa tarbiya.

    ''An ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaftace tarbiya da nuna kyawawan ɗabi’u a dukkan bidiyoyin da ake fitarwa, tare da tabbatar da bin dokokin hukuma ya kamata'', in ji sanarwar.

    Hukumar ta ce bidiyon ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa dakatarwar na nufin an hana su gudanar da duk wani aikin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.

    ''Karya wannan doka na iya jawo hukunci mai tsauri kamar yadda yake ƙunshe cikin tanadin dokar da ta kafa hukumar'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta kuma ambato shugaban hukumar, Abba El-Mustapha na kira ga daraktoci da masu shirya fina-finai su mutunta wannan umarnin dakatarwa.

    A nasa ɓangare jarumi Adam Garba ya nuna damuwarsa kan dakatarwar.

    Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa ya ce ya kamata hukumar ta tuntuɓe su, domin jin abin da ya faru a bidiyon.

  2. Gobara ta tashi a tashar nukiliyar UAE

    Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce gobara ta tashi cibiyar nukiliyar ƙasar da ke yankin Al Dhafra, bayan harin jirgin maras matuƙi.

    Harin ya faɗa kan wanin injin wuta da ke wajen tashar nukiliyar ƙasar ta Barakah

    Hukumomin ƙasar sun ce babu labarin jikkata ko rasa rai a lamarin, saboda bai yi wata illa wa tashar ba.

  3. Iran ta naɗa kakakinta majalisar dokokinta matsayin lura da alaƙar China

    Iran ta naɗa kakakin majalisa dokokinta - wanda ya zama babban mai shiga tsakanin a yarjejeniyar ƙasar da Amurka - a matsayin wanda zai lura da alaƙar ƙasar da China.

    Naɗin Mohammad Bagher Ghalibaf na zuwa ne kwanaki bayan ziyarar Shugaba Trump na Amurka zuwa China.

    Shugaba Trump ya yi iƙirarin cewa Shugaban China Xi Jinping ya ce zai taimaka wajen buɗe mashigar Hormuz, sannan zai tabbatar ƙasarsa ba ta aike wa Iran tallafin soji ba..

    Tsohon babban mai shiga tsakani na Iran, Ali Larijani, da aka kashe a hare-hare ta sama watanni biyu da suka gabata, shi ma da na irin wannan muƙami game da China.

  4. 'FIFA ta magance ƙorafe-ƙorafen Iran kan Gasar Kofin Duniya'

    Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Iran Mehdi Taj ya gana da babban sakataren ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, Mattias Gradstrom a birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya inda suka tattauna ƙorafe-ƙorafen da ƙasar ke da su game da Gasar Kofin Duniya.

    Mista Taj ya ce tattaunawar ta warware duka matsalolin da Iran ke ganin za su iya kawo mata tarnaƙi a bulagron nata domin halartar gasar.

    Ya ce bayan tattaunawar a yanzu tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar za ta iya halartar gasar ba tare da wata matsala ba.

    A nasa ɓangare sakaten na FIFA, Mattias Gradstrom ya yaba wa tattaunawar, wadda ya ce ta taimaka wajen magance damuwar da Iran ke da shi game da zuwanta gasar.

    A gobe Litinin ne ake sa ran tawagar Iran za ta tashi zuwa sansanin horonta da ke Turkiyya, a shirye-shiryen zuwa gasar.

  5. Makaken jirgin ruwan yaƙin Amurka na USS ya koma ƙasar bayan yaƙin Iran

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa makaken jirgin ruwan yaƙin ƙasar, na USS Gerald R. Ford da akja tura yankin Gabas ta Tsakiya kafin fara yaƙin Iran ya koma Amurka a ranar Asabar bayan aikin kwanaki 326.

    Wannan ne lokaci mafi tsawo da jirgin - wanda ke ɗaukar jiragen yaƙi, kuma suke sauka a kansa - ya yi tun bayan yaƙin Vietnam.

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegsett ya je tashar ruwa ta Norfolk da ke jihar Virginia domin tarbar jirgin, wanda shi ne mafi girma da ke jiragen sama.

    A cewar sojojin Amurka, jirgin ta taimaka a hare-haren da ƙasar ta ƙaddamar a yankin Karebiyan, inda sojojin Amurka suka ƙaddamar da hare-hare kan ƙananan jiragen ruwan masu safarar ƙwaya, tare da ƙwace tankokin mai da kuma kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro da mai ɗakinsa.

    Daga nan kuma jirgin ya nufi yankin Gabas ta Tsakiya, domin taimakawa a hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kan Iran.

    A tsawon wannan lokaci, akwai lokacin da gobara ta tashi a sashen wanke-wanke na jirgin inda ta ji wa ma'aikata biyu mummunan raunuka tare da lalata kusan gadaje 100.

    An kuma riƙa samun rahotonnin matsaloli a sashen banɗakunan jirgin da sashen tsaftace shi.

  6. Hezbollah ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Isra'ila arewacin ƙasar

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari da jirage marasa matuƙa kan wani sansanin sojin Isra'ila a arewacin ƙasar, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta mai tangal-tangal ƙasashen ɓangarorin biyu ta kasa dakatar da hare-haren da aka fara tun a ranar 2 ga watan Maris.

    Ƙungiyar wadda ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar cewa dakarunta sun kai hari kan sansanin soji na ''Yaara garisson'' ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.

    A baya Hezbollah ta sha bayyana kai hare-hare kan dakarun sojin Isra'ila a kudancin Lebanon, inda a cewar ƙungiyar, Isra'ila ta kwace wasu yankunan a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

  7. Kazakhstan ta aika wa Iran manyan motocin kayan agaji 30

    Gwamnan birnin Sarakhs a Iran ya ce manyan motoci ɗauke da kayan agaji daga Kazakhstan sun ira lardin.

    Majid Beiki ya ce kayan agajin da suka karɓa sun haɗa da fulawa da magunguna da kayyakin gwangwani a sikari waɗanda suka isa ƙasar.

    Mista Beiki ya bayyana kayan agajin a matsayin alamar jin kai da tsausayawa daga maƙwabtan ƙasashe.

    Birnin Sarakhs na yankin arewa maso gabashin lardin Khorasan Razavi a kusa da kan iyakar ƙasar da Turkmenistan da ke tsakiyar Asiya.

  8. Sarkin Musulmin Najeriya ya buƙaci a fara duba watan babbar sallah daga yau

    Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar musulmin ƙasar su fra duban watan babbar sallah daga yau Lahadi 17 ga watan Mayun 2026.

    Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce a kai rahoton ganin watan ga dagaci ko hakimi mafi kusa, domin a sanarwa fadar Sarkin Musulmin, wanda shi ne shugaban kwamitin ƙoli kan Addinin Musulunci a Najeriya.

    Akan gudanar da babbar sallah a ranar kowace 10 ga watan Zulhijja, kwana guda bayan tsayuwar Arfa da mahajjata ke yi a Saudiyya.

    Al'ummar Musulmi kan yanka dabbobi domin yi layya a lokacin babbar sallar, yayin da mahajjata ke yin hadaya.

  9. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukan sada zumunta.