Shin mutum zai iya gane naman mushen dabba?

Nama

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A wani mataki da rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana a matsayin irin shi na farko a Jihar Borno, jami'an tsaro sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da safara da kuma sayar da naman shanun da suka mutu ga jama'a, inda su kuma suke sayarwa ga mutane.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴansandan Jihar Borno, DSP Nahum Kenneth Daso ne ya bayyana haka, inda ya ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da jami'an tsaro suka samu.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun ɗauki naman shanun da suka mutu daga kasuwar shanu ta Maiduguri ne suka sayar wa masu suya da sauran masu sana'ar nama. Haka kuma, ana zargin suna kai wani ɓangare na naman har zuwa Jihar Benue domin sayarwa.

"Mun samu rahoto daga masu tattara bayanan sirri cewa akwai masu safarar naman shanun da suka mutu. Bayan mun bi sawunsu, muka kama matasa biyar suna kan hanyar sayar da wani shanu mushe ga masu suya. Yanzu suna hannunmu, kuma muna ci gaba da bincike. Da zarar an kammala, za mu gurfanar da su a gaban kotu," in ji shi.

A cewar DSP Daso, binciken ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da waɗanda ake zargin suka aikata hakan ba.

"Sun amsa cewa sun daɗe suna wannan harkar. Jagoransu ya bayyana cewa suna sayar da naman shanun da suka mutu. Haka kuma ya ce akwai wata mata da suke bai wanama tana kai wa har jihar Benue domin ta sayar."

Rundunar ta ce wannan shi ne karo na farko da ta gano tare da kama masu hannu a irin wannan laifi a jihar.

A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga jama'a da su kasance masu lura da inda suke sayen nama, su guji sayen naman da ake sayarwa a wuraren da ba su dace ba, tare da tabbatar da cewa suna sayen nama daga wuraren da hukumomi suka amince da su domin kare lafiyarsu.

'Duk mahaucin da ya sayar da mushe da gangan ya yi'

Mahauta

Asalin hoton, Aminu Lawan Baƙin Ruwa

Bayanan hoto, Aminu Lawan Baƙin Ruwa tare da abokan sana'arsa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan kama wasu mutane a Jihar Borno bisa zargin sayar da naman shanun da suka mutu ga jama'a, Shugaban Mahauta na Abuja, Aminu Lawan Baƙin Ruwa, ya ce a Babban Birnin Tarayya ba a fuskantar irin wannan matsala saboda matakan sa ido da aka kafa a kasuwannin nama.

A cewarsa, ƙungiyar mahauta ta Abuja tana da kwamitin sa ido na musamman da ke aiki tare da likitocin dabbobi domin tabbatar da cewa naman da ake sayar wa jama'a ya cika ƙa'idojin lafiya.

"Maganar naman mushe, gaskiya mu a Abuja ba mu da wannan matsalar. Muna da kwamitin kar-ta-kwana da ke sa ido, sannan muna da tsarin yanka da likitocin dabbobi ke dubawa," in ji shi.

Ya ce ko dabba tana da rai, idan ba ta da lafiya ba za a yarda a yanka ta ba. Bayan an yanka ma, sai an sake duba naman kafin a ba jama'a.

Ya bayyana cewa babban burinsu shi ne kare lafiyar al'umma ta hanyar tabbatar da cewa naman da ake ci ba shi da wata barazana ga lafiya.

Aminu Lawan ya ce a baya sun taɓa fuskantar matsalar sayar da naman jaki, amma haɗin gwiwar shugabannin mahauta da hukumomi ya taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.

Da yake bayani kan yadda ake iya gano naman dabbar da ta mutu kafin a yanka ta, ya ce gogaggen mahauci ba zai yi wahalar gane bambancin ba.

"Dabbar da aka yanka yadda ya kamata, jininta yana fita sosai, naman kuma zai kasance sabo, mai haske kuma a tsaye," in ji shi.

Aminu ya ce za a iya gane danan dabbar da ta mutu ta hanyar da abubuwa kamar haka:

  • Naman zai yi duhu
  • Naman zai yi yaushi (zai riƙa bajewa)
  • Ƙuda ya fi taruwa a kan shi

Mahaucin ya ƙara da cewa da zarar an buɗe ta, gogaggen mahauci da ya gani zai gane cewa dabbar ta mutu.

Ya kuma ƙara da cewa ƙudaje kan fi taruwa a kan naman dabbar da ta mutu kafin a yanka fiye da wanda aka yanka bisa ƙa'ida.

Shugaban mahautan ya yi bayani game da abin da ake kira "fiɗa", wato dabbar da ta kasa aka yanka cikin gaggawa. A cewarsa, a wasu lokuta ana iya kawo irin wannan dabba kasuwa, amma a Abuja ba a yarda a yanka ta kai tsaye ba.

"Muna da kwamitin da ke tabbatar da cewa duk dabbar fiɗa sai likitocin dabbobi sun bincike ta sosai kafin a ba da izinin amfani da ita. Sai an tabbatar ba mutuwa ta yi ba kuma babu wata matsalar lafiya."

Ya jaddada cewa duk mahaucin da ya sayar da naman mushe da gangan ya aikata hakan, kuma ya kamata doka ta yi aiki a kansa.

A ƙarshe, ya shawarci masu sayen nama da su guji sayen naman da ake sayarwa a bakin titi ko gefen hanya.

"Ina ba da shawara ga jama'a su riƙa sayen nama a kasuwannin da aka amince da su, saboda akwai shugabanni da jami'an sa ido da ke kula da ingancin naman da ake sayarwa."

'Daga farashi ya kamata a fara tunanin matsala'

Wani ƙwararren likitan dabbobi, Dr. Abdulfattar Ɗayyib Umar, ya yi kira ga jama'a da su kasance masu lura da farashin nama da kuma wuraren da suke saya, yana mai cewa nama da ake sayarwa da farashi mai rahusa fiye da yadda aka saba na iya zama abin da ya kamata a yi shakku a kansa.

A cewarsa, a hukumance ana da tsarin bin diddigin kowace dabbar da ake yankawa ta hanyar amfani da rasiti da ke nuna asalinta da kuma yadda aka sarrafa ta.

"Ka ga ni ina aiki a kwata, kuma muna amfani da rasiti na kowace dabba. Haka kuma ya kamata a riƙa sa ido kan farashin nama. Idan dabbar da darajarta ta kai kusan naira miliyan ɗaya, amma aka ga ana sayarwa a misali naira dubu 200, wannan ya kamata mutum ya dasa alamar tambaya."

Ya ce hukumomi suna aiki tare da sarakunan fawa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da cewa naman da ya isa kasuwa ya dace da ƙa'idojin lafiya.

Dr. Abdulfattar ya bayyana cewa idan aka samu hatsarin mota da ya rutsa da dabbobi, wasu kan yi gaggawar kwashe dabbobin da suka mutu kafin jami'an da abin ya shafa su isa wurin.

"Muna haɗa hannu da Sarkin Fawa da kuma jami'an tsaro. Idan aka samu hatsari dabbobi suka mutu, muna zuwa ne mu kwashe su zuwa kwata domin ƙonawa. Sai dai a wasu lokutan, kafin mu isa wurin, wasu sun riga sun kwashe su saboda akwai masu neman irin wannan nama."

Ya ƙara da cewa naman dabbar da ta mutu kafin a yanka ta yana da wasu alamomi da ƙwararru kan iya ganewa.

"Naman dabbar da ba a yanka ba yakan kasance da jini sosai a cikinsa. Idan ya fara lalacewa, launinsa kan fara komawa kore. Amma gaskiya, gano irin wannan nama ba abu ne mai sauƙi ba. Yawanci sai ƙwararre ne zai iya tabbatar da hakan."

Saboda haka, ya ce hanya mafi sauƙi ga talakawa ita ce su kula da inda suke sayen nama da kuma farashinsa.

A ƙarshe, Dr. Abdulfattar ya yi kira ga masu hulɗa da harkar nama da su ji tsoron Allah tare da fifita lafiyar al'umma fiye da neman riba.

"Ya kamata kowa ya ji tsoron Allah. Lafiyar jama'a ta fi kowace irin riba muhimmanci."