Ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba - Atiku

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027, yana mai cewa har yanzu ‘yan Najeriya da dama na cikin ƙunci duk da ikirarin Shugaba Bola Tinubu cewa ƙasar ta shiga zamanin wadata.
Atiku ya bayyana hakan ne a jawabinsa na “Yanayin da ƙasa ke ciki" da ya gabatar ranar Alhamis domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Ya ce duk wani cigaban tattalin arziki ba shi da wani amfani idan iyalai ba za su iya biyan buƙatun rayuwa na yau da kullum ba.
Ya ce raguwar hauhawar farashi kaɗai ba za ta mayar wa ‘yan Najeriya ƙarfin sayen kayayyakin da suka rasa ba, musamman ganin yadda farashin muhimman kayayyaki da ayyuka ke ci gaba da tashi.
Domin nuna irin matsin tattalin arzikin da ma’aikata ke fuskanta, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kwatanta ƙarfin sayen albashin mafi ƙaranci kafin da bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da aka yi.
A cewarsa, albashin mafi ƙaranci na yanzu, wato naira 70,000, na iya sayen kusan lita 50 na man fetur ne kawai, yayin da tsohon albashin naira 30,000 zai iya sayen lita 118 a watan Afrilun 2023.
Ya kuma yi nuni da tashin farashin burodi da ƙwai, yana mai cewa tsadar kayan masarufi na yau da kullum na ci gaba da yi wa gidaje nauyi.
A wani ɓangare na shirinsa na rage farashin man fetur, Atiku ya gabatar da shawarar bayar da tallafin gwamnati ga man fetur da aka tace a Najeriya kaɗai, yayin da za a cire man da aka shigo da shi daga ƙasashen waje daga shirin.
Ɗan takarar na ADC ya kuma yi tambaya kan kuɗaɗen tallafin kai tsaye da gwamnati ta ce tana bai wa marasa galihu, inda ya nemi a bayyana yadda aka gano mutum miliyan 10 da aka ce an bai wa kowannensu naira 75,000.
“Idan har za ku iya gano mutum miliyan 10 da za ku biya kuɗi, to ya kamata ku iya yin bayanin yadda aka biya su.”
Har ila yau, ya yi kira da a wallafa bayanan lamuni da kwangilolin gwamnati, yayin da ya nuna damuwa kan yawaitar kasafin kuɗi iri ɗaya da kuma rashin biyan wasu ‘yan kwangila haƙƙoƙinsu.
Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati ta yadda ‘yan Najeriya za su iya biyan buƙatun rayuwarsu da kuma rayuwa cikin tsaro, ba wai kawai ta hanyar alkaluman tattalin arziki da gwamnati ke fitarwa ba.
Dangane da zaɓen shekarar 2027, ya yi alƙawarin mutunta ‘yancin kan hukumomin zaɓe tare da goyon bayan fitar da sakamakon zaɓe daga kowace rumfar kaɗa ƙuri’a cikin gaggawa.





















