Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo: Yadda salon kwallon gwarzon dan wasan Man Utd ya sauya cikin shekaru
- Marubuci, Daga Emlyn Begley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United shekaru 12 bayan barin kungiyar - amma wanne irin dan wasa ne ya koma gasar Premier a yanzu?
Dan wasan ya ci kwallo 551, tun da ya bar Old Trafford ya koma Real Madrid a 2009, ya ci Champions hudu tare da kyautar Ballons d'Or ita ma guda hudu, ya ci La Liga hudu da kuma dan wasan da ya fi zura kwallaye da yawa a gasar.
Yayin da ya kai shekara 36, ta tabbata dan wasa ya wuce ganiyarsa, amma kididdiga ta nuna har yanzu yana cikin taurarin nahiyar Turai wadanda suka fi zura kwallo.
Ta yaya za mu iya kwatanta Ronaldo da kuma kalla a baya da na yanzu?
Kwallaye...
Yawan cin kwallayen Ronaldo ya ragu tun bayan da ya ci wa Real Madrid kwallo 40 a kaka uku cikin biyar. A 2014-15 ya ci kwallo 61 a wasa 54 da ya buga.
Duk da za a iya cewa nasararsa ba ta yi nisa ba Juventus, amma dai ya ci kwallo 101 cikin wasanni 134 da ya buga a duka gasa.
Idan muka kwatanta lokacin da Ronaldo yana matashinsa ya ci kwallo 118 a wasa 292 a kaka shida da ya buga a United.
Kwallaye 29 da ya ci su ne suka ishe shi ya zama ya lashe takalmin zinare, ya kara a kan wanda ya ci a Premier a (2008) da na La Liga a (2011, 2014 da kuma 2015).
A takaice tun bayan komawarsa Juventus a 2018, Robert Lewandowski da ya ci kwallo (99) da Messi da ya ci (91) ne kawai suka sha gabansa a cin kwallo inda ya ci 81.
Ya fi arry Kane da Erling Braut Haaland da Kylian Mbappe da dai sauran matasan 'yan kwallo zura bal a raga.
Kofuna...
Ronaldo ne daya daga cikin yan wasa biyu da suka fi cin kofin European/Champions inda ya lashe biyar - yaci hudu a Real Madrid bayan ya ci daya a Manchester United.
Ya kuma lashe kyautar Ballon d'Or ta dan wasan da ya fi kowa a duniya - inda ya lashe sau hudu bayan wanda ya fara ci a United.
Cikin shekara 11 bayan da yabar Manchester, ya lashe kofin gasar kasashe hudu ( biyu a Spaniya da na Italiya ).
A shekara shida da ya yi a United ya lashe kofina a kaka da dama, manyan kofi bakwai ciki har da na Premier da yaci sau uku a jere, da kuma wasu kananan kofina uku na daban.
A Madrid kuwa, ya lashe manyan kofina takwas da wasu kanana suma takwas a shekara tara da ya yi a kungiyar.
Ya lashe manyan kofina uku da Juventus da kuma wasu kanana cikin shekara uku da ya yi da su - sai dai lashe kofin Serie A da Inter Milan ta yi a bara ya kawo karshen shekaru tara da suka yi suna cin kofin a jere.
Ba da kwallo a ci...
A tarihin Ronaldo ya fi cin kwallo sama da yadda yake bayarwa a ci - amma dai ya bayar da kwallo da yawa an ci a La Liga (Kwallo 87 a kaka tara da ya buga).
Amma a yan shekarun nan, bayan zamansa lambara tara, yadda yake bayar da kwallo a ciki ya dan karu. Kaka biyar da ya yi ta karshe - biyu a Real Madrid uku a Juventus ya karu da kashi 5.4 cikin dari.
Hakan ya yi daidai da wadanda ya yi lokacin yana Manchester inda ya ke da kashi 5.67 cikin dari.
Salon taka leda....
Tabbas Ronaldo ya sauya cikin 'yan shekaru. A Manchester ya fara ne a matsayin dan wasan gefe mai cike da yanke-yanke a kafarsa.
Ya gina kansa ta yadda ya koma cin kwallo shi ne abin da ya sa a gaba, ya zama ya fi kowanne dan kwallo zura kwallo a tarihin Real Madrid.
A farkon zuwan sa Real yana yawan yanke-yanke bugun fenariti da kuma wasa da kwallo amma daga baya sai ya koma dan wasan tsakiya da baya da aiki sai cin kwallo.
Haka dai ya ci gaba ko lokacin da ya koma Juventus.