Ghana ta soma kwaso ƴan ƙasar daga Afirka ta kudu saboda rikicin ƙin jinin baƙi
Gwamnatin Ghana ta mayar da ɗaya daga cikin ƴan ƙasarta, Emmanuel Asamoah, wanda ke Afirka ta Kudu gida, bayan da aka ganshi a wani bidiyo a yayin da wasu ƴan Afrika ta Kudu suka tsare shi suna ce mishi 'ya koma gida ya gyara ƙasar sa'.
Lamarin ya fusata ƴan Ghana da dama, wanda ya kai har gwamnatin ƙasar ta gayyaci jami'an ofishin diflomasiyyar Afirka ta Kudu da ke Accra.
A yanzu haka ƙasar ta Ghana na tayin dawo da ƴan ƙasar da ke son dawowa, a yayin da ake gudanar da zanga zangar nuna ƙin jinin baƙi a Afirka ta kudun.
''Duk ɗan Ghana da ke son komawa gida ya tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar domin a dawo da shi a cikin aljihun gwamnati,'' a cewar ministan harkokin wajen Ghana Okudzato Ablakwah.
Wannan lamari na ƙin jinin baƙi dai ba sabon abu bane a Afirka ta kudu, inda ƴan ƙasar ke zargin baƙi da aikata laifuka da kuma ƙwace musu ayyuka.
Hukumomi Afirka ta kudun sun ce suna duba lamarin shigar baƙi ƙasar, sai dai mutane da dama na ganin akwai buƙatar Afirka ta kudu ta tuna da tarihin goyon bayan da ƙasashen da lamarin ya shafa suka bata, maimakon kai wa baƙi hari.