Muna da ƙarfin ikon kai wa jiragen ruwan Amurka hari - Iran

Asalin hoton, iRNA
Muƙaddashin ministan tsaron Iran Majiɗ Ibn-e-Reza, ya ce dakarun sojin ƙasar suna da ƙarfin ikon kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka.
A cikin ƴan kwanakin da suka gabata, jami'an Iran sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu a Tekun Fasha, ta hanyar amfani da makamai masu linzami da ake amfani da su wajen kai hari kan jiragen ruwa.
Sakataren majalisar ƙoli ta tsaron ƙasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya ce cikin sa'o'i 48 da suka gabata, dakarun sojin Iran sun samu damar gwada makamin da aka ƙera a ƙasar.
Ya ce: “A karon farko, mun gwada wani makami mai linzami na Iran da aka ƙera domin kai hari kan jirgin yaƙi, a kan wani jirgin ruwan Amurka. Wannan makami ya jefa Amurkawa cikin wani hali na tashin hankali, kuma suka gudu.”
Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM, ba ta mayar da martani kai tsaye kan iƙirarin Iran ba.
Sai dai jiya, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ta yi alamar cewa ta na magana ne kan harin da aka ce an kai wa jiragen ruwanta guda biyu.
Ta ce: “Idan kuka harbi jiragen ruwanmu guda biyu, za mu kakaba muku wani mummunan takunkumin tattalin arziki, tare da lalata jiragen ruwanku guda uku.”
CENTCOM ta ƙara da cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen kare sojojin Amurka ba, kuma idan ya zama dole, za ta lalata jiragen ruwan dakon mai na Iran.
















