Malaman KASU fiye da 200 ne suka bar jami'ar - ASUU

Asalin hoton, Uba Sani/X
ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) reshen jami'ar jihar Kaduna (KASU) ta ce malamai fiye da 200, ciki har da furofesoshi, sun bar jami'ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU a 2025.
Shugaban ASUU-KASU, Dakta Abubakar Abdullahi, ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin, inda ya ce mafi yawan malaman da suka fice sun samu aiki a sabbin jami'o'i da ke ciki da wajen jihar Kaduna.
Ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar, wadda ta fara aiki tun watan Janairun 2026, ya sanya malaman KASU cikin mafi ƙarancin albashi tsakanin ma'aikatan jami'o'i a Najeriya.
ASUU ta bai wa gwamnatin jihar Kaduna da mahukuntan jami'ar wa'adin makonni biyu su fara aiwatar da yarjejeniyar, tare da gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo yajin aikin sai baba-ta-gani a jami'ar.


















