Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Za mu kawo muku wasan Bayern Munich da PSG kai tsaye anjima

  2. Wannan shi ne karo na biyu da Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

    Za ta zira wadda za ta fuskanta tsakanin Bayern Munich da Paris St Geramin.

    Ranar Laraba Bayern Munich za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu na daf da karshe a gasar ta zakarun Turai.

    A wasan farko a makon jiya PSG ce ta yi nasara da cin 5-4.

    Shin wa zai hadu da Arsenal a wasan karshe a Budapest a Champions League?

  3. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Babbar murna daga ‘yan wasan Arsenal da ma’aikatan ƙungiyar.

    Sun kai wasan ƙarshe a Champions League karo na farko tun 2006, kuma karo na biyu kacal a tarihin su.

    Wasan ya bugu kuma kowa ya samu dama, Arsenal ce da nasara.

  4. An tashi wasan, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    ARSENAL TA KAI WASAN KARSHE A CHAMPIONS LEAGUE'

  5. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Arsenal na ƙara kusantar zuwa wasan karshe sosai.

    Yanzu kuma Mikel Arteta ya samu katin gargadi.

  6. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Arsenal na ta kokari a waɗannan mintuna na ƙarshe sosai da kyau.

    Amma Atlético ba ta matsa musu da yawa ba.

  7. Karin lokaci, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An yi karin minti biyar, lokacin da ya rage Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

  8. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Alex Baena ya yi wani yunƙurin buga kwallo da ƙarfi, wanda ya sa magoya bayan Arsenal suka yi ta kuwa, amma ƙwallon ta wuce sama da raga.

    Minti ɗaya kawai ya rage tare da ƙarin lokaci a tashi daga wasan nan kowa ya kama gabansa.

  9. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Kash! Abin tausayi sai kuka ake ana ta zubar da hawaye a ɓangaren magoya bayan Atlético Madrid. Ba su da lokaci mai yawa don su farke ƙwallon, kuma gaskiya a wannan lokaci ba ya nuna kamar za su iya dawowa cikin wasannan.

  10. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Gabriel Martinelli ya shiga fili ya kuma canji Leandro Trossard - kuma lokaci yana ta kurewa.

  11. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An bugo ƙwallo mai kyau daga Marcos Llorente zuwa cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma David Raya ya karkatar da ita, kuma babu wanda ya jo daga baki ko zai yi wani abun..

    Lokaci yana ƙurewa Atlético.

  12. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Ko yaya kociyan Atletico ke ji kuwa?

  13. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Maritn Zubimendi ya maye gurbin Myles Lewis-Skelly. Saura minti 15 Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

  14. Me Arteta ke cewa ga Arsenal, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

  15. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Lallai Viktor Gyökeres ya kamata ya tabbatar da tikitin Arsenal zuwa wasan ƙarshe a nan!

    An kai wata ƙwallo da sauri mai kyau cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai ya buga ta kai tsaye ta kuma yi kyau, amma ta wuce saman raga. Wata dama ce mai kyau, amma dai ana sa ran ƙwallon za ta shiga raga, amma hakn bai samu ba.

  16. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Atlético ta samu bugun kai tsaye, amma kwallon da Antoine Griezmann ya kawo an fitar da ita kai tsaye daga ɗan wasan Arsenal.

    Julian Alvarez ya yi ƙoƙarin ɗaga ƙwallo sama, amma ta yi kusa sosai da David Raya, wanda ya kama ta cikin sauƙi.

  17. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Na manta na sanar da ku Arsenal ta yi canji

    Riccardo Calafiori da Eberechi Eze da kuma Bukayo Saka, an maye gurbinsu da Noni Madueke da Martin Odegaard da kuma Piero Hincapie - to anya canjin nan ya yi kyau kuwa.

    Suma baki sun yi canji inda, Ademola Lookman da Giuliano Simeone da kuma Robin Le Normand, inda Johnny Cardoso da Alexander Sorloth da kuma Nahuel Molina suka shiga fili.

  18. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Akwai wasu hukunci guda biyu da ka iya jawo cece-kuce a nan.

    Ƙalubalen Gabriel a kan Antoine Griezmann da kuma na Riccardo Calafiori, shima a kan Griezmann.

  19. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Gudu mai kyau daga Declan Rice nan da nan ya bai wa Viktor Gyokeres kwallo daga bangaren hagu, amma kuma Marcos Llorente ya hana shi yin wani abu.

    .

  20. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Wannan shi ne lokaci mai kyau daga Atletico Madrid. Sun fito gabaki ɗaya ko za su farke ƙwallon sun fara fahimtar lokaci ya fara ja.