Chelsea na son Rogers, Barcelona ta san Villa na son ɗaukar Rashford

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na son ɗaukar ɗan wasan Aston Villa, Morgan Rogers, sai dai Arsenal da Manchester United, da Paris St-Germain na son ɗaukar sa su ma. (Talksport)

Barcelona, da ke jan ƙafa wajen biyan Euro miliyan 30 kan ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford da ke a matsayin ɗan wasa aro a Barca zuwa na din-din-din, na sa ne da aniyar Auston Villa na son ɗaukar ɗan wasan Ingilar. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Chelsea na neman mai tsaron ragar, kuma hankalinsu ya fi karkata kan mai tsaron Ragar Sunderland Robin Roefs. (Mirror)

Shekara ɗaya ya ragewa ɗan wasan tsakiya na Spaniya, Rodri a Manchester City, sai dai ya ce hankalinsa a kwance ya ke, sannan ya mayar da hankalinsa kan yadda zamansa zai kasance har zuwa ƙarshen kakar wasanni a ƙungiyar. (Marca - in Spanish)

Arsenal na harin ɗan wasan gaban Brazil Gaberial Jesus kan fam miliyan 30, a dai dai lokacin da ake alaƙanta shi da Ac Milan da Juventus.(Caught Offside)

Brentford ta bi sahun Brighton da Chelsea wajen ɗaukar ɗan wasan Congo Said El Mala. (Mail)

Leeds United na son tsawaita kwnataragin ɗan wasan tsakiyar Wales Ethan Ampadu, inda ƙungiya ke sa ran zai amince da hakan, saboda yadda yake son ganin an sabunta masa kwantaragin. (Football Insider)

Mai horar da ƴan wasan Napoli Antonio Conte ya sanar da cewar zai iya barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan nan, bayan samun nasarar kai ƙungiyar shiga gasar Champion. (Football Italia)

Akwai yiwuwar mai horar da ƴan wasan Lazio Maurizio Sarri, na tattaunawa da Napoli don maye gurbin Conte, inda ya ce yana cikin farin ciki, da rashin sauraren sa da ƙungiyar da ya ke, ke yi masa.(Football Italia)