Wane mataki INEC za ta ɗauka kan Pantami da Gwarzo?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Nan gaba a yau ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC za ta fitar da matsaya kan wasu yantakarar gwamna da ta cire sunayensu daga cikin jerin yantakara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Daga cikin fitattun sunayen da ake sa ran ganin makomarsu a yau ɗin har da ɗantakarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Farfesa Ali Isa Pantami, da ɗantakarar gwamnan Kano na NDC Comdr. Aminu Abdussalam gwarzo.

Haka ma akwai sunayen ɗan takarar gwamnan Kaduna na NDC, Sanata Danjuma Laah da ɗan takarar gwamnan Jihar Benue na jam'iyyar SDP, Sebastine Hon.

A makonnin da suka gabata ne INEC ta fitar da sunayen ƴantakarar gwamna, amma kuma babu sunayen waɗannan yantakara.

Comdr. Aminu Abdussalam Gwarzo da Farfesa Pantami su ne manyan ƴantakarar hamayya a jihohinsu, kuma suke da ɗimbin magoya baya.

Akwai kuma ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Ogun Ladi Adebutu, da na NDC a Kaduna Danjuma La'ah, da wasu ƴantakarar gwamna na SDP a wasu jihohi guda shida da suma aka cire sunayensu.

Wani abu da masu lura da al'amuran siyasa ke ganin fafatawar zaɓen gwamna za ta yi zafi a jihohinsu.

Me ya sa INEC ta cire sunayen nasu?

A lokacin fitar da jerin sunayen hukumar zaɓen Najeriyar ta bayyana cewa ta cire sunayen wasu ƴan takarar ne saboda jam'iyyunsu sun gaza gabatar da kundin rajistar mambobinsu kamar yadda doka ta tanada.

A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan fitar da sunayen ƴantakarar, INEC ta ce ta dogara ne da hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari'ar INEC a ZLP, wajen cire sunayen nasu.

A cewar INEC hukunicn kotun kolin ya tabbatar da sahihancin Sashe na 77(5)–(7) na Dokar Zaɓe ta 2026 a ƙarƙashin kundin tsarin mulki.

''Waɗannan tanade-tanaden sun wajabta wa jam'iyyun siyasa su miƙa rijistar mambobinsu ga hukumar cikin lokacin da aka tsara'', in ji sanarwar.

INEC ta ƙara da cewa kotun ta kuma tabbatar da jadawalin INEC da ya buƙaci jam'iyyun su miƙa rijistar tsakanin ranar 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.

A cewar hukumar, Kotun Ƙolin ta yanke cewa jam'iyyun da suka kasa cika waɗannan buƙatu ba su cancanci tsayar da 'yan takara a zaɓen ba.

Wanne mataki jam'iyyun yantakarar suka ɗauka?

Jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe, wadda Pantami ke yi wa takarar, ta ce tana da yaƙinin za a gyara abin d ata kira kuskuren da INEC ta yi wajen cire sunan ɗantakarar tata.

A wata sanarwa da kakakin tafiyar Pantamiyya, Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya fitar a lokacin ya ce jam'iyyar da kuma INEC sun fara tattaunawa, domin ganin an gyara lamarin cikin wa'adin da doka ta tanada.

"Wannan ƙalubale ne na ɗan lokaci, amma lallai ba wai mataki na ƙarshe ba ne," in ji sanarwar.

Ta kuma buƙaci magoya bayan Pantami da na ƙungiyar Pantamiyya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da tattara goyon baya, tare da mai da hankali kan manufofin da suka sa suka shiga siyasa.

Shi ma jagoran tafiyar, Farfesa Ali Pantami cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a baya-bayan nan ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankali, yayin da yake bayyana ƙwarin gwiwar samun nasara.

A nata ɓangare ƙungiyar Kwankwasiyya, wadda Aminu Abdussalam ke yi wa takara ta bayyana matakin a matsayin kuskuren da ta ce tana da yaƙinin INEC za ta gyara.

Sakataren ƙungiyar, Dokta Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya shaida wa BBC cewa lamarin bai tayar masu da hankali ba.

''Na farko dai ɗan takararmu na gwamna a jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya riga ya yi rajista da jam'iyyar NDC kuma ya yi ta a kan lokaci, sannan abu na biyu kuma shi ne bai yi rajista da jam'iyya biyu ba, a don haka wannan hukunci na kotun ƙoli ba zai shafe shi ba,'' in ji shi.

Ko INEC na da hurumin cire sunan ɗantakara?

Ɗaya daga cikin tambayoyin da ƴan ƙasar da dama ke yi ita ce ko INEC na da hurumin cire sunan ɗantakarar da aka miƙa mata?

Farfesa Nasiru Aliyu SAN, babban ƙwararren lauya ne a ƙasar, kuma masanin dokokin ƙasar ya ce sam hukumar ba ta da hurumin cire sunan kowane ɗantakara.

''Abin da doka ta ba ta dama shi ne ta karɓi sunayen ƴantakara daga jam'iyyu, sannan ta wallafa su domin tsayawa zaɓe'', in ji shi.

Ya ce in ma da matsala kan saɓa ƙa'ida na yadda wani ya zama ɗantakara kotu ce kawai za ta tantance hakan, ta kuma bayar da umarnin cire sunansa.

Shi ma Barista Danbaba Gangei wani lauya a ƙasar, ya ce hukumar zaɓen ba ta da hurumin cire sunayen ƴantakara.

''Ko da an bayar da sunan ba daidai ba, ko kuma an saɓa ƙa'ida wajen bayar da sunan, INEC ba ta da hurumin cire suna'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa kotu ce kawai ke da wannan hurumi na cire sunan wani ko kuma saka sunan wani.