Jerin ƴantakarar gwamna na jam'iyyar NDC a Najeriya

Asalin hoton, Facebook Multiple
Jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓukan gwamnoni a Najeriya a 2027, yayin da masu neman takara ke fafatawa domin samun tikitin jam'iyyunsu.
Tuni dai jam'iyyun suka fara fitar da sunayen ƴantakararsu a muƙamai daban-daban ciki har da gwamnoni, waɗanda ke cikin muƙamai masu muhimmanci a ƙasar.
Kamar sauran jam'iyyu ita ma jam'iyyar hamayya ta NDC ta fitar da jerin ƴan takarar da za su nemi goyon bayan mambobinta domin jagorantar jihohin ƙasar daban-daban.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na cewa zaɓen fitar da gwani na taka muhimmiyar rawa wajen tantance waɗanda za su shiga babban zaɓe, tare da ba mambobin jam'iyya damar zaɓar waɗanda suke ganin sun fi dacewa da jagoranci.
A wannan rahoto, za mu duba jerin ƴan takarar gwamna na jam'iyyar NDC, tare da bitar bayanansu da kuma jihohin da suke neman jagoranta, kamar yadda jam'iyyar ta fitar.
Aminu Abdussalam Gwarzo (Kano)

Asalin hoton, Aminu Abdussalam Gwarzo/FB
Aminu Abdussalam Gwarzo gogaggen ɗan siyasa ne daga ƙaramar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.
Ya kasance tsohon gwamnan jihar, wanda ya sauka daga muƙaminsa bayan da gwamnan jihar Abba Kabir ya sauka sheƙa zuwa jam'iyyar APC daga NNPP da aka zaɓ shu a 2023.
Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jagororin siyasar kwankwasiyya a jihar Kano, musamman saboda gogewarsa a harkokin mulki da tafiyar da gwamnati.
Kafin ya zama mataimakin gwamnan Kano, Gwarzo ya riƙe muƙaman siyasa daban-daban ciki har da shugaban ƙaramar hukuma da kuma kwamishina.
Kabiru Garba Marafa (Zamfara)

Asalin hoton, Kabiru Marafa/FB
Sanata Kabiru Marafa gogaggen ɗansiyasa ne a jihar Zamfara, wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 da 2019.
Kafin haka ya yi aiki a fannonin gwamnati daban-daban, ciki har da matsayin kwamishina a jihar.
Ya yi suna a siyasar Najeriya saboda yadda yake bayyana ra'ayinsa kan batutuwan da suka shafi shugabanci da yaƙi da cin hanci.
Ana ganinsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar Zamfara masu tasiri.
Aishatu Ahmed Binani (Adamawa)

Asalin hoton, Aishatu Binani/FB
Sanata Aishatu Binani ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mata ƴansiyasa a Najeriya.
Ta kasance mamba a Majalisar Wakilai kafin daga baya ta zama Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya.
Ta samu karɓuwa a siyasance bayan ta zama ɗaya daga cikin fitattun matan da suka nemi kujerar gwamnan Adamawa.
Baya ga siyasa, ta yi fice a harkokin kasuwanci da tallafa wa mata ta hanyar shirye-shiryen bunƙasa rayuwa.
Farfesa Yahaya Mohammed Sani (Taraba)

Asalin hoton, Other
Farfesa Yahaya Mohammed Sani masani ne a fannin ilimi wanda ya riƙe manyan muƙamai a jami'o'i daban-daban.
A zaɓen 2023 Farfesa Sani ya tsaya takarar gwamnan Taraba a jam'iyyar NNPP.
Ya taɓa zama shugaban Jami'ar Taraba kuma ya yi suna wajen ƙoƙarin inganta tsarin ilimi a jihar.
Masu goyon bayansa na cewa gogewarsa a fannin ilimi da gudanarwa na iya taimakawa wajen magance wasu matsalolin ci gaban Taraba.
Aminu Sani Dutse (Jigawa)
Aminu Sani Dutse ɗan siyasa ne daga babban birnin Jihar Jigawa.
Ya shiga fafutikar siyasa da manufar inganta rayuwar matasa da manoma, waɗanda su ne ginshiƙan tattalin arzikin jihar.
Ya daɗe yana shiga harkokin ci gaban al'umma, kuma yana bayyana muhimmancin samar da ayyukan yi da bunƙasa kananan sana'o'i.
Dr. Bolaji Odusina (Ogun)

Asalin hoton, Bolaji Odusina/FB
Dr. Bolaji Odusina ƙwararriyar likitar yara ce wadda ta shafe shekaru da dama tana aiki a fannin lafiya a Amurka.
Baya ga aikin likitanci, ta shahara wajen ayyukan jin ƙai da tallafa wa marasa galihu ta hanyar gidauniyarta.
Ta ce babban burinta idan ta samu gwamna shi ne inganta kiwon lafiya da ilimi da walwalar mata da yara a Ogun.
Dumo Lulu-Briggs (Rivers)

Asalin hoton, Dumo Lulu-Briggs/FB
Dumo Lulu-Briggs sanannen ɗan kasuwa ne kuma shugaban kamfanin Platform Petroleum.
Ya yi fice a harkokin mai da iskar gas, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin fitattun attajiran Jihar Rivers.
Haka kuma ya daɗe yana gudanar da ayyukan jin ƙai ta gidauniyar iyalinsu, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da tallafa wa matasa.
Ya taɓa neman kujerar gwamna a baya, lamarin da ya ƙara masa gogewa a siyasar jihar.
Yakubu Solomon Ndam (Plateau)
Yakubu Solomon Ndam ɗan siyasa ne daga Jihar Plateau kuma yana cikin jiga-jigan jam'iyyar NDC a jihar.
Ya taɓa zama shugaban jam'iyyar NDC na jihar Plateau, inda ya jagoranci ƙoƙarin bunƙasa jam'iyyar zuwa matakin ƙasa.
Ya yi fice wajen kira ga haɗin kai, samar da ayyukan yi da magance matsalolin tsaro a jihar.
Deacon Chris Iyovwaye (Delta)

Asalin hoton, Deacon Chris Iyovwaye/FB
Chris Iyovwaye ɗan kasuwa ne kuma shugaban kamfanonin Wellmann Group.
Ya fito daga ƙaramar hukumar Okpe a Jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya, kuma sananne ne a harkokin kasuwanci da ayyukan addini a matsayin Deacon.
Ya gina sunansa a fannin samar da ayyukan yi da bunƙasa masana'antu, ya kuma ce ya shiga takarar gwamna da manufar kawo ci gaban tattalin arziki da ilimi da kiwon lafiya a jihar Delta.
Farfesa Abdulmumin Yinka Ajia (Kwara)
Farfesa Abdulmumin Yinka Ajia masanin harkokin kasuwanci ne kuma malami a jami'a.
Ya koyar a Jami'ar Lincoln da ke Amurka, kuma ya yi fice wajen bayar da shawarwari kan tsarin mulki da tattalin arziki.
Ya ce ya shiga siyasa da manufar inganta gudanar da gwamnati ta hanyar amfani da fasaha da gaskiya da riƙon amana a Jihar Kwara.
Barrista Ibrahim Kashim (Bauchi)
Ibrahim Kashim lauya ne kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi (SSG).
Ya riƙe manyan muƙamai a gwamnati tare da gogewa a harkokin gyaran tsarin mulki da gudanarwar jama'a.
Ya ce yana takarar gwamna ne da manufofin inganta ilimi da lafiya da noma da samar da ayyukan yi da kuma gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci.
Ibrahim Sanusi Kasim (Borno)
Rear Admiral Ibrahim Sanusi Kasim tsohon babban jami'in rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ne.
Ya yi aiki a muƙamai daban-daban na tsaro da gudanarwa a cikin rundunar ruwa kafin yin ritaya.
Ya ce ya shiga siyasa da niyyar amfani da ƙwarewarsa wajen magance matsalolin tsaro, bunƙasa tattalin arziki da sake farfaɗo da ci gaban Jihar Borno.
Ƴantakarar sauran jihohi
Sauran ƴantakarar jihohin sun haɗa da:
- Jonga Gabakau - Yobe
- Umar Usman Besse - Kebbi
- Shamsudden Aliyu - Sokoto
- Terhemba Shija - Benue
- Dogo Danladi Shimma - Nasarawa
- Yusuf Akim Adebola - Oyo
- Nwofe Boniface - Ebonyi
- Chinyeake Christian Ohaa - Enugu
- John Odeh - Cross River
- Babanta Okon - Akwa Ibom
Haka ma jam'iyyar ta ce ba ta kammala daddalewa kan ƴantakarar jihohi biyar ba da suka haɗa da:
- Gombe
- Kaduna
- Katsina
- Neja
- Legas
Sai kuma jihohi bakwai da ba a yin zaɓen gwamnansu tare da sauran jihohi, don haka ne jam'iyyar ba ta fitar musu daƴantakara ba tukunna da suka haɗa da:
- Imo
- Osun
- Kogi
- Anambra
- Edo
- Ekiti
- Ondo











