Manyan abubuwa biyar da Cristiano Ronaldo ke buƙata kafin ya yi ritaya

Asalin hoton, Getty Images
Da zarar an fara magana kan zaratan ƴan wasan ƙwallon ƙafa na duniya a tarihi, sunan Cristiano Ronaldo yana daga cikin na farko da ke zuwa zuciyar mutane musamman masu bibiyar harkar.
Tun bayan da ya fara haskawa a Sporting Lisbon kafin komawarsa Manchester United a shekarar 2003, ɗan wasan na Portugal ya gina tarihin da ƴan wasa kaɗan ne suka kai matakin.
Ya lashe kofunan lig a Ingila, Spain da Italiya, ya kuma kafa dimbin tarihin cin ƙwallaye da ba a taba ganin irinsu ba.
A sama da shekara 20 yana taka leda a babban mataki, Ronaldo ya lashe Champions League sau biyar, Ballon d'Or sau biyar, sannan ya jagoranci Portugal lashe kofin Turai na Euro a 2016 da UEFA Nations League biyu.
Haka kuma ya zama ɗanwasan da ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin wasannin ƙasa da ƙasa, tare da zama ɗaya daga cikin fitattun ƴanwasa da suka fi tasiri a duniyar ƙwallon ƙafa.
Sai dai duk da wadannan nasarori, akwai wasu manyan abubuwa da lambobin yabop da suka kuɓuce masa.
Ga wasu daga cikin manyan nasarori da tarihi da har yanzu Ronaldo zai iya nema kafin ya ajiye takalmansa, da kuma irin yiwuwar samun su.
Ƙwallo uku rigis da Cristiano Ronaldo ya zura ya taimaka wa Al-Nassr ta doke Al-Kholood da ci 5-3 a gasar Firimiya ta Saudiyya a ranar Alhamis, tare da kai yawan ƙwallayen da tauraron ɗan wasan na Portugal ya zura a rayuwarsa zuwa 985.
Wannan shi ne ƙwallo uku rigis na 67 da Ronaldo mai shekara 41 ya ci a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, yayin da yake ci gaba da kokarin cimma wani sabon tarihi a cikin fitacciyar sana'arsa.
Kofin duniya na FIFA
Duk da kusan duk wani babban kambu da ɗan wasan ya taɓa nema ya lashe, Kofin Duniya shi ne babban abin da har yanzu ya gagare shi.
Ronaldo ya buga gasar cin kofin duniya tun daga 2006 zuwa 2022, amma mafi nisan da Portugal ta kai a zamaninsa shi ne wasan kusa da na ƙarshe a 2006. A tarihi, yawancin manyan ƴan wasa kamar Pele, Maradona da Messi sun ƙara ƙarfi ga gadonsu ne bayan lashe kofin duniya.
Idan Portugal ta samu damar kai wa gasar ta gaba, tare da haɗin kan sabbin taurari kamar Gonçalo Ramos, João Neves da Vitinha, Ronaldo na iya zama wani ɓangare na tawagar.
Sai dai shekarunsa da ƙaruwa, kuma ƙarfin masu neman kofin kamar Spain, France da Argentina suna sanya wannan buri ya zama mafi wahala cikin jerin.
Ƙwallo 1,000
Za a iya cewa wannan shi ne tarihin da ya fi kusa da cimmawa. A tsawon shekaru an yi ta muhawara kan ko akwai wani ɗan wasa da zai taɓa kai wa ga samun nasara zura ƙwallo 1,000 a matakin manyan ƴan wasa.
Ronaldo ya karya kusan dukkan tarihin cin ƙwallaye da aka sani, kuma yanzu ya rage masa ƴan ƙwallo kaɗan don kai wannan adadi.
Idan ya ci gaba da taka leda na kakar wasa ɗaya ko biyu, musamman a Saudiyya da kuma tawagar Portugal, akwai yiwuwar ya zama mutum na farko da ya kai wannan adadi a zamanin kwallon kafa na zamani.
Zuwa yanzu yana da ƙwallo 981 ko 982 (akwai ƙwallon da ya zura da ake kai-komo a kai) a ƙungiyar Al Nassr.
Amma koma dai yaya ne, za a iya cewa saura ƙiris fitaccen ɗanwasan ya cika burinsa na zura ƙwallo 1,000.
Lashe AFC Champions League
Lokacin da Ronaldo ya zo Al-Nassr a ƙarshen 2022, ɗaya daga cikin manyan manufofin kulob ɗin shi ne mamaye ƙwallon ƙafa ta Asiya.
A Turai, ya gina sunansa ne ta hanyar lashe Champions League sau biyar. Amma har yanzu bai taɓa zama zakaran Asiya ba.
A tarihi, wasu daga cikin manyan ƴan wasan Turai da suka je Asiya sun kasa lashe babbar gasar nahiyar. Lashe AFC Champions League zai ba Ronaldo damar zama ɗaya daga cikin tsirarun ƴan wasan da suka yi tasiri a nahiyoyi biyu daban.
A yanzu ƙungiyar Al Nassr tana fafatawa a gasar, inda Ronaldo ke da burin lashe kofin.
Lashe Ballon d'Or na shida
Ronaldo na da Ballon d'Or biyar a tarihinsa, kuma tsawon shekaru ya yi gogayya da Lionel Messi wajen mamaye kyautar.
Sai dai tun bayan da ya bar Turai ya koma Saudiyya, damar sake lashe kyautar ta ragu sosai. Sabbin taurari irin su Kylian Mbappé, Erling Haaland da Lamine Yamal suna mamaye hankulan masu kada kuri'a.
Duk da haka, idan ya kai ƙwallaye 1,000 tare da lashe manyan kofuna da Al-Nassr ko Portugal, za a iya sake buɗe tattaunawa game da kyautar.

























