Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 8/08/2026

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 8 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. An rantsar da sabon shugaban Colombia

    An rantsar da sabon shugaban Colombia Abelardo de la Espriella inda ya sha alwashin murkushe abin da ya kira ta'addancin masu fataucin miyagun kwayoyi.

    An rantsar da shi ne a birnin Cali maimakon babban birnin kasar - wani sauyi da ke nuna alamar yaki da kungiyoyi da ke dauke da makamai a yankin.

    Wakilin BBC ya ce ya gabatar da jawabi ga dakarun kasar a wani sansani bayan rantsar da shi, inda ya bukaci tabbatar da doka da yanci a Colombia. Gwamnatin Trump da ke goyon bayan shugaban ta yi alkawalin ba shi tallafin tsaro na biliyoyin daloli

  2. Auren gata ga mutum 3,000 a Kano

    Auren gata ga mutum 3,000Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da Auren Gata ga mutum 3,000 (ma'aurata 1,500), tare da tallafin fara rayuwar aure.

    Daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren akwai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da sauran manya a jihar.

  3. Muna da sharuɗɗa kafin buɗe mashigar Hormuz - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran ya sake jaddada cewa sake buɗe Mashigin Hormuz zai dogara ne da wasu sharuɗɗa da dama, waɗanda suka wuce yarjejeniyar da Tehran ke tattaunawa a kai da Oman a halin yanzu.

    Abbas Araghchi ya ce Oman da Iran sun kusa cimma yarjejeniya kan wata sabuwar hanya da jiragen ruwa za su rika bi ta mashigin ruwan.

    Sai dai ya ƙara da cewa za a sanya wasu sharuɗɗa, ciki har da biyan diyya kan abin da Tehran ke cewa Amurka ta karya daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuni domin kawo ƙarshen yaƙin.

  4. 'Mutum 25 sun mutu, macizai sun sari wasu, mata biyu sun haihu muna wajen masu garkuwa'

    Fiye da mutane 300 da aka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja sun samu ƴanci bayan kusan shida, bayan wani ceto da fadar shugaban Najeriya ta bayyana a matsayin mafi girma da jami'an tsaro suka gudanar a rana guda.

    Daga cikin waɗanda aka ceto akwai mutum 163 da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kan al'ummomin Woro da Nuku a jihar Kwara a watan Fabrairu, inda aka kashe wasu mutane.

  5. UEFA ba ta biya wadda aka yi zargin muna soyayya ba - Infantino

    FIFA ta ce shugabanta, Gianni Infantino, ya yi kakkausar suka tare da musanta wani zargi cewa UEFA ta biya wata mata da aka bayyana a matsayin masoyiyarsa, a lokacin da yake shugabantar hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai.

    Wani mai magana da yawun FIFA ya ce zargin, wanda jaridar Daily Telegraph ta Birtaniya ta wallafa, ba gaskiya ba ne ko kaɗan.

    UEFA ta tabbatar da cewa ta biya ma’aikaciyar da ake magana a kanta wani kuɗin sallama daga aiki, sannan ta dauki nauyin karatun MBA dinta, amma ta ce an yi hakan ne bisa ƙa’idojin da suke aiki a lokacin.

    Zargin ya fito ne a daidai lokacin da ake fama da tsamin dangantaka tsakanin FIFA da UEFA, musamman kan shirin Infantino da aka yi watsi da shi na sayar da hannun jari a gasar cin kofin duniya da sauran gasa.

  6. Amurka za ta kashe dala biliyan uku domin ƙera sababbin makamai

    Gwamnatin Trump ta sanar da cewa za ta kashe dala biliyan uku a ayyukan haƙar ma’adanai masu muhimmanci da kuma samar da batura.

    Wannan na cikin wani ɓangare na zuba jari da nufin taimakawa wajen sake cike rumbunan makamai na Amurka bayan yaƙin da aka yi da Iran.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa sojojin Amurka sun yi amfani da adadi mai yawa na makamai masu linzami da kuma makamai masu linzami na kare sararin samaniya yayin yaƙin da suka shafe watanni biyar suna yi da Iran.

    Jami’an tsaro da ’yan majalisar dokokin Amurka sun yi gargadin cewa zai iya ɗaukar shekaru kafin a maye gurbin wasu daga cikin waɗannan makamai, saboda ƙalubalen da ake fuskanta wajen samar da su cikin gaggawa.

    Ana amfani da wasu ma’adanai kamar rare earth, tungsten, germanium da scandium wajen kera makamai masu linzami masu bin sahihin manufa, jiragen yaƙi, motocin sulke da kuma ingantattun na’urorin soji.

  7. Harin RSF ya yi ajalin aƙalla mutum biyar a Sudan

    Rahotanni daga Sudan sun ce akalla mutum biyar aka kashe a wani hari da dakarun RSF suka kai a jihar Kordofan ta Arewa.

    Majiyoyin tsaro sun ce mayakan sun bude wuta kan mutanen kauyen Al Tamid bayan sun bijere wa wani yunkuri na satar dabbobinsu.

    An kai harin ne a kudancin birnin El-Obeid da aka yi wa kawanya inda fadan da ake gwabzawa ya raba dubban mutane da gidajensu.

  8. Trump ya soki kotun Amurka bisa dakatar da gini dala miliyan 400 a White House

    Donald Trump ya yi kakkausan maartani ga hukuncin da kotun daukaka kara ta Amurka ta yanke na dakatar da gina dakin taro na dala miliyan dari hudu a Fadar White House.

    Mista Trump ya ce hukuncin siyasa ce kawai kuma abin kunya ne ga kasa Wakilin BBC ya ce hkuncin kotun wani cikas ne ga matakin Trump na gina dakin taron Mr Trump ya ce zai daukaka kara zuwa Kotun Koli.

    A bara ne, Mista Trump ya rusa wani bangare na Fadar White House domin samar da wurin shirya taro. Kotun ta ce irin wannan gagarumin aiki ya kamata ya sami amincewar Majalisa.

  9. Harin mayaƙan Houthi ya kashe aƙalla 10 a Yemen

    Wani harin mayakan Houthi ya kashe akalla mutum 10 a birnin Marib na Yamen.

    Mayakan masu samun goyon bayan Iran da kuma ke rike da ikon babban birnin Yemen har zuwa yammacin Marib sun ce sun kai harin ne kan dakarun da ke samun goyon bayan Saudiyya.

    Sun kai harin ne kwana guda bayan kashe wasu dakarun gwamnatin Yemen da dama a wani hari ta sama da mayakan na Houthi suka kai a sasanonin soji na Marib da lardin Hadramawt bayan mutuwar wasu fararen hula 11 a wani harin na Houthi a yankin Najran na Saudiyya

  10. Amurka da Isra'ila ba su ci ribar yaƙi da mu ba - Iran

    A cikin wata sanarwa da rundunar dakarun juyin-juya-halin Iran (IRGC) ta fitar a yayin bikin ranar ƴan jarida, rundunar ta ce Amurka da Isra’ila ba su cimma manufofinsu ba a yaƙe-yaƙen baya-bayan nan da suka yi da Iran.

    Ta ce abin da ta kira “yarjejeniyoyin da aka cimma” ba komai ba ne illa “takardar miƙa wuya da Amurka ta yi ga halin da ake ciki a fagen daga da kuma ƙarfin Iran wajen tattaunawa.”

    Sanarwar ta kuma ce Washington ta fuskanci “tsaka mai wuya ta fuskar dabarun yaƙi” a yaƙin da take yi da Iran, sannan kuma an samu ɓaraka tsakanin ƙawayenta na ƙasashen Yamma.

    Sai dai IRGC ba ta bayyana takamaiman yarjejeniyoyin da take magana a kansu ba.

  11. Farawa

    Jama'a masu bibiyar wannan shafi na kai-tsaye daga BBC Hausa.

    A wannan shafi za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.