Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 22/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Mutum 11 sun ji rauni bayan buɗe wuta a Turkiyya

    Aƙalla mutum 11 sun ji rauni sakamakon buɗe wuta da wani mahari ya yi a wajen wata makarantar sakandare da ke Turkiyya.

    Daga bisani kuma ɗan bindigar ya tsere. Lamarin ai ya faru ne a makarantar da ke Lardin Manisa a yammacin ƙasar.

    Tuni dai aka kama ɗan bindigar, kamar yadda ofishin gwamnan yankin ya sanar.

    Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa biyu daga cikin mutanen da aka kai asibiti suna cikin mawuyacin hali.

    Bidiyon da aka wallafa a intanet ya nuna wani mutum a kusa da makarantar ɗauke da bindiga, sai kuma bidiyon ya nuna shi yana tserewa amma da makamin a hannunsa.

    Zuwa yanzu ba a san dalilinsa na kai harin ba.

    Bayanai daga kakafen yaɗa labaran Turkiyya na cewa maharin ɗalibi ne ɗan shekara 15 sai dai hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ilimi ta Turkiyya ta ce lamarin ya jefa ƙasar, musamman ɓangaren ilimi cikin yanayi na alhini.

    Ma'aikatar ta kuma ce ta tura jami'ai zuwa Manisa domin gudanar da bincike.

  2. Iran ta yi tayin buɗe Mashigar Hormuz

    Kamfanin dillancin labarai na Japan, Kyodo ya ruwaito wani babban jami’i a Iran da ba a bayyana sunansa ba yana cewa ƙasar tana tayin buɗe Mashigar Hormuz nan da mako ɗaya don a sassauta mata takunkumin da aka ƙaƙaba mata.

    Matakin wani ɓangare ne na yunƙurin da Tehran ke yi na komawa kan teburin tattaunawa da Amurka don kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, kamar yadda dillancin labaran ya bayyana.

    Kyodo ya ruwaito jami’in na cewa Majalisar tsaron ƙasar da Jagoran addini Mojtaba Khamenei sun amince da shawarar.

    A cewar rahoton, tuni masu shiga Tsakani suka gabatar da shawarar ga Amurka.

    Jami’in ya ce Iran na son ganin alamu da za su tabbatar da cewa Amurka a shirye take ta koma teburin sulhu, a dakatar da ayyukan soji a Mashigar Hormuz tare kuma da ƙarshen ci gaba da rufe tashoshin jiragen Ruwan Iran.

  3. Mutum biyar sun mutu sakamakon ƙaƙƙarfar guguwa a Japan

    Aƙalla mutum biyar sun mutu, wasu da dama kuma sun ɓace sakamakon wata ƙaƙƙarfar guguwa da ta afkawa gaɓar tekun gabashin Japan.

    Guguwar ta kuma haddasa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka jima ba a samu irinsa ba a yankunan da ke kewaye da babban birnin ƙasar, Tokyo, tare da jefa dubban gidaje cikin duhu bayan da wutar lantarki ta ɗauke.

    Jami'an hukumar kula da yanayi a ƙasar sun buƙaci jama'a su ci gaba da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan.

    Tun kafin guguwar ta fice daga ƙasar, ta tilasta rufe ɗaya daga cikin manyan bukukuwan baje kolin wasannin bidiyo mafi girma a duniya da ake gudanarwa a Tokyo.

    Haka kuma, an soke tashi da saukar ɗaruruwan jiragen sama, yayin da aka dakatar da wasu ayyukan sufurin jiragen ƙasa saboda mummunan yanayin da guguwar ta haifar.

  4. Ya kamata Isra'ila ta sassauta matakan shigar da kayan agaji Gaza - MDD

    Shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa, ya yi kira ga Isra’ila da ta sassauta matakan da take ɗauka wajen ba da damar shigar da kayayyaki da kayan aiki zuwa Gaza.

    Christian Saunders ya shaida wa BBC cewa kusan dukkan mutanen da ke yankin na zaune ne a cikin tantuna, ko ƙarƙashin buhun roba ko kuma a cikin gine-ginen da aka ruguza wani ɓangare.

    Shugaban hukumar ya ce matuƙar ba a samu ci gaba wajen sake gina yankin ba, to akwai yiwuwar mawuyacin yanayi da rashin tsafta su zame wa mutanen yankin jiki.

    Mista Saunders ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar kayayyaki irin su sandunan kafa tanti da man injina, amma Isra’ila ta hana shigar da su.

    A baya dai Isra’ila ta ce takunkumin da take sanya wa wasu kayayyaki ko kuma binciken da take yi a kan su na nufin hana ƙungiyar Hamas amfani da su.

  5. White House ta buɗe gidan talabijin na Trump TV

    Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ƙaddamar da tashar talbijin ta yanar gizo mai suna Trump TV.

    Matakin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan manyan gidajen talabijin na Amurka sun dakatar da rahotannin da suke ɗauka daga fadar ta White House, domin nuna rashin amincewarsu da matakin da Shugaba Trump ya ɗauka na haramta wa tashoshin CNN, MS Now da kuma Politico shiga fadar.

    Trump ya zargi kafafen yaɗa labaran da wallafa labaran ƙarya.

    Shafin intanet na White House ya bayyana Trump TV a matsayin tashar da ta fi dacewa domin samun muhimman bayanai.

    A cikin wata sanarwa da gwamnatin Trump ta fitar, ta ce samun damar shiga White House alfarma ce, ba wai haƙƙi ba ne.

    Sanarwar ta kuma ce babu wani shugaban ƙasa da doka ta tilasta masa karɓar abin da ta bayyana a matsayin wata kafar yaɗa labarai mai adawa da gwamnatinsa.

  6. Shugaba Tinubu ya tsawaita hutunsa

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tsawaita hutunsa da ƴan kwanaki kuma zai koma ƙasar a ƙarshen mako.

    Shugaba Tinubu dai ya bar Najeriya ne a ranar 30 ga Agusta inda ya tafi birnin London domin fara hutunsa.

    Bayan shafe mako ɗaya a London kuma, sai Tinubu ya je birnin Paris a Faransa inda ya gana da takwaransa Emmanuel Macron da ɗan kasuwa Mr Vincent Bollore.

    Shugaba Tinubu dai ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki daga inda yake a yayin hutun nasa.

    A cewar sanarwar da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar, tun bayan soma hutun nasa, Shugaba Tinubu ya ci gaba da tuntuɓar gida inda kuma yake tafiyar da harkokin ƙasar ciki har da bayar da umarnin kafa kwamitin bincike kan mutuwar matasa 37 da ake zargin masu haƙar ma'adanai ne ba bisa ƙa'ida ba a Minna, babban birnin jihar Neja.

    Sannan sanarwar ta ƙara da cewa a yayin hutun, Tinubu ya wakilta mataimakinsa Kashim Shettima don halartar wasu taruka a ƙasar.

    Sanarwar ta ce duk da cewa Shettima ya tafi Amurka don halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka, Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume,wanda yake wakiltar shugaban a taruka, zai ci gaba da yin hakan.

  7. G7 ta buƙaci Houthi ta dakatar da hare-hare kan Yemen da Saudiyya

    Kungiyar ƙasashen nan bakwai da ke da ƙarfin tattalin arziki a duniya wato G7, ta yi kira ga mayaƙan Houthi da ke samun goyon bayan Iran da su gaggauta dakatar da hare-haren da suke kai wa Yemen da kuma Saudiyya.

    Ministocin harkokin wajen Amurka da Birtaniya tare da na sauran ƙasashen biyar, sun kuma buƙaci a kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa na farar hula a Tekun Bahar Maliya, waɗanda suke haifar da cikas ga harkokin kasuwanci a duniya.

    Sanarwar haɗin gwiwar ta zo ne bayan da Birtaniya ta ce za ta bai wa Saudiyya taimakon soji a yaƙin da take yi da mayaƙan Houthi.

    Wakilin BBC ya ce jami’an gwamnati sun ce wannan tayin na da iyakacin lokaci, kuma a matakin farko ana sa ran zai ci gaba ne na tsawon wasu makwanni.

    A kwanakin baya bayan nan, mayaƙan Houthi sun kai hare-hare kan babban birnin Saudiyya, Riyadh, da kuma wasu wuraren samar da makamashi da ke gaɓar Tekun Bahar Maliya a ƙasar.

  8. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa Najeriya da ma sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma yin muhawara.

    Ku kasance tare da mu.