Yaya shugabar ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu za ta yi idda?

Samia Suluhu

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Bayan rasuwar mijinta a ranar 7 ga watan Satumba, 2026, shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan na fuskantar wani lamari da ba kasafai ake samunsa ba.

A matsayinta na musulma, wajibcin iddah ya rataya a kanta.

A bisa tsarin shari'ar Musulunci, iddah wani lokaci ne na makoki da ke da wa'adin wata huɗu da kwana goma inda ake son mace ta ƙauracewa batun sake wani aure da amfani da kayan ado da kuma rage mu'amula da hada-hadar jama'a.

A wani ɓangare kuma matsayinta na shugabar ƙasa ya buƙaci ta ci gaba da gudanar da harkokin al'ummar da ta ke jagotranta bisa abin da klundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Daidaita waɗannan ayyukan guda biyu yana haifar da wata muhimmiyar tambaya: Ta yaya shugabar ƙasa mace za ta gudanar aikin ibada na idda ta kuma ci gaba da jagorancin al'ummar ƙasarta duk a lokaci guda?

Me musulunci ya ce kan iddar Samia Suluhu?

Babban ƙalubalen da Shugaba Samia ke fuskanta ya shafi yadda za ta taƙaita al'amuran rayuwarta da suka shafi hulɗa da jama'a da zirga-zirga kamar yadda ƙa'idojin idda suka tanada.

Duk da haka, a matsayinta ta shugabar ƙasa ba za ta iya yin watsi da harkokin gwamnati ba tare da an saɓawa tsarin mulkin ƙasa ba.

Dokokin Musulunci sun yi bayani dalla-dalla game da yanayin larura a lokacin idda. Malaman Musulunci sun yi ittifaki cewa mata masu riƙe da muhimman muƙamai —kamar likitoci, da alƙalai, ko shugabannin ƙasa—an ba su izinin fita daga gidajensu a lokacin iddah domin gudanar da muhimman ayyukan da ke amfanar al'umma.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malaman addini irinsu Sheikh Halliru Maraya, malamin addini a jihar Kadunan Najeriya, sun yi bayanin cewa shari'ar musulunci ta bayar da damar macen da ke iddah ta fita daga gidanta da rana domin ta gudanar da ayyukan da suka zame ma ta dole.

''Kamar ita shugaba Samia Suluhu, lura da irin muƙamin da ta ke riƙe da shi, tana iya fita, ta je ofishinta domin gudanar da wasu ayyukanta, amma da zaran rana ta faɗi dole ta koma gidan da ta ke kwana. A nan ana nufin gidan mijinta.'' in ji shi

''Haka kuma dare a bisa shari'ar musulunci na nufin daga faɗuwar rana zuwa fitowar alfijir.''

Sheikh Maraya ya ƙara da cewa duk da addini ya bayar da damar mai idda ta fita da rana, akwai cikakkiyar hani game da batun yin balaguro a lokacin da ta mace ke cikin idda.

''Kamar yanzu yanzu za a fara taon majalisar ɗinkin duniya a birnin New York, ita shugabar ƙasa ba za ta halarci wannan taron ba, sai da ta tura wakili, saboda macen da ke iddar rasuwar mijnta babu damar ta yi tafiya.''

Malamin addinin ya kuma yi ƙarin bayanin cewa baya ga misali mace mai riƙe da babban muƙami kamar ta shugabar ƙasa, wasu mata da ke gudanar da wasu ayyuka na musamman kamar malaman makaranta da likitoci da alƙalai da ma'aikatan jinya dk suna iya fita da rana domin gudanar da ayyukansu, muddin za su koma gidajensu kafin faɗuwar rana.

Baya ga batu fita daga gida ƙa'idojin idda sun tanadi cewa mace ba za ta yi ado ko kwalliya ba ko da kuwa za ta fita daga gida.

''Idan za ta fita da ranan nan, maganar sutura, babu damar ta sa sutura mai tsada, mai ado. Babu kuma damar ta sa kayan kwalliya irinsu zobe da warwaro ko abun wuya na zinare ko azurfa. Har ma da abubuwan da suka shafi kwalliya irinsu lalle da makamantansu'' in ji shi

Haka kuma malamin ya ce shari'a ta hana sanya turare ko kuma amfani da mai da ke da ƙamshi.

Ya ce, ''Babu damar ta sa turare, a jikinta ko tufafinta. Dole ne mace mai idda ta kiyaye duk waɗannan ƙa'idojin na tsawon wata hudu da kwana goma.''

A kan batubn wa'din idda kuma, malamin addinin ya ce ga mace mai ciki, iddar ta ba ya ƙarewa har sai bayan ta haihu. Ko da kuwa sai bayan watanni da dama da rasuwar. Haka kuma ko da ta haihu ne kwana ɗaya bayan rasuwar mijin, a lokacin iddar ta za ta ƙare nan take.

Wane ne Haafid Ameir, jagoran Tanzania a bayan fage?

Samia Suluhu

Asalin hoton, Social

Hafid Ameir Hassan, shi ne mijin shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, wanda ya rasu a ranar 7 ga Satumba, 2026 a asibitin tunawa da Emilio Mzena da ke Zanzibar, inda yake jinya.

Sai dai, duk da cewa shi ne mijin Shugabar ƙasar, Hassan bai kasance mutumin da ake yawan gani a bainar jama'a ba.

Tsawon shekaru, ya yi rayuwa a asirce, nesa da idanun jama'a da na kafofin watsa labarai, inda ya ƙauracewa duk wasu harkokin siyasa.

Ko lokacin da ya halarci wasu tarukan matarsa, ba ya nuna kansa ko neman shahara.

Rashin hayaniyarsa ya sa Haafid ya zama mutumin da yawancin ƴan Tanzaniya ba su sani sosai ba, duk da cewa shi ne mijin ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar ƙasar.

Hafidh tsohon masani ne a fannin aikin gona. Ya auri Samia Suluhu Hassan a shekarar 1978, kuma Allah ya albarkace shi da ƴa'ƴa huɗu.

Sun shafe kusan shekaru 50 tare a matsayin ma'aurata.

A shekarar 2021, lokacin da Samia ta zama Shugabar Tanzania, Haafid ya zama mijin shugabar ƙasa mace ta farko a tarihin ƙasar.

Duk da cewa ya samu wannan matsayin, bai riƙa amfani da shi wajen halartar tarukan shugaban ƙasa akai-akai ba.

Ba kasafai ake ganinsa tare da Samia ba, kuma bayanai game da rayuwarsa ta na da ƙaranci sosai.

Daga cikin ƴaƴansu akwai Wanu Xaafid Ameir, wadda ƴar siyasa ce, kuma ƴar majalisar dokoki mai wakiltar mazaɓar Makunduchi, tare da riƙe mukamin Mataimakiyar Ministan Ilimi, Kimiyya da Fasaha.