Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman abubuwa 10 da ke cikin jawabin Tinubu na ranar ƴancin kai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi ikirarin cewa ƙasar ta kai wani muhimmin mataki a tafiyar farfaɗo da tattalin arzikinta, yayin da yake jawabi ga al'umma a ranar bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai.
Tinubu ya ce yanzu an wuce matakin ɗaukar matakan gaggawa, inda ya ce matakan gaggawa na gyaran tattalin arziki sun yi tasiri, kuma an kafa tubalin farfaɗowar tattalin arziki.
Tinubun ya ce abin da gwamnatinsaza ta mayar da hankali daga gyare-gyaren tattalin arziki zuwa tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun amfana da ci gaban.
Wannan shi ne karo na huɗu da Bola Tinubu ke gabatar da jawabin ranar ƴancin kan Najeriya tun bayan da ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayun 2023.
Ga wasu muhimman abubuwa 10 da ya bayyana a jawabin nasa na ranar Alhamis 1 ga watan Oktoban 2026.
- Tattalin arziki ya fara samun ci gaba: Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasa da sama da kashi 4% a shekarar 2026.
- Saukar hauhawar farashi: Ya ce hauhawar farashi (inflation) ta ragu sosai idan aka kwatanta da kololuwar matakin da ta kai a baya.
- Ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen waje: Ya ce Najeriya ta sake gina ajiyar kuɗaɗen ƙetare (foreign reserves).
- Daidaituwar kasuwar canjin kuɗi: Ya ce kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare ta samu kwanciyar hankali.
- Karuwar fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba: Najeriya ta samu sama da dala biliyan 6 daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a shekarar 2025, wanda ya ce shi ne mafi girma a tarihin ƙasar.
- Raguwar satar danyen mai: Ya bayyana cewa an samu raguwar satar man fetur, lamarin da ya taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga ga ƙasa.
- Alƙawarin rage tsadar rayuwa: Ya yi alƙawarin samar da abinci mai araha, sauƙaƙa sufuri, inganta wutar lantarki da samar da ayyukan yi.
- Bunƙasa noma da ababen more rayuwa: Ya yi alkawarin ƙara amfani da injinan noma da inganta hanyoyi, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin jigilar kayayyaki.
- Ƙarfafa masana'antu da kasuwanci: Ya ce gwamnati za ta tallafa wa masana'antu, amfani da iskar gas wajen samar da makamashi, da kuma inganta hanyoyin sadarwar zamani.
- Yaƙi da talauci: Ya amince cewa har yanzu jama'a na fama da tsadar rayuwa, amma ya ce manufar gwamnati ita ce kawar da talauci ba kawai sarrafa shi ba.
Martanin Atiku Abubakar
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027, yana mai cewa har yanzu 'yan Najeriya da dama na cikin ƙunci duk da ikirarin Shugaba Bola Tinubu cewa ƙasar ta shiga zamanin wadata.
Atiku ya bayyana hakan ne a jawabinsa na "Yanayin da ƙasa ke ciki" da ya gabatar ranar Alhamis domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai.
Ya ce duk wani cigaban tattalin arziki ba shi da wani amfani idan iyalai ba za su iya biyan buƙatun rayuwa na yau da kullum ba.
Ya ce raguwar hauhawar farashi kaɗai ba za ta mayar wa 'yan Najeriya ƙarfin sayen kayayyakin da suka rasa ba, musamman ganin yadda farashin muhimman kayayyaki da ayyuka ke ci gaba da tashi.
Domin nuna irin matsin tattalin arzikin da ma'aikata ke fuskanta, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kwatanta ƙarfin sayen albashin mafi ƙaranci kafin da bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da aka yi.
A cewarsa, albashin mafi ƙaranci na yanzu, wato naira 70,000, na iya sayen kusan lita 50 na man fetur ne kawai, yayin da tsohon albashin naira 30,000 zai iya sayen lita 118 a watan Afrilun 2023.
Ya kuma yi nuni da tashin farashin burodi da ƙwai, yana mai cewa tsadar kayan masarufi na yau da kullum na ci gaba da yi wa gidaje nauyi.
A wani ɓangare na shirinsa na rage farashin man fetur, Atiku ya gabatar da shawarar bayar da tallafin gwamnati ga man fetur da aka tace a Najeriya kaɗai, yayin da za a cire man da aka shigo da shi daga ƙasashen waje daga shirin.
Ɗan takarar na ADC ya kuma yi tambaya kan kuɗaɗen tallafin kai tsaye da gwamnati ta ce tana bai wa marasa galihu, inda ya nemi a bayyana yadda aka gano mutum miliyan 10 da aka ce an bai wa kowannensu naira 75,000.
"Idan har za ku iya gano mutum miliyan 10 da za ku biya kuɗi, to ya kamata ku iya yin bayanin yadda aka biya su."
Har ila yau, ya yi kira da a wallafa bayanan lamuni da kwangilolin gwamnati, yayin da ya nuna damuwa kan yawaitar kasafin kuɗi iri ɗaya da kuma rashin biyan wasu 'yan kwangila haƙƙoƙinsu.
Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati ta yadda 'yan Najeriya za su iya biyan buƙatun rayuwarsu da kuma rayuwa cikin tsaro, ba wai kawai ta hanyar alkaluman tattalin arziki da gwamnati ke fitarwa ba.
Dangane da zaɓen shekarar 2027, ya yi alƙawarin mutunta 'yancin kan hukumomin zaɓe tare da goyon bayan fitar da sakamakon zaɓe daga kowace rumfar kaɗa ƙuri'a cikin gaggawa.