Ba ƙoƙarin maye gurbin Ronaldo da Messi nake yi ba - Mbappe

Lokacin karatu: Minti 1

Tauraron ɗanwasan gaba na Real Madrid Kylian Mbappe ya ce "zarta Cristiano Ronaldo da Messi ba shi ne a gabansa ba".

Kyaftin ɗin na Faransa na tare da tawagar ƙasarsa yanzu haka domin buga gasar Uefa Nations League, inda za su kara da Croatia gida da waje.

Yayin taron manema labarai a ranar Laraba kafin wasan na ranar Alhamis, Mbappe ya jaddada cewa ba zai yiwu a shafe tarihin Messi da Ronaldo a ƙwallon ƙafa ba.

"Messi da Cristiano Ronaldo ba zai yiwu wani ya maye gurbinsu ba, saboda haka ba ƙoƙari nake na ga na shafe su ba," in ji ɗanƙwallon mai shekara 26.

"Amma game da Ballon d'Or, zan je wajen Luka Modric ya faɗa min yadda zan yi na lashe kyautar, zai iya faɗa min."

A farkon kakar wasa ta bana Mbappe ya koma Real Madrid a kyauta bayan kwantaraginsa ya ƙare a Paris Saint-Germain, inda zuwa yanzu ya zira ƙwallo 20 a gasar La Liga.

Cristiano Ronaldo ɗan ƙasar Portugal ya ci wa Real Madrid ƙwallo 450 a dukkan gasanni tun daga 2009 zuwa 2018, kuma zuwa yanzu ya ci 928 jimilla a sana'arsa ta ƙwallon ƙafa da kuma manyan kofuna 35.

Mbappe ya sha bayyana cewa Ronaldo ne abin koyinsa a harkar ƙwallon ƙafa.

A gefe guda kuma, Lionel Messi na Argentina ya ci ƙwallo 854 jimilla da kuma manyan kofuna 46.