Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
City na kan gaba a zawarcin Vinicius, Barcelona na da damar sayen Alvarez
Manchester City ce a gaba wajen neman daukan dan gaban Real Madrid da Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, wanda shekara daya da dan lokaci suka rage masa a kwantiraginsa a Bernebau. (Teamtalk)
Bayern Munich ta tuntubi Newcastle United a kan dan gabanta na gefe kuma dan Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, sai dai akai tazarar fam miliyan 20 a kan yadda Newcastle ta yi masa kudi da kuma yadda Munich ta taya shi. (Mail)
Dan gaban Paris St-Germain Bradley Barcola zai iya barin kungiyar a bazara, kuma tuni Arsenal, da kuma Barcelona suka nuna sha'awarsu a kan dan Faransan mai shekara 23. (Sky Sports)
Kociyan Tottenham Roberto de Zerbi yana son amfani da damar da kungiyar take da ta saye dan wasan tsakiya Joao Palhinha na Portugal mai shekara 30 a kan fam miliyan 27, wanda kungiyar ta karba aro daga Bayern Munich. (Mail)
Barcelona na da dama har ta iya yuro miliyan 100 ta sayi dan wasan Argentina mai kai hari Julian Alvarez daga Atletico Madrid to amma kungiyar ta tsaya ta ga ko dan wasan mai shekara 26 zai nemi barin kungiyar kafin su yi zawarcinsa. (Mundo Deportivo)
Dan wasa mai kai hari na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 26, zai kasance ba shi da sauran kwantiragi a bazaran nan da Juventus, kuma yana jiran Barcelona ko Bayern Munich su dauke shi. (Sportmediaset, daga Football Italia)
Manchester City na tattaunawa da dan bayanta na Crotia Josko Gvardiol mai shekara 24 a kan tsawaita kwantiraginsa da kungiyar. (Sky Sports)
Brighton, da Leeds United da kuma West Ham ka iya shan kan Brentford a kokarin da take yi na sayen matashin dana bayan RB Salzburg, Jannik Schuster, dan Austria mai shekara. (Teamtalk)
Dole sai Everton ta dage a zawarcin da take yi na sayen dan bayan Burnley Maxime Esteve saboda Bayer Leverkusen na sha'awar dan Faransan mai shekara 23. (Football Insider)
Eintracht Frankfurt na tunanin rabuwa da kociyanta Albert Riera, tsohon dan wasan gaba na gefe na Liverpool da Sifaniya da ta dauka a watan Janairu. (Sky Sports)