Abin da ya kamata ku sani kan lalurar rashin ƙarfin mazakuta

An wallafa

Wani bincike da aka wallafa a mujallar 'Impotence Research' ya nuna cewa fiye da maza miliyan 322 ne a faɗin duniya za su gamu da lalurar rashin ƙarfin mazaƙuta nan da shekarar 2025.

Nikola mai shekara 36 da ke zaune a Belgrade ya shafe lokaci mai tsawo ba tare da saduwa da iyalinsa ba, saboda fama da da lalurar rashin ƙarfin mazakuta.

Ya ce "zan iya saduwa sau da yawa, to amma matsalar a kowanne ba na wuce daƙiƙa 20,''

Ya damu matuƙa kan yadda baya iya gamsar da abokiyar zamansa.

Lalular rashin miƙewar azzakari na daga cikin cutakan rashin ƙarfi da maza ke fama da su, da ke haddasa rashin jin sha'awar saduwa.

Sabon binciken ya nuna cewa, mutum ɗaya cikin kowanne biyar a ƙasar Sabiya na ɗauke da lalurar rashin miƙewar azzakari, kamar yadda alƙaluma daga shafin intanet na magungunan Apoteka suka nuna.

"Kashi 29 cikin 100 na mutanen da ke mu'alama da shafin, na neman magungunan da suka shafi matsalar rashin miƙewar azzakari'', kamar yadda alƙaluman suka nuna.

Me ke haifar da lalurar rashin miƙewar azzakari?

Dakta Marković Žigić ta ce wannan matsalar za a iya samunta ta hanyar wasu sauye-sauye a jiki ko na tunani.

Sauyi a jiki yakan samu ne sakamakon rashin wasu sinadarai, ko samun sauyi a jijiyoyin jini, ko sakamakon samun wata lalura a jiki kamar cutar ciwon Suga da cutar ƙwaƙwalwa.

"Azzakari kan miƙe ta hanyar amfani da wasu magunguna na ƙara kuzari," in ji ta.

Marković Žigić ta ce matsalar tunani da ke haifar da rashin miƙewar azzakari sun hadar da, fargaba, da rashin jin ƙwarin gwiwa ko samun asara a kasuwanci.

"Cutar damuwa ma na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da rashin sha'awa.''

Likitar ta ƙara da cewa kawar da cutar damuwa, zai taimaka wajen magance matsalar.

Miƙewar azzakari na faruwa ne a lokacin da namiji ya fara jin sha'awar saduwa.

Hanyoyin jijiyoyin azzakarin sukan buɗe, ta yadda za samu gudanar jini a cikinsu.

A yayin da ƙofofin suka buɗe, jiyoyin kan samu damar janyo jini ta yadda zai riƙa gunada a tsakanin jijiyoyin azzakarin.

Da haka ne zai miƙe tare ƙarfin sha'awar saduwa.

'Na ɗauka ni kaɗai ne ke da matsalar'

Da farko idan aka samu matsalar, mutane kan magance ta ta hanyar amfani da wasu magungunan da ba na asibiti ba, in ji Dakta Žigić.

Wannan ita ce hanyar da Tamara mai shekara 34 ta bi domin nemo wa mijinta maganin lalurar.

"Ba ma gamsar da juna a lokacin saduwa," in ji Tamara.

"A duk lokacin da na buƙace shi, sai ya nuna ba ya so, nan da nan sai in ga yanayinsa ya sauya."

A lokacin da ta fara fuskantar wannan matsala da mijinta ta ɗauka matsalar daga gareta ne.

"da na kuance shi sai ya juya min baya, ya ce shi a gajiye yake, nan da nan sai ya fara bacci, a da na ɗauka matasalar daga ni ce'', in ji Tamara.

Ita ce ke fara nuna sha'awarta na neman magani, da fari mijinta baya son yin magana game da batun, to amma daga baya ya fahimci matsala ce.

"Yana jin cewa yana zalunta ta, don haka yake fargabar cewa wataƙila zan guje shi'', in ji ta.

Daga nan suka yanke shawarar fara neman magani kan lalurar.

Maganin matsalar saduwa, abu ne ma'aurata da dama ke nema domin kauce wa matsalolin da suke fuskanta.

Cutar lanƙwashewar mazakuta

Cutar lanƙwashewa azzakari na haifar da wasu sauye-sauye a azzakari waɗanda ke haifar da ciwo a lokacin miƙewar azzakari.

Wadansu bincike sun nuna cewa an samu cutar ne daga wata matsala da aka samu sakamakon zubar jini a cikin azzakarin.

Da farko cutar kan fara kama jijiyoyin azzakarin, lamarin da zai sanya shi ya karkace, musamma lokacin da yake miƙewa.

Wannan cuta kan haifar da zafi, tare da cutar damuwa a zukatan masu ita.

Ƙananan sauye-sauye ba sa haifar da samun waɗannan alamomi, dan haka ba dole ne sai an nemi magani ba.

Kawo yanzu babu wani takamamman maganin wannan lalura.

A waɗansu lokutan akan yi wa mutane tiyata domin magance matsalar.

Amfani da magungunan ƙarfin maza

Akwai fitattun magunguna irin su 'Viagra' da ake amfani da su wajen magance matsalar rashin miƙewar azzakari.

"Idan matsalar daga sinadaran 'hormones' ne aka ƙara su da magunguna, idan kuma daga ciwon suga ne ana magance ta ta hanyar rage yawan sugan da ake sha'', in ji Dakta Marković Žigić.

Wani bincike da aka gudanar a shafin sayar da magunguna na Apoteka na Sabiya ya nuna cewa kashi 29 na maza na amfani da magunguna domin magance matsalar tashin azzakari.

"Wannan na nuna yadda matsalar ta yi ƙamari, da kuma yadda za mu magance ta," in ji Mirjana Spajić masanin harkokin magunguna.

Masu amfani da magungunan ƙara ƙarfin maza kan sayi magungunan a shafin intanet musamman saboda kunya.

Matsalar rashin miƙewar azzakari lalura ce da mutane ke kunyar bayyanata.

Dakta Marković Žigić ta ce maza da dama ba sa son yin magana game da lalurar, lamarin da ke ƙara ta'azzara magance ta.