Ko Mbappe zai iya lashe Ballon d'Or ba tare da kofi ba?

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Kylian Mbappé yana cikin ƴan wasa 30 da aka zaɓa domin takarar Ballon d'Or ta 2026, amma tambayar da ke tasowa ita ce: Shin ɗan wasan Real Madrid zai iya lashe babbar kyautar ɗan ƙwallo mafi fice a duniya a bana duk da cewa bai ɗauki babban kofi ba a kakar 2025/26?

Dokokin Ballon d'Or ba su ce dole sai ɗan wasa ya lashe kofi ba a kakar kafin ya samu damar lashe kyautar. A tsarin 2026, an bayyana ma'auni uku da da za a yi amfani da su wajen tantance ɗan wasa da zai zama gwarzon bana

Waɗanne abubuwa ake dubawa?

France Football mai gudanar da bikin ta bayyana cewa ana duba abubuwa uku, cikin waɗan nan tsari don zaƙulo zakara:

1. Ƙwazon ɗan wasa da tasirinsa a fili

Wannan shi ne ma'aunin farko. Ana duba yadda ɗan wasa ya taka leda da tasirinsa a wasanni da ya buga a kakar da cin ƙwallaye da kuma yadda ya kasance mai muhimmanci ga ƙungiyarsa da kuma ƙasarsa.

2. Gudunmuwa a ƙungiya da kofunan da aka lashe da shi

Wannan shi ne ma'auni na biyu. Don haka lashe kofuna yana da muhimmanci, amma ba shi ne sharadin farko ko tilasta lashe Ballon d'Or ba.

3. Halayya ɗa'a ko wasa bada gaba ba wato Fair Play

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kuma la'akari da halayyar ɗan wasa da kuma yadda yake mutunta dokokin wasa da abokan hamayya.

Saboda haka, rashin ɗaukar kofi ba yana nufin an cire ɗan wasa daga takara ko rashin damar lashe Ballon d'Or ba.

Yaya ake zaɓen wanda zai lashe?

Akwai 'yan wasa 30 a jerin waɗanda aka zaɓa.

Daga nan, ba magoya baya ko ƴan wasa ne za su sake kada wata kuri'a ba.

A maimakon haka, akwai ƴan jarida 100, inda kowace ƙasa daga cikin ƙasashe 100 da ke kan gaba a jadawalin FIFA za ta samu wakilci guda.

Kowane ɗan jarida zai zaɓi ƴan wasa 10 daga cikin 30, sannan ya jera su daga na farko zuwa na goma.

Tsarin maki kuwa shi ne:

Na 1 – maki 15

Na 2 – maki 12

Na 3 – maki 10

Na 4 – maki 8

Na 5 – maki 7

Na 6 – maki 5

Na 7 – maki 4

Na 8 – maki 3

Na 9 – maki 2

Na 10 – maki 1

Daga nan sai a tara dukkan maki. Wanda ya fi kowa samun maki shi ne zai lashe Ballon d'Or.

Idan aka samu kunnen doki, ana fara duban wanda ya fi samun kuri'ar matsayi na farko, sannan na biyu da na uku da sauransu.

Su waye ƴan takarar Ballon d'Or na 2026?

Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Ga jerin ƴan wasa 30 da aka zaɓa:

  • Jude Bellingham – Real Madrid
  • Pau Cubarsí – Barcelona
  • Marc Cucurella – Chelsea/Real Madrid
  • Ousmane Dembélé – Paris Saint-Germain
  • Luis Díaz – Bayern Munich
  • Bruno Fernandes – Manchester United
  • Gabriel – Arsenal
  • Erling Haaland – Manchester City
  • Achraf Hakimi – Paris Saint-Germain
  • Harry Kane – Bayern Munich
  • Khvicha Kvaratskhelia – Paris Saint-Germain
  • Lamine Yamal – Barcelona
  • Sadio Mané – Al-Nassr
  • Marquinhos – Paris Saint-Germain
  • Lautaro Martínez – Inter
  • Kylian Mbappé – Real Madrid
  • Nuno Mendes – Paris Saint-Germain
  • Lionel Messi – Inter Miami
  • João Neves – Paris Saint-Germain
  • Michael Olise – Bayern Munich
  • Willian Pacho – Paris Saint-Germain
  • Julián Quiñones – Al-Qadsiah
  • Declan Rice – Arsenal
  • Rodri – Manchester City/Barcelona
  • Fabián Ruiz – Paris Saint-Germain
  • William Saliba – Arsenal
  • Ferran Torres – Barcelona/Paris Saint-Germain
  • Dayot Upamecano – Paris Saint-Germain
  • Vinícius Júnior – Real Madrid
  • Vitinha – Paris Saint-Germain.

Wannan shi ne jerin ƙarshe na ƴan wasa 30, yanzu zaɓen da ƴan jarida za su gabatar ne zai tantance wanda zai zo na farko, ya zama gwarzin bana.

Me ya sa Mbappe ya ke da damar lashe ƙyautar Ballon d'Or?

Mbappe yana cikin jerin yan takara ne, bayan kakar da ya ci kwallaye masu yawa tare da Real Madrid, sannan ya kasance ɗaya daga cikin manyan sunayen da ake tattaunawa a kai da yake da damar lashe ƙyautar Ballon d'Or ta bana.

Amma matsalar da ke gabansa ita ce Real Madrid ta kammala kakar ba tare da lashe kofi ba.

Wannan na iya zama wani abu da masu jefa kuri'a za su duba saboda kofunan ƙungiya suna cikin ma'aunin zama zakaran Ballon d'Or.

Sai dai dokar ƙyautar ta sanya tasirin ɗan wasa a ƙungiya a matsayi na farko, kafin nasarorin ƙungiya. Don haka Mbappé bai rasa damar lashe kyautar ba, saboda rashin kofi kai tsaye.

An taba lashe Ballon d'Or ba tare da ɗan wasa ya ci kofi ba?

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

A tarihin Ballon d'Or, akwai ƴan wasa da suka lashe kyautar duk da cewa ba su ɗauki kofi a ƙungiya su ba a shekarar da suka gwarzon ƙyautar.

Waɗanda aka tabbatar sun yi hakan su ne:

1956 – Stanley Matthews

Shi ne ɗan wasan farko da ya lashe Ballon d'Or. Ya ci ƙyautar duk da rashin lashe kofi a ƙungiya a wannan shekarar.

1964 – Denis Law

Ɗan wasan Manchester United ya lashe kyautar ba tare da lashe babban kofin ƙungiya ba a lokacin.

1970 – Gerd Müller

Fitaccen ɗan wasan Bayern Munich da Jamus ya lashe kyautar bayan ƙwazon da ya nuna da tasirin da ya yi a ƙungiyar da shi kansa.

1978 – Kevin Keegan

Keegan ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka lashe kyautar ba tare da samun ɗaukar babban kofi a ƙungiya ba.

2000 – Luís Figo

Figo ya zama gwarzon Ballon d'Or bayan rawar da ya taka a kakar, duk da rashin lashe babban kofi a ƙungiya a wancan lokacin.

2013 – Cristiano Ronaldo

Ronaldo shi ne na baya-bayan nan da ya lashe Ballon d'Or ba tare da cin kofi a ƙungiya ba a wannan tsarin.

Wannan yana nuna cewa lashe kofi ba sharadi ba ne na farko, kafin ɗan ƙwallo ya zama gwarzon Ballon d'Or.

A waccan shekarar, Ronaldo ya yi fice sosai a matakin kokrin da ya yi na kashin kansa, kuma ƙididdigar kokarinsa da ƙwallayen da ya ci, sune suka taimaka masa wajen samun kuri'u masu yawa.

Daga ƙarshe ya lashe kyautar, duk da cewa bai ɗauki babban kofin ƙungiya ba.

Ba za a ce kofi shi ne hujjar lashe Ballon d'Or ba

A gaskiya, dokokin Ballon d'Or sun sanya nasarorin ƙungiya da kofuna a matsayin ma'auni na biyu don zama zakara.

Wannan yana nufin ɗan wasa zai iya samun ƙididdiga masu ƙarfi a matakin kokari na kashin kai, amma wanda ya taimaka wa ƙungiyarsa wajen lashe manyan kofuna na iya samun ƙarin hujja a fiye da shi a wajen masu kaɗa kuri'a.

Saboda haka, Mbappé yana buƙatar dogaro da abubuwan da ya yi a filin wasa domin ya gamsar da masu zaɓen.

Ba Mbappé bane kaɗai dake takara ba

A cikin jerin akwai Harry Kane, wanda ya yi fice wajen cin kwallaye a bana da Lamine Yamal, wanda ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa a Barcelona da Sifaniya da Ousmane Dembélé, wanda shi ne wanda ya lashe Ballon d'Or na 2025 da Rodri da Vinícius Júnior da Jude Bellingham da Erling Haaland da kuma Lionel Messi.

Haka kuma akwai ƴan wasa kamar Declan Rice, Vitinha, Achraf Hakimi, Nuno Mendes, Michael Olise da Luis Díaz, wadanda ke cikin jerin 30 kuma za su iya samun kuri'u daga masu zaɓe.

Ba a bayyana wani matsayi na ƙarshe ba kafin a kammala kada kuri'a, saboda tsarin Ballon d'Or yana dogara ne kan jimillar maki daga masu jefa kuri'ar.

Yaushe za a bayyana wanda ya lashe ƙyautar bana?

Za a gudanar da bikin Ballon d'Or na 2026 a London ranar 26 ga watan Oktoba, kuma wannan zai kasance bikin cika shekaru 70 da fara kaddamar da kyautar.

Idan muka karkare:

Tambayar ko Mbappé zai iya lashe Ballon d'Or ba tare da cin kofi ba tana da amsa mai sauƙi.

Abin da dokokin lashe ƙyautar suka tabbatar shi ne cewa ba dole ba ne ɗan wasa ya lashe kofi kafin ya zama zakaran Ballon d'Or.

Tarihin lashe ƙyautar mun samu misalai da yawa da ƴan wasa da suka karɓi Ballon d'Or ba tare da cin kofi a ƙungiya ba, kuma Cristiano Ronaldo ya yi haka a 2013 shi ne misali na baya-bayan nan.

Saboda haka, Mbappé cikin ƴan takara, amma samun zakaran bana zai kasance bayan ƴan jarida 100 sun kaɗa kuri'arsu.