Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasan da zai kafa gagarumin tarihi a Gasar Kofin Duniya
Hukumar wallon kafa ta duniya, Fifa mai tsara gasar cin kofin duniya, za ta gabatar da wani wasan da zai shiga kundin tarihinta.
Wannan wasan shi ne tsakanin Tunisia da Japan ranar Asabar da zai zama na 1,000 a babbar gasar tamaula ta duniya a ranar 20 ga watan Yunin 2026.
Za kuma su kece raini ne a wasan cikin rukuni na shida da za su fafata a katafaren filin wasa da ke Monterrey a Mexico.
A tarihin gasar cin kofin duniya ta FIFA, akwai wasu wasanni da ba a mantawa da su. Amma a gasar FIFA World Cup 2026, za a kafa wani babban tarihi mai matukar muhimmanci — wasa na 1,000 a tarihin gasar.
Yadda aka kai wannan matsayi a tarihin gasar
Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta fara ne a shekarar 1930 a Uruguay, inda aka buga wasanni kaɗan, idan aka kwatanta da wadda ake yi a bana.
A wancan lokaci, kasashe kalilan ne ke shiga gasar.
Amma a tsawon shekaru, sai gasar ta faɗaɗa daga ƴan kalilan tawaga zuwa 13 daga nan suka koma 32, sannan yanzu kasashe 48 ke kece raini a gasar 2026
Yawan wasanni ya ƙaru sosai, saboda karin kasashe da sabon tsarin wasannin cikin rukuni zuwa zagaye na biyu kai har ta kai ga wasan karshe.
Wannan ci gaba ne ya sa aka kai ga adadin wasanni da ya haura 999, sannan wasa na 1,000 zai zo a wannan gasar ta 2026 da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
A cewar rahotanni na FIFA, wannan wasa na tarihi zai gudana a Estadio BBVA, Monterrey, inda Tunisia da Japan za su kara domin rubuta suna a littafin tarihi.
Wasan yana da abubuwa da suka sa ya zama na musamman
1. Yawan wasan da ake buga wa
Ba kowace rana ba ce ake kaiwa wasa 1,000 a gasar duniya. Wannan yana nuna tsawon tarihin gasar da ci gaban da ta samu da kuma girmanta.
2. Kasashen daban-daban
Tunisia daga Afirka take, Japan kuma daga Asiya take wakilta. Wannan yana nuna yadda wasannin gasar cin kofin duniya ke haɗa tawaga daga nahiyoyin duniya, domin tantance gwana daga karshe.
3. Filin wasa na zamani
Wasan zai gudana a filin Monterrey a Mexico, daya daga cikin sabbin wuraren da ke karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2026 na gani na faɗa mai dauke kayayyakin zamanin.
Takaitaccen tarihin FIFA World Cup
An fara a 1930
Brazil ce kasa mafi yawan lashe kofin
Kasashe sama da 80 sun taɓa shiga gasar tun fara ta
Yanzu tana ɗaya daga cikin manyan wasannin da ake fi kallo a duniya
A tsawon wannan lokaci, an buga daruruwan wasanni masu tarihi — amma wasa na 1,000 zai zama wani sabon babi mai muhimmanci.
Yadda aka fara wasan farko zuwa na 1,000 da za a buga
A cewar FIFA, an riga an tantance wasu muhimman wasannin tarihi, yayin da za a buga fafatawa ta 1,000 a gasar kofin duniya. Ga bayanan da aka tattara:
Wasa na farko (1) France 4-1 Mexico da kuma Amurka 3-0 Belgium (an fara su lokaci guda a ranar 13 Yuli 1930)
Wasa na 500 Wasannin ƙarshe a rukuni na huɗu a gasar 1994, inda Najeriya da Bulgaria da Argentina suka kai zagaye na gaba. FIFA ta ayyana wannan rana a matsayin wasa na 500 a tarihin gasar.
Wasa na 900 Final ɗin gasar 2018 tsakanin France da Croatia (Faransa ta ci 4-2). FIFA ta bayyana wannan a matsayin wasa na 900 a tarihin gasar.
Wasa na 999 Netherlands da Sweden a rukuni na shida, kafin Tunisia da Japan.
Wasa na 1,000 Tunisia da Japan a Monterrey, Mexico, ranar 20 Yuni 2026.
Kovacs ne zai busa wasa na 1,000 a gasar kofin duniya
An naɗa alkalin wasa ɗan ƙasar Romania, István Kovács, domin busa wasa na 1,000 a tarihin gasar Kofin Duniya ta FIFA, wanda zai kasance karawar rukuni na shida tsakanin Tunisia da Japan a filin wasa na Monterrey ranar Asabar, 20 ga watan Yuni.
Kovács mai shekara 40 zai yi alkalancin karawar tare da taimakon takwarorinsa ƴan ƙasar Romania, Ferencz Tunyogi da Mihai Marica.
Haka kuma, Juan Calderon da Juan Carlos Mora daga Costa Rica za su kasance alkalin wasa na huɗu da kuma mai jiran ko ta kwana.
Wannan wasan yana daga cikin fitatciyar karawa da za ta shiga tarihi a wannan gasa mai ɗimbin tarihi da daraja.
A farkon wannan shekarar ranar 31 ga watan Mayu, Kovács ne ya yi alƙalancin wasan ƙarshe a UEFA Champions League tsakanin Paris Saint-Germain da Inter Milan a Munich.
Haka kuma, ya jagoranci wasan ƙarshe a Europa Conference League a shekarar 2022, sannan shi ne alkalin wasan ƙarshe a Europa League a 2024 tsakanin Atalanta da Bayer Leverkusen.
Naɗin Kovács domin wannan wasa mai tarihi ya nuna irin amincewar da FIFA ke da ita a kansa da ƙwarewarsa a manyan wasannin ƙwallon ƙafa na duniya.
Muhimmancin wannan wasa ga duniya
Wannan wasa ba kawai game da Tunisia ko Japan ba ne. Yana nuna:
Yadda kwallon kafa ke hada al'ummomi
Yadda gasar ta girma daga karama zuwa babba a duniya
Yadda ake ci gaba da kafa tarihi da yin abubuwan bajinta duk bayan shekara huɗu
Ga magoya bayan kwallon kafa, wannan wasa zai zama lokacin tunawa, wanda za a dade ana magana akai.
Yadda magoya baya ke kallon wasan:
Magoya baya a duniya suna ganin wannan wasa a matsayin na musamman
Damar ganin tarihin buga wasa na 1,000 a babar gasar tamaula ta duniya
Wani abin alfahari ga kasashen da ke taka leda a karawar
Me zai iya faruwa a wasan?
Duk da cewa wasa ne na tarihi, yana da muhimmanci a fagen gasar
Kowanne daga tawagar na bukatar maki a karawar rukunin
Japan da Netherlands sun tashi 2-2 a wasan farko a rukuni na shida,
Ita kuwa Tunisia ta sha kashi 5-1 a hannun Sweden a dai wasan farko a rukuni na shida
Tunisia za ta so ta taka rawar gani da take wakiltar Afirka
Japan kuma na da burin kaiwa mataki mai nisa a gasar cin kofin duniya ta 2026
Wasa tsakanin Tunisia da Japan a FIFA World Cup 2026 zai zama wani babban tarihi a kwallon kafa, saboda shi ne na 1,000 a tarihin gasar Kofin Duniya.
Daga 1930 zuwa 2026, FIFA World Cup ta yi tafiya mai nisa — kuma wannan wasa zai zama alamar sabon babi a tarihin kwallon kafa a duniya.