Mutumin da ya yi kwanaki 555 ba tare da zuciya a jikinsa ba

Asalin hoton, Getty Images
Jikin ɗan Adam na da wata irin ƙwaƙƙwarar damar jure wa yanayi masu wahala, kamar yadda tarihi ya nuna a wasu lokuta, wasu mutanen sun rayu duk da rasa wasu muhimman sassan jikinsu.
Nazarin likitanci ya nuna cewa jikin ɗan Adam na iya jurewa fiye da yadda mutane da dama ke zato. Akwai wasu fitattun misalai da aka sani, ciki har da na wani mutum ɗan Faransa wanda likitoci suka gano a shekarar 2007 cewa yana rayuwa duk da cewa kusan kashi 90 cikin 100 na ƙwaƙwalwarsa ba sa aiki yadda aka saba.
Mutumin mai shekara 44 a lokacin yana rayuwa kamar kowane mutum, yana da aiki da iyali, kafin likitoci su gano cewa yana fama da wata matsananciyar cuta da ake kira hydrocephalus.
Wannan cuta na faruwa ne lokacin da ruwa ya taru a cikin ƙwaƙwalwa, lamarin da kan matsar da wasu sassan kwakwalwar tare da rage yawan ƙwayoyin halittar da ke cikinta
Wannan wani abin mamaki ne da ke nuna yadda jikin ɗan Adam ke iya daidaita kansa da manyan sauye-sauye da suka shafi muhimman sassan jikinsa.
Masana sun bayyana cewa sauran ƙwayoyin halittar kwakwalwar mutum na iya ɗaukar wasu daga cikin ayyukan wasu da suka lalace ko suka daina aiki, ta hanyar wani tsari da ake kira neuroplasticity.
Neuroplasticity na nufin ikon ƙwaƙwalwa na sake tsara yadda take aiki da kuma ƙirƙirar sabbin hanyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin kwakwalwa. Wannan ne ya sa wasu mutane ke iya ci gaba da gudanar da rayuwa ta yau da kullum duk da munanan matsalolin da suka shafi kwakwalwarsu.
Irin wannan yanayi na iya faruwa a wasu sassan jiki da ake da su bibbiyu, kamar huhu, ƙoda ko mazakuta. Idan ɗaya daga cikinsu ya lalace ko aka cire shi, wani lokacin ɗayan kan iya ɗaukar aikin dukansu tare da ba mutum damar ci gaba da rayuwa ba tare da wata babbar matsala ba.

Asalin hoton, Getty Images
Dabarun da likitoci ke yi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai a wasu lokutan, ci gaban kimiyyar likitanci ne ke ba mutane damar rayuwa bayan rasa wasu muhimman sassan jikinsu.
Ɗaya daga cikin misalan da suka fi jan hankali shi ne na wani matashi ɗan Amurka da ya shafe kwanaki 555 yana rayuwa ba tare da zuciyarsa ta asali a jikinsa ba.
A wannan lokaci, zuciyarsa ta daina aiki kuma an cire ta yayin da yake jiran a samu masa zuciyar da za a dasa masa.
A maimakon zuciyar da aka cire, likitoci sun yi amfani da wata na'ura ta musamman ta wucin gadi da ke taimakawa wajen zagayawar jini a jikinsa. An ce matashin yana ɗauke da wata na'ura mai aiki kamar zuciya a cikin jaka, wadda ta ba shi damar ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin da aka yi masa dashen sabuwar zuciya.
A wasu lokutan da ake kira "empty chest cases", likitoci kan cire zuciya da huhu gaba ɗaya daga jikin mara lafiya saboda tsananin rashin lafiyarsu.
Daga nan sai a haɗa mara lafiyar da wata na'urar tallafa wa rayuwa da ake kira ECMO, wadda ke ɗaukar aikin zuciya da huhu na ɗan lokaci har sai an samu mafita ta dindindin.
Baya ga waɗannan misalan, tarihin likitanci ya kuma tattara labaran wasu mutane da suka rayu duk da rasa sassa da dama na jikinsu. Waɗannan lokuta sun sa masana ke ƙara fahimtar irin ƙarfin da jikin ɗan Adam ke da shi wajen jurewa da kuma neman hanyoyin ci gaba da aiki ko da a cikin yanayi mafi wahala.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai misalan mutane da suka rayu duk da cewa sun rasa sassa da dama na jikinsu.
Wasu marasa lafiya masu fama da cutar sankarar ciki kan buƙaci a cire musu sassa da dama na tsarin narkar da abinci, ciki har da cikinsu gaba ɗaya, saifa, ƙaramin hanji da babban hanji.
A irin waɗannan lokuta, marasa lafiyar na iya ci gaba da rayuwa ta hanyar amfani da magungunan maye gurbin ruwa a jiki, tsarin cin abinci na musamman da kuma ba su abinci ta jijiyoyi. Haka kuma ana iya ba su sarrafaffen sukari domin maye gurbin sukarin da jikinsu ba zai iya samarwa da kansa ba.
Sauran sassan jikin da mutum zai iya rayuwa ba tare da su ba sun haɗa da mafitsara, thyroid da kuma dubura.
Sai dai har yanzu ba a fayyace takamaiman adadin sassan jikin da mutum zai iya rasa wa kuma ya ci gaba da rayuwa ba. Duk da haka, masana sun ce rasa sassa da dama a lokaci guda kan iya jawo mutuwa sakamakon zubar jini mai yawa, kamuwa da cuta ko mummunar rauni a jiki.



























