Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Jamus ta kai zagaye na biyu

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Germany 2 , Ivory Coast 1 at Full time
Jamus
Cote d'Ivoire
Full time
Hutun rabin lokaci Jamus 0 , Cote d'Ivoire 1

Key Events

Jamus

  • D. UndavGoal 68 minutes, Goal 90 minutes plus 4

Cote d'Ivoire

  • F. KessieGoal 30 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Jamus,N. Amiri (68 minutes), F. Nmecha (90 minutes plus 4)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Za mu kawo muku wasan Sifaniya da Saudiya kai tsaye ranar Lahadi tun daga misalin karfe 4:00 na yammaci a take leda da karfe 5:00 na yammaci.

    Sunana Mohammed nake ce muku sai da safe

  2. Wasannin da za a buga

  3. Yadda aka gara wasan

  4. An tashi wasan

    Jamus ta kai zagaye na biyu a karon farko tun bayan 2014.

    Za ta buga wasan karshe da Equador.

  5. GOAL - Jamus 2-1 Ivory Coast, Undav

    Undav wanda aka saka shi daga baya ya kara na biyu, kuma kwallo mai kyau ya ci.

    Tun daga nesa aka buga masa kwallo ya taba sau daya ya juya ya buga ta shiga ragar Ivory Coast kuma a cikin karin lokaci.

  6. , Germany 1-1 Ivory Coast

    An yi karin minti shida.

    Gaskiya Ivory Coast tana kokari da taimakon mai tsaron ragarta Fofana da yanzu sakamakon ya sauya.

    Ya tare kwallo uku da ya kamata su fada raga.

    Ya kamata yan wasan Ivory Coast su kara nutsuwa, domin lokaci ya kure, duk wanda aka ci shike nan.

  7. , Germany 1-1 Ivory Coast

    Lokaci na kurewa wasan sai kara daukar zafi yake kuma kowacce tawaga na kai harin kara kwallo na biyu.

  8. , Jamus 1-1 Ivory Coast

    An maye gurbin Wilfried Singo da Guela Doué.

    Nan take ya zauna a kujera dama yana daf da wajen zaman benci, yana runtse idanu. Ya shiga damuwa matuka — kuma babu mamaki a hakan. Akwai yiwuwar gasar kofin duniyarsa ta kare a wajen shi zai sha jinya.

  9. , Jamus 1-1 Ivory Coast

    Watakila a sa Ivory Coast ta yi canjin dole, domin Wilfried Singo ya nuna alamun samun matsala a kafarsa, yayin da ya tokare Kai Havertz a gefen fili wajen jifa..

    Wannan babbar matsala ce ga tawagar Emerse Faé, domin ya yi dan wasan yana matuƙar taka rawar a daren yau.

  10. , Jamus 1-1 Ivory Coast

    ‘Yan wasan da suka shiga sauyi na Jamus sun riga sun bayar da gudummawar cin kwallaye biyar, ko dai su ci ko kuma su bayar a zura a raga a gasar kofin duniya ta 2026 — mafi yawa fiye da kowace ƙasa.

  11. Ivory Coast ta canja yan wasa uku, Jamus 1-1 Ivory Coast

    Tawagar Ivory Coast ta canja yan wasa uku inda Evann Guessand, Seko Fofana da Simon Adingra suka maye gurbin Ange-Yoan Bonny, Ibrahim Sangare da kuma Amad Diallo.

  12. , Germany 1-1 Ivory Coast

    Tuni an koma zagaye na biyu bayan hutun shan ruwa, kuma kasa da minti 14 a kammala wasan nan, shi ne na biyu a rukuni na uku.

    Kawo yanzu kowacce tana da maki hurhudu.

  13. An je hutun shan ruwa

  14. GOAL - Jamus 1-1 Ivory Coast, Undav

    Jamus ta farke kwallon.

    An bugo kwallo daga sama mai tsaron bayan Ivory Coast ya yi tsalle bai samu ba, nan da nan Undav ya sa kafa ta fada ragar Ivory Coast.

  15. Kdan ya rage Jamus ta farke kwallo.

    Kai Havertz ya kasa taba ƙwallon da Joshua Kimmich ya buga masa, inda mai tsaron raga Yahia Fofana ya je ya kama.

  16. , Germany 0-1 Ivory Coast

    Jamus ta kara samun kwana. Tuni ta samu da yawa a minti na 17 da komawa zagaye na biyu, fiye da yadda ta samu a zagayen farko.

  17. Jamus ta yi vanjin yan wasa uku, Germany 0-1 Ivory Coast

    Kociyan Jamus, Julian Nagelsmann ya canja Leroy Sane, Jamal Musiala da Aleksandar Pavlovic ya maye gurbinsu da Jamie Leweling, Deniz Undav da kuma Nadiem Amiri.

  18. , Germany 0-1 Ivory Coast

  19. , Germany 0-1 Ivory Coast

    Jamus ta buga kwana, amma cikin ruwan sanyi fofana ya kama, ya yi sauri ya jefa cikin fili, amma kwallon ya fita jifa na Jamus.

  20. , Jamus 0-1 Ivory Coast

    Lokaci ne na Yan Diomande, ya yi amfani da jan kwallo a kan layi ya kuma shiga gidan Jamus ya buga, amma Manuel Neuer ya kama.