Biranen duniya 10 mafiya yawan jama'a a 2026

Dandazon mutane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da jama'ar duniya ke ci gaba da ƙaruwa, birane na zama cibiyoyin tattalin arziki da ilimi da ci gaban al'umma.

Wannan ya sa wasu birane suka cika da miliyoyin mutane fiye da kowane lokaci a tarihi.

Wani sabon rahoton World Popolation Review na 2026 ya sake fayyace jerin biranen duniya mafiya yawan jama'a a shekarar 2026.

Rahoton ya nuna cewa manyan biranen Asiya ne kan gaba a jerin biranen da ke da yawan jama'a.

Sai dai abin da ya ja hankali shi ne yadda birnin Kano da ke arewacin Najeriya ya shiga sahun birane 10 na farko da suka fi yawan jama'a a duniya.

Lamarin da ke nuna saurin haɓakar yawan jama'arsa da faɗaɗar birnin cikin shekaru da dama da suka gabata.

Ko a ƙidayar jama'ar da Najeriya ta yi a 2006, Kano ta kasance kan gaba a yawan jama'a a Najeriya.

A wannan muƙala mun duba rahoton tare da kawo muku jerin biranen duniya 10 da suka fi yawan jama'a a duniya a 2026

Shanghai

Mutane

Asalin hoton, Getty Images

Birnin Shanghai da ke ƙasar China ne kan gaba yawan al'umma a duniya a cewar rahoton na World Population Review.

Birni ne da ke gaɓar ruwa, wanda yake cike da ƴankasuwa da ke harkokin hada-hada.

A cewar rahoton na World Population Review Shanghai na da yawan jama'a sama da miliyan 24.7.

Birnin ne mai matuƙar muhimmanci ga ƙasar China, wanda ke samar da kusan kashi 30 cikin 100 na tattalin arzikin ƙasar.

Delhi

Hoton Delhi

Asalin hoton, Getty Images

Babban birnin ƙasar Indiya, na daga cikin biranen da suka fi yawan jama'a a duniya, inda ya zo na biyu a jerin biranen duniya mafi yawan jama'a na shekarar 2026, a cewar rahoton World Population Review.

Birnin na da muhimmanci sosai a fannonin siyasa da kasuwanci da harkokin gwamnati, kasancewarsa cibiyar mulkin ƙasar Indiya.

Delhi na ɗaya daga cikin biranen da suka fi saurin karɓar baƙi sakamakon ƙaurar jama'a daga sassa daban-daban na ƙasar.

Rahoton ya nuna cewa Delhi na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 23.3, lamarin da ya sa ta kasance ɗaya daga cikin manyan biranen duniya mafi cunkoson jama'a.

Birnin na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin tattalin arziki da ci gaban Indiya, tare da taka rawa mai muhimmanci a bunƙasar ƙasar.

Kinshasa

Mutane

Asalin hoton, Getty Images

Babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), na daga cikin biranen da suka fi yawan jama'a da saurin bunƙasa a nahiyar Afirka.

A cewar rahoton World Population Review, birnin na cikin jerin manyan biranen duniya mafi yawan jama'a a shekarar 2026.

Kinshasa ce cibiyar siyasa da tattalin arziki da al'adun DR Kongo. Birnin ya shahara da kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a yankin tsakiyar Afirka.

Rahoton ya nuna cewa Kinshasa na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 21.8 lamarin da ya sa ta zama ɗaya daga cikin biranen da suka fi yawan jama'a a Afirka.

Mumbai

Mutane

Asalin hoton, Getty Images

Mumbai, wadda aka fi sani da cibiyar kasuwanci da kuɗi ta ƙasar Indiya, na daga cikin biranen duniya mafi yawan jama'a.

Birnin wanda ke gefen Tekun Arabian Sea, ya kasance hedikwatar manyan kamfanoni da cibiyoyin kuɗi na Indiya.

Mumbai ta shahara da masana'antar fina-finantan Indiya ta Bollywood, wadda take ɗaya daga cikin mafi girma a duniya.

Rahoton World population Review ya nuna cewa Mumbai na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 21.7, lamarin da ya sanya ta cikin biranen duniya mafi cunkoson jama'a.

Beijing

Dandazon mutane

Asalin hoton, Getty Images

Babban birnin ƙasar China, na daga cikin biranen duniya mafiya yawan jama'a kuma mafi tasiri a harkokin siyasa da tattalin arziki.

Birnin shi ne cibiyar gwamnatin China, inda manyan hukumomin ƙasar da cibiyoyin jakadancin ƙasashe duniya yake.

Rahoton ya nuna cewa Beijing na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 21.5.

Duk da ƙalubalen da ke tattare da cunkoson jama'a da gurɓacewar muhalli, Beijing na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tattalin arziki da fasaha da ilimi a duniya, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar ƙasar China.

Karachi

Mutane

Asalin hoton, Getty Images

Karachi, birni mafi girma a ƙasar Pakistan, na daga cikin biranen duniya mafi yawan jama'a kuma muhimmin cibiyar tattalin arziki a yankin Kudancin Asiya.

Birnin, wanda ke gaɓar Tekun Arbian Sea, shi ne cibiyar kasuwanci da masana'antu da harkokin kuɗi na Pakistan.

Hakanan tashar jiragen ruwansa tana daga cikin mafi yawan hada-hadar kasuwanci a ƙasar.

Rahoton ya nuna cewa Karachi na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 21.2.

Shenzhen

Shenzhen Market

Asalin hoton, Getty Images

Shenzhen na ɗaya daga cikin manyan biranen ƙasar China kuma mafi saurin bunƙasar tattalin arziki.

Birnin, wanda ke kudancin China kusa da Hong Kong, ya kasance ƙaramin garin kamun kifi, kafin gwamnatin China ta ayyana shi a matsayin yankin bunƙasa tattalin arziki a shekarun 1980.

Tun daga lokacin, Shenzhen ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin fasaha da masana'antu a duniya.

Rahoton ya nuna cewa Shenzhen na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 20.6.

Haka kuma birnin ya kasance hedikwatar manyan kamfanonin fasaha na China, ciki har da Huawei da Tencent.

Guangzhou

Taron jama'a

Asalin hoton, Getty Images

Guangzhou da ke lardin Guangdong da ke kudancin ƙasar, ya kasance ƙofar kasuwanci tsakanin China da sauran sassan duniya.

Haka kuma ya shahara da baje kolin kasuwanci na Canton Fair, wanda yake ɗaya daga cikin manyan bukukuwan kasuwanci mafi girma a duniya.

Rahoton ya nuna cewa Guangzhou na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 18.5.

Kano

Mutanen Kano

Asalin hoton, Getty Images

Birni mafi girma a arewacin Najeriya, na daga cikin biranen da suka fi yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Kano, wadda ke ɗaya daga cikin tsofaffin biranen Afirka ta Yamma, ta daɗe da kasancewa cibiyar kasuwanci da sana'o'i da harkokin al'adu a arewacin Najeriya.

Matsayinta na cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya da maƙwabtan ƙasashe ta taimaka wajen haɓakar tattalin arzikinsa tsawon shekaru.

Rahoton ya nuna cewa Kano na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 17.

Yawan al'ummar Kano da faɗaɗar birnin na nuna irin muhimmiyar rawar da take takawa a tattalin arziki da ci gaban ƙasar.

Chengdu

Mutane

Asalin hoton, Getty Images

Chengdune birni na biyar daga ƙasar China da suka samu shiga jerin biranen duniya 10 da suka fi yawan jama'a a duniya a 2026.

Birnin ya shahara wajen haɗa tsoffin al'adun China da ci gaban zamani, sannan kuma gida ne ga fitattun namun daji, abin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido mafiya jan hankali a ƙasar.

Rahoton ya nuna cewa Chengdu na da yawan jama'a da ya haura mutum miliyan 15.8.

Chengdu ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin fasaha da bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a China.

Birnin na ci gaba da jan hankalin masu zuba jari da kamfanonin cikin gida da na ƙetare, wanda ke ƙara ƙarfafa matsayinsa a tattalin arzikin ƙasar.