Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid na son Van Dijk, Bayern Munich na harin Kounde
Real Madird na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Liverpool Virgil van Dijk, a dai-dai lokacin da ɗan wasan ke dab da zama mai zaman kansa a ƙarshen kakar wasannin nan. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Bayern Munich na shirin miƙawa ɗan wasan gaban Faransa Michael Olise sabon kwantaragi zuwa 2032, yayin da kwantaraginsa ke dab da ƙarewa a 2029. (Bild - in German)
Sai dai duk da haka Munich ɗin na son ɗaukar mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford, 32. (TeamTalk)
Ɗan wasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, na cikin yan wasan da Manchester United ke son ɗauka don inganta gaban ƙungiyar. (TeamTalk)
Haka kuma Unitedɗin na shiri miƙa sabon kwantiragi ga ɗan wasan Ingila Luke Shaw, da kwantaraginsa za ta ƙare a ƙarshen kakar wasannin.(Football Insider)
Bayern Munich na sa ido kan dan wasa Jules Kounde, yayin da Barcelona ta fara nuna son sallamar ɗan wasan. (Sport - in Spanish)
Tottenham Hotspur ta nuna sha'awar ɗaukar dan wasan Koriya ta Kudu Kim Min-jae, daga Bayern Munich.(Sport - in Spanish)
Tsohon mai tsaron bayan Manchester United Matteo Darmian, ya shirya fara ƙarbar horo a Bologna a ranar Laraba bayan da Inter Milan ta saki ɗan wasan a kakar wasa. (Gianluca Di Marzio - in Italian)