Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun malaman Musulunci 7 da aka yi wa kisan gilla a arewacin Najeriya
Kisan da wasu ƴanbindiga suka yi wa fitattcen malamin Addini Musulunci, Sheikh Yahaya Masusuka a jihar Katsinan Najeriya ya sake taso da tattaunawa kan kisan gillar da ake yi wa fitatun malaman addini arewacin ƙasar.
A ranar Litinin da maraice ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka buɗe wa malamain wuta jim kaɗan bayan fita daga gidansa domin halartar wurin da yake karantawar.
Shaidu sun ce an garzaya da malamin zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Ba wannan ne karon farko da ake yi wa malamin kisan gilla ba a arewacin Najeriya ba.
A wannan mukala za mu duba wasu fitattun malamai biyar da aka taɓa yi wa kisan gilla a arewacin ƙasar.
Sheikh Yahaya Masussuka - 2026
A ranar Litinin 26 ga watan Oktoban 2026 ne wasu mahara a kan babur suka buɗe wa malamin wuta a ƙofar gidansa.
Malamin ya sharaha wajen aƙidarsa ta bin koyarwar Al'qur'ani kaɗai ban da hadisai, wani abu da ya jano masa suka daga wasu malaman addinin.
Malamin ya shafe fiye da shekara 30 yana wa'azi, bayan kammala karatuttukansa a wurare daban-daban ciki har da Jami'ar Al-Azhar da ke ƙasar Masar
A tsawon rayuwarsa ya fuskanci ƙalubale daban-daban yayin gudanar da ayyukan wa'azinsa, ciki har da ƙoƙarin kama shi da kuma kiransa da jami'an tsaro ke yi.
Sheikh Albani Zariya - 2014
A watan Fabrairun 2014 ne kuma wasu mutane ɗauke da makamai suka halaka fitaccen malamin addini Sheikh Albani Zariya.
An kashe malamin tare da matarsa da kuma ɗansa a lokacin harin.
Shaidu a lokacin sun ce maharn sun kashe malamin tare da iyalansa a lokacin da suke cikin mota a kan hanyarsu ta komawa gida bayan tashi daga makarantar da yake koyarwa a cikin garin Zariya da ke jihar Kaduna.
Sheikh Goni Tijjani - 2011
Sheikh Goni Tijjani, fitaccen malamin addinin Musulunci ne a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
An kashe shi ne ranar 9 ga watan Mayun 2011 a gidansa da ke birnin Maiduguri.
Masu bincike sun danganta hare-haren da adawar da malaman suka nuna wa Boko Haram, kodayake ƙungiyar ba ta ɗauki alhakin kisan ba.
An kashe malamin ne a lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ƙungiyar a birnin Maiduguri.
Sheikh Ali Jana'a - 2011
An harbe Sheikh Ali Jana'a a wajen gidansa da ke unguwar Bulabulin Ngarnam a Maiduguri.
Wasu bayanai sun zargi ƙungiyar Boko Haram da kai masa hari, bayan da aka ce ƙungiyar ta zarge shi da bai wa jami'an tsaro bayanai game da ayyukan ƙungiyar.
Kisan nasa ya faru ne a lokacin da Boko Haram ke ƙara kai hare-hare kan mutanen da take ganin abokan gaba ne ko kuma masu taimaka wa jami'an tsaro.
Sheikh Ibrahim Birkuti - 2011
Sheikh Ibrahim Birkuti malamin addinin Musulunci ne da shi ma aka zarga da sukar ayyukan ƙungiyar Boko Haram a Maiduguri.
An kashe shi a wani harin da aka kai masa a wajen gidansa a watan Yunin 2011 a Maiduguri.
Binciken cibiyar yaƙi da ta'addanci ta Afrika ya ambaci kisan nasa cikin hare-haren da aka kai wa malaman addinin Musulunci da suka nuna adawa da akidar ƙungiyar.
Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam - 2007
Shekih Ja'afar ya kasance aya daga cikin fitattun malaman Addinin Musulunci mafiya tasiri a Najeriya.
Ƙwararren masanin tafsiri da hadisi da ya yi fice wajen sanin hukunce-hukunce.
A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu yanbindiga suka buɗe masa wuta yayin da yake tsaka da jagorantar sallar Asuba a masallacinsa da ke Gadon Ƙaya a birnin Kano.
Kisan malamin ya haifar da tambayoyi daga mabiyansa da masoyansa, kan abin da ya sa aka kashe shi.
Shekih Ja'afar ya yi fice a lokacinsa wajen sukar a kidun Boko Haram, wadda ta fara a lokacin.
Malamin na ɗaya daga cikin manyan malaman addini a ɓangaren mabiya Sunnah da ke da ɗimbin magoya baya.
Sheikh Umaru Ɗanmaishiyya - 2007
Sheikh Ɗan maishiyya fitaccen malamin addinin ne da ya yi fice a shekarun 2000.
Wasu Mahara ne suka kashe shi ranar 18 ga watan Yulin 2007, a kan hanyarsa da komawa gidansa bayan idar da sallar Isha'a a masallancinsa da ke birnin Sokoto.
Kisan malamin ya haifar da arangama da rikici tsakanin mabiyansa da wasu masu bin aƙida daban da tsa.