Jadawalin manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na zaɓen fitar da gwani

Nigeria major political parties

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP via Getty Images, ADC, NDC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Manyan jam'iyyu huɗu a Najeriya sun fitar da jadawalin da suke shirin bi wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani kafin babban zaɓen 2027.

Sabuwar jam'iyyar NDC ta fara bayyana shirinta na tantance da kuma zaɓar wanda zai wakilce ta a zaɓen 2027.

A baya, jam'iyya mai mulki ta APC ta riga ta fitar da sabon jadawali da tsarin ayyukanta, inda ta yi gyare-gyare kan lokacin tantance 'yan takara da zaɓen fitar da gwani, da kuma sauraron ƙorafe-ƙorafe da sauran matakan cikin gida na jam'iyya.

A cikin sanarwar, jam'iyyun sun kuma bayyana bayanan lambar asusun ajiya ta banki da masu sha'awar sayen fom ɗin tsayawa takara za su biya kuɗi domin samun fom ɗin shiga takara.

Sun ce dalilin gyaran jadawalin ya haɗa da bukatar daidaitawa da hutun ranar ma'aikata ta duniya, wanda ya shafi lokacin gudanar da wasu ayyukan cikin tsarin jam'iyya

A yayin da jam'iyyun adawa ke fuskantar rikice-rikicen kotu a 'yan kwanakin nan, jam'iyyar ADC ita ma ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na shekarar nan.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Jam'iyyar na Kasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta ce jadawalin na su ya nuna ƙudirin jam'iyyar na tabbatar da dimokuradiyya ta cikin gida da bin doka da oda, da kuma cikakken bin ƙa'idojin hukumar zaɓe.

Dangane da batun ko jam'iyyar za ta iya tsayar da 'yan takara a zaɓen 2027, ADC ta ce babu wani ɓangare na doka da ke hana ta shiga zaɓen. Ta kuma ƙara da cewa duk wani zance da ke nuna akasin haka "yunƙuri ne na ruɗa jama'a da kuma rage ƙwarin gwiwar 'ya'yan jam'iyyar."

Jam'iyyar ta kuma bayyana kanta a matsayin "babbar jam'iyyar adawa a Najeriya," tana mai cewa tana daukar wannan matsayi da muhimmanci.

A ɓangaren jam'iyyar Labour kuwa, ita ma ta fitar da nata jadawalin zaɓen fidda gwani, yayin da shirye-shiryen tunkarar zaɓukan 2027 ke ƙara ɗaukar hankali a faɗin kasar.

Jadawalin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar NDC

Sabuwar jam'iyyar NDC ta bayyana jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwanin 'yan takararta gabanin babban zaɓen shekarar 2027, tare da bayyana farashin fom da kuma rangwame ga wasu rukuni na 'yan takara.

Ga jadawalin kamar haka,

  • Sayar da fom: daga ranar 21 zuwa 23 ga watan Mayu
  • Tantance 'yan takara: daga ranar 26 ga Mayu
  • Zaɓen fidda gwani na muƙamai daban-daban: daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Mayu
  • Zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa: daga ranar 29 ga Mayu a Abuja

Farashin fom

  • Takarar shugaban ƙasa ciki har da fom ɗin nuna sha'awa da na takara kan naira miliyan 60
  • Takarar gwamna: kan naira miliyan 60 zuwa naira miliyan 30
  • Takarar sanata: kan naira miliyan 8
  • Takarar majalisar Wakilai: kan naira miliyan 6
  • Takarar majalisar jiha: kan naira miliyan 2.5

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa mata 'yan takara za su samu rangwamen kashi 50 cikin 100.

Masu nakasa kuma za su samu rangwamen kashi 25 cikin 100

NDC ta ce wannan tsari na daga cikin ƙoƙarinta na inganta shiga siyasa da kuma tabbatar da dimokuradiyya

Jadawalin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar ADC

Ga cikakken jadawalin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar ADC na shekarar 2026 kamar haka

  • Sayar da fom: daga ranar 5 ga Mayu zuwa 10 ga Mayun 2026
  • Mayar da takardun da aka cike: daga ranar 11 ga Mayu zuwa 13 ga Mayu, 2026
  • Tantance 'yan takara: daga ranar 14 ga Mayu zuwa 15 ga Mayu, 2026
  • Fitar da sakamakon tantancewa: daga 17 ga Mayu, 2026
  • Daukar korafe-korafe kan sakamakon: daga 18 ga Mayu zuwa 19 ga Mayu, 2026

Zaɓen fidda gwani

  • Majalisar Jiha da majalisar wakilai da majalisar Dattawa: daga ranar 21 ga Mayu, 2026
  • Zaɓen gwamna: daga 22 ga Mayu, 2026
  • Zaɓen shugaban ƙasa: daga ranar 25 ga Mayu, 2026
  • Taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar (NEC): daga ranar 26 ga Mayu, 2026
  • Babban taron musamman na ƙasa: daga ranar 27 ga Mayu, 2026
Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Jadawalin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC

Ga kuma cikakken jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC.

  • Sayar da fom: daga ranar 2 ga Mayu zuwa 4 ga Mayu, 2026
  • Mayar da takardun da aka cike: daga ranar 4 ga Mayu zuwa 5 ga Mayu, 2026
  • Tantance 'yan takara: daga ranar 6 ga Mayu zuwa 8 ga Mayu, 2026
  • Tantance 'yan takarar Shugaban Kasa: daga ranar 9 ga Mayu, 2026
  • Fitar da sakamakon tantancewa: daga ranar 11 ga Mayu, 2026
  • Ɗaukar korafe-korafe kan sakamakon tantancewa: daga ranar 12 ga Mayu zuwa 13 ga Mayu, 2026

Zaɓen fidda gwani

  • Majalisar wakilai: daga ranar 15 ga Mayu, 2026
  • Majalisar dattawa: daga ranar 18 ga Mayu, 2026
  • Majalisar Jiha: daga ranar 20 ga Mayu, 2026
  • Gwamna: daga ranar 23 ga Mayu, 2026
  • Shugaban ƙasa: daga ranar 25 ga Mayu, 2026
Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Jadawalin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Labour

Ga cikakken jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Labour kamar haka;

  • Sayar da fom: daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu, 2026
  • Mayar da takardun da aka cike: daga ranar 17 ga Mayu zuwa 18 ga Mayu, 2026

Tantance 'yan takara

  • Majalisar jiha da gwamna: daga ranar 20 ga Mayu, 2026
  • Majalisar wakilai da dattawa da shugaban ƙasa: daga ranar 22 ga Mayu, 2026
  • Fitar da sakamakon tantancewa: daga ranar 23 ga Mayu, 2026

Daukar ƙorafe-ƙorafe

  • Majalisar jiha da gwamna: 24 ga Mayu, 2026
  • Majalisar wakilai da dattawa da Shugaban Kasa: 25 ga Mayu, 2026
  • Fitar da jerin ƙarshe na 'yan takara da aka amince da su: 26 ga Mayu, 2026

Zaben fidda gwani

  • Majalisar jiha da gwamna: 27 ga Mayu, 2026
  • Majalisar wakilai da dattawa da shugaban ƙasa: 29 ga Mayu, 2026

Farashin Fom na Jam'iyyar Labour Party

  • Takarar shugaban ƙasa: Naira miliyan 50
  • Takarar gwamna: Naira miliyan 25
  • Takarar sanata: Naira miliyan 10
  • Takarar majalisar wakilai: Naira miliyan 5
  • Takarar majalisar jiha: Naira miliyan 3
Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin zaɓen shekarar 2027.

A cikin jadawalin, INEC ta bai wa jam'iyyun siyasa wa'adin tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayun 2026 domin su gudanar da zaɓukan fidda gwani, tare da warware duk wata matsala ko rigima da ka iya tasowa a cikin wannan lokaci.

Haka kuma, an bayyana cewa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya zai fara ne a ranar 19 ga watan Agusta, yayin da yaƙin neman zaɓen gwamna da na 'yan majalisar jiha zai fara a ranar 9 ga watan Satumba.