Hotunan yadda tsananin zafi ya takura wa al'ummar Turai

An wallafa

An dauki waɗannan hotunan ne a lokacin da aka zabga zafi a Birtaniya, inda birnin London ya zama ɗaya daga cikin wurare mafi zafi a duniya.

.
Bayanan hoto, Yadda rana ta fito a Mevagissey Harbour da ke Cornwall a ranar da tsananin zafi ya kai maki 41 a ma'aunin celcius.
.
Bayanan hoto, A kusa da Mevagissey Harbour, masu kamun kifi ne suka yi samako domin kama kifi.
..
Bayanan hoto, A Penzance da ke Cornwall, masu kurme ne suka faɗa cikin ruwa jim kaɗan bayan rana ta fito.
..
Bayanan hoto, Yadda wani mai gida ya rufe tagogin gidansa da leda domin guje wa hasken rana
...
Bayanan hoto, Yadda wata hanya da ke Dunsden, Oxfordshire ta bushe kuma ta tsage sakamakon ƙarancin ruwan sama
..
Bayanan hoto, Wani jinjirin biri da ke ƙoƙarin shan iska a gidan zoo na Chessington
...
Bayanan hoto, Yadda wani ɗalibi a kudu maso yammacin London Muhammed Ismail Moosa ke ba itace ruwa a Palm House
...
Bayanan hoto, Yadda wasu matasa ke tafiya cikin kwale-kwale da sanyin safiya a Bristol
.
Bayanan hoto, Yadda ake ba wani dokin ƴan sanda ruwa daga bokiti a Whitehall da ke tsakiyar Birnin London.
..
Bayanan hoto, Joanne Dunwell da ɗanta mai wata takwas na son su sha iska a wani gulbi da ke Edinburgh
..
Bayanan hoto, A nan kuma ana shayar da ɗaya daga cikin sojojin Sarauniyar Ingila ruwa a wajen fadar Buckingham da ke tsakiyar birnin Londan
..
Bayanan hoto, Wata mata kenan a lokacin da take ƙoƙarin shan sanyi ta hanyar tsoma ƙafafuwanta cikin Kogin Thames da ke kusa da Chertsey a Surrey.
..
Bayanan hoto, Jasmine Bowers da ƴarta wadda ke tsotsar alewa mai tsinke a wajen gidansu da ke arewacin Belfast.