Shin yanzu zamanin Arsenal ne?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alex Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai kawo rahoto kan ƙungiyar Arsenal
- Lokacin karatu: Minti 5
Abin mamaki ne yadda Arsenal fa faɗa cikin mawuyacin hali a baya-bayan nan, amma sai ga shi a yanzu ta kai wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai ta Champions League.
Matsi ya tattaru a kan Mikel Arteta domin ganin ya kawo ƙarshen shekara 22 da ƙungiyar ta yi tana ƙamfar kofi.
Ƙoƙarin da suka nuna na kauce wa rashin yin nasara a dukkanin wasan da suka buga na Chamiopns League abu ne da har yanzu bai samu yabon da ya cancanta ba.
Ƙwallon da Bukayo Saka ya jefa a raga kafin zuwa hutun rabin lokaci shi ne ya bai wa Arsenal nasarar da ta samu 1-0 a kan Atletico Madrid a daren ranar Talata, wanda hakan ke nufin an tashi da jimillar ƙwallaye Arsenal 2-1 Atletico Madrid daga wasa biyu da ƙungiyoyin suka buga.
A gaskiyar lamari, duk da cewa wasan da suka buga a filin wasa na Emirate bai ƙayatar sosai ba, Arsenal ɗin ta yi ƙoƙari sosai a wasanninta na gasar Turai.
Arsenal ce ƙungiyar da har yanzu ba ta yi rashin nasara ba a gasar tun daga farkon wannan kaka, inda ta lallasa ƙungiyoyi kamar Bayern Munich da Inter Milan da kuma Sporting kafin kawowa wannan matsayi.
Kuma za a iya cewa Arsenal ta nuna rashin tausayi a wasanninta na gasar, kusan za a iya cewa babu wani lokaci da ta shiga wani babban haɗarin da za a ce tana fargabar za a fitar da ita.
"Ba na tunanin wani zai raina ƙoƙarin da muka yi a wannan gasa har zuwa wannan lokaci," in ji dan wasan tsakiya na ƙungiyar Declan Rice lokacin tattaunawarsa da Amazom Prime.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Muna da hujjar da za mu yi murna a wannan lokaci. Gasa mafi daraja a ƙwallon ƙafa."
"Gabanin fara wasan mun san irin haɗarin da muke fuskanta, idan ba mu tunkare shi ba, to ba za ka iya tunkarar kowane wasan ƙwallon ƙafa ba.
Lokacin da muka ci ƙwallo ta farko, na san cewa za mu yi nasara. Na ji a jikina cewa wani muhimmin abu ya tunkaro mu."
Magoya bayan Arsenal sun tarbi motar bas din da ta ɗauko ƴan wasan da wasan tartsatsin wuta da sowa, wani abu da ba a saba gani ba - wani abu da mai horaswa Mikel Arteta ya bayyana a matsayin dare na musamman.
"Mun kafa tarihi gaba ɗayanmu," in ji Arteta. "Na yi matuƙar farin ciki kuma ina alfahari da duk wanda ya taimaka wa wannan ƙungiya. Yadda aka tarbe mu a lokacin da muka iso abu ne na mausamman.
"Goyon bayan da aka nuna mana ya ƙara mana kuzari, ban taɓa ganin irin wannan lamari ba."
"Mun san yadda kowa ke ji game da haka, ƴan wasan sun yi duk abin da ya dace, kuma ga shi bayan shekara 20 a karo na biyu mun je wasan ƙarashe na gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Ƙoƙarin Arsenal a faifai
A ƴan makonnin nan, Arsenal na ta ƙoƙarin samun nasarori a ƙarshen kakar wasanni ta bana.
Bayan nasarar doke Fulham da ci uku da nema a ƙarshen makon jiya, Arsenal ta da magoya bayanta sun bayyana farin ciki.
Wannan nasarar ta zo a daidai lokacin da ake nemanta, wato kafin wasan ƙungiyar na kusa da ƙarshe. Sai kuma nasarar da ta samu ta zuwa wasan ƙarshe na gasar zakarun turai. Wani ƙarin arashin shi ne ƙwallo shida kawai aka zura a ragar ƙungiyar.
Da aka tambaye shi ko yana alfahari da nasarar da ƙungiyar ke samu, Arteta ya ce, "ƙwarai da gaske domin mun san ƙarfin ƙungiyoyin da muka fafata da su a kowane mataki."
"Atletico babbar ƙungiya ce kuma tana da ƙarfi sosai. Mun san irin ƙoƙarin da take yi da irin rawar ganin da take nuna."
Ga yadda Arsenal ta kai wasan ƙarshe:
- Wasa 14 ta buga kuma ba a doke ta a ko ɗaya ba a zakarun na turai. Wannan lokaci mafi tsawo da ƙungiyar ta yi ba tare da rashin nasara ba bayan wasa 13 da ta yi ba tare da rashin nasara ba a tsakanin watan Maris na 2005 zuwa Afrilun 2006.
- Arsenal ta kai wasan ƙarshe na zakarun turai a karon farko tun shekarar 2006. Wannan lokaci mafi tsawo da ƙungiya za ta kai wasan ƙarshe a gasannin turai manya biyu - Europa da zakarun turai - bayan Atletico da ta kai shekara 40 kafin ta kai wasan ƙarshe a 2014.
- A wasa 14 da Arsenal ta buga, ba a zura mata ƙwallo ba a guda tara.
Yiwuwar lashe kofuna biyu
Canjaras da Man City ta yi da Everton ya ƙara ba Arsenal damar sa rai wajen lashe kofin Premier ɗin ta bana.
City ta ɓarar da babbar damar ce mako biyu bayan Arsenal ta yi rashin nasara a gasar, inda aka fara tunanin tamkar ta watsar da damar lashe gasar premier ta bana bayan dogon dako da ta yi.
Amma bayan doke Atlatico da kuma zama ɗerere a saman teburin premier ɗin da maki biyar, yanzu kusan za a iya cewa ta fi kusa da nasara.
"Irin ƙoƙarin da ƙungiyar nan take ta yi a cikin shekarun nan abin lura ne," in ji Rice a lokacin da yake bayyana irin rawar da ƙungiyar ta taka a kaka uku da suka gaba da take ƙarewa a ta biyu.
"Muna ta haƙuri, muna ta aiki tuƙuru tare da goyon bayan kocinmu."
Arteta ya ba mutane mamaki ganin yadda ya fara wasan da Myles Lewis-Skelly mai shekara 19 a tsakiya.
Haka kuma ɗan wasan gaba Viktor Gyokeres, wanda ya zura ƙwallo biyu a ƙarshen makon jiya, ya nuna bajinta matuƙa, domin wasan na cikin wasannin da ya fi ƙwazo.
Rice na cikin ƴanwasan da suka taimakon Arsenal a kakar bana, inda ko a wasan Atletico shi ne ya zama gwarzon ɗanwasa.
Yanzu kallo ya fara komawa filin wasa na Emirate, inda ake sa ran wataƙila Arteta ya samu nasarar share wa magoya bayan Arsenal hawaye na samun kofi babba a kakar bana.











