Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Darajar Mbappe ta zube a China, bisa barkwanci kan shugaba Mao Zedong
Dan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe yana fuskantar koma baya a kasar Sin bayan kalamansa game da shugaba, Mao Zedong, lamarin da ya bi sahun katse huldar kasuwanci tsakaninsa da wasu kamfanonin kasar
Batun ya hada da yin fushi daga masu amfani da intanet da nesanta kai da kamfanonin China da suka yi da takunkumin da aka dora kan masu amfani da abin da ya danganci dan wasan da kuma tsoma bakin hukumomi.
A cikin sa'o'i 24 bayan bayyana wani gajeren bidiyon tattaunawar da kyaftin din Faransa ya yi, inda ya bayyana tsohon shugaban Sin, Mao a matsayin "wani mutum ne kawai, ina tsammanin wani mai mulkin kama-karya na kasar Sin ne", kamar yadda ya fada.
Koda yake Mbappe ya bayar da shawara kan kalaman da ya yi, Shugaban La Liga da Real Madrid dun sun bayar da hakuri kan rashin jin dadi da kalaman na kyaftin din Faransa da ya haifar.
Sai kawai masu huldar talla da dan wasan na Faransa ciki har da Mengniu Dairy, Shanghai Milkground da kamfanin abin sha na Eastroc suka kawo karshen hadin gwiwarsu da dan wasan.
Gidan talabijin na gwamnati CCTV ya cire tallace-tallacen da suka shafi Mbappe, yayin da dandamalin sada zumunta na kasar Sin suka takaita samun damar shiga shafukansa. Mbappe ya nemi afuwa ranar Talata, yana mai cewa kalaman nasa "ba a yi tunani sosai a kansu ba".
Yaduwar illar lamarin ba sabon abu ba ne ga kamfanonin, kayayyakin kasuwanci da fitattun mutane masu hulda da kasuwar kasar Sin. Masana sun ce wannan sabon misali ne da ke nuna irin hadarin kasuwanci da har yanzu ke da wahalar tafiyarwa da ya dauki shekaru yana faruwa ta irin wadannan rikice-rikice.
Kamfanonin kasashen waje sun sha fuskantar fushin jama'a a kasar Sin, tun daga soke shirin nuna kayan kwalliya na Dolce & Gabbana a Shanghai a shekarar 2018, neman afuwa da Versace, Dior mallakin LVMH da Coach na Tapestry suka yi a 2019, zuwa kaurace wa kayayyakin H&M, Nike da Adidas saboda batun audugar Xinjiang da kuma sabanin da ya barke tsakanin NBA da CCTV bayan wani jami'in Houston Rockets ya nuna goyon baya ga masu rajin dimokuradiyya a Hong Kong.
Ko da yake cikakkun bayanan suna bambanta, tsarin rikice-rikicen kusan iri daya ce: wato ko dai yin kalamai ko nuna hoto ko sanarwar da za ta jawo cece-kuce da za ta yadu a intanet, abokan hulda na kasuwanci sun fuskanci matsin lamba ta mayar da martani, sannan illar da take yi tana zarce girman abin da ya jawo rikicin tun farko.
Michael MacRitchie, wanda ya kafa MGI Group da ke hada fitattun mutane na duniya da kamfanonin kasar Sin, ya ce:
"Ba sai ka yi tunanin kamar dan kasar Sin ba, domin ka yi nasara a kasar Sin, amma dole ne ka fahimci yadda masu sauraro a kasar Sin za su mayar da martani da kuma tasirin al'adu idan ba haka ba za ka fada matsala."
Batun Girmamawa
Abin tambaya a irin wadannan lokuta shi ne yawan fushin da ake gani yana nuna hakikanin bacin ran jama'a ne ko kuma wani bangare na tasirin kafafen yada labarai na gwamnati, dandamalin intanet da kuma hukumomi.
Batun Mbappe ya nuna yadda yake da wahala a bambance wadannan abubuwa. Yayin da rikicin ke ci gaba, ainihin kalaman da ya yi game da Mao ba za ka samu ba cikin sauki a Intanet, saboda matakan tace abubuwa daga gwamnatin Sin.
Saboda haka, mutane da dama ba su ji kalamansa kai tsaye ba, sai dai rahotannin cewa masu daukar nauyinsa sun rabu da shi kuma kafafen watsa labarai na gwamnati suna sukar sanar da hakan.
Mark Dreyer, masanin harkokin wasanni kuma marubucin littafin Sporting Superpower da ke magana kan burin kasar Sin a fannin wasanni, ya ce:
"A wannan yanayin, abin da muka gani wani nau'i ne na fushin da aka samar da shi a wani mataki."
Sai dai ya gargadi cewa gasar kungiyoyi da 'yan wasa ba za su yi tasiri ba idan suka raina irin martanin da irin wadannan lamura ke haifarwa.
"Ba za a ga suna bai wa 'yan wasansu umarni kai tsaye kada su fadi wani abu da zai bata wa kasar Sin rai ba," in ji shi.
"Amma babu shakka a bayan fage ana gaya musu su yi taka-tsantsan, su kasance masu tunani kuma su fahimci cewa irin wadannan martani na iya faruwa."
Zak Dychtwald, wanda ya kafa BridgeWorks Global mai ba kamfanoni masu aiki a kasashe da dama shawara, ya ce duk da cewa irin wadannan rikice-rikice har yanzu suna faruwa, ana iya kauce musu.
"Idan kana shiga wannan kasuwa, ana sa ran za ka mutunta yadda kasar Sin ke kallon kanta kuma kana fahimtar asali game da hakan. Koyar da mutane inda jan layi yake ya kamata ya zama tushen komai," in ji shi.
Wani kalubale ga kamfanoni da gasa da fitattun mutane shi ne cewa duk da ana fahimtar galibin batutuwan siyasa da al'adu masu matukar muhimmanci a kasar Sin, sau da yawa ba a fayyace iyakokinsu a sarari.
Wannan rashin tabbas kan sa kamfanoni da abokan hulda su nesanta kansu da mutane masu janyo cece-kuce tun kafin a tantance cikakken girman abin da ya faru.
Wei Kan, wanda ya kafa kamfanin bayar da shawara na Conduit Asia, ya ce:
"Babu wata doka karara da ke nuna abin da ya ketare iyaka."
Ya kara da cewa iyakar tana sauyawa ne bisa "yadda masu amfani ke ji, yanayin da al'umma ke ciki da kuma yadda dandamali da kafafen yada labarai ke kara yada labari."
Ga kamfanonin kasashen waje, irin wadannan batutuwa masu sarkakiya na kasar Sin bai kamata su zo musu da mamaki ba. Amma masana sun ce har yanzu ana kallon hadurran siyasa da na al'adu a matsayin abubuwan da ba su da muhimmanci sosai maimakon a dauke su a matsayin hadurran kasuwanci na yau da kullum.
MacRitchie ya ce kamfaninsa na sanya sharuddan halayya da kare suna a cikin kwantiragin tallace-tallace, yayin da wasu ke nuna muhimmancin ba da takamaiman bayanai game da kasuwa, horas da mutane kan hulda da kafafen yada labarai da kuma shirye-shiryen tunkarar rikici a matsayin matakan kariya da suka zama wajibi.
Dychtwald ya ce:
"Idan abubuwa suna tafiya daidai, kowa yana murna.
"Amma idan ka yi kuskure game da kasar Sin, sakamakon zai iya kasancewa mai zafi sosai kuma cikin sauri."