Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kama mahaifin Adeyemi Adeniyi: Me dokar Najeriya ta ce?
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da rahotonnin kamen da ake zargin jami'an tsaro sun yi wa mahaifi da dangin shugaban hukumar PFIPC da ake zargi ta bogi ce.
A ranar Litinin ne bayanai suka ce ƴansanda sun kai samame gidan Prince Adeniyi Adeyemi da ke Ogbomoso na jihar Oyo tare da kama wasu daga cikin danginsa ciki har da mahaifinsa.
A baya-bayan nan ne dai aka zargi Prince Adeniyi Adeyemi da kafa sabuwar hukumar gwamnati ta bogi, wadda kuma har ta samu kaso a kasafin kuɗin ƙasar na 2026.
Bayanai sun ce an kama dangin nasa ne a lokacin da suka ziyarci gidan Adeyemi a ranar Litinin.
Sai dai babu bayani dangane da ko jami'an tsaron sun kama dangin Prince Adeyemi bisa hannu a laifin da ake zargin ɗan uwan nasu da aikatawa.
A cikin wannan muƙala mun duba abin da dokokin Najeriya suka tanada kan kama wani bisa laifin ɗan'uwansa.
Abin da dokar Najeriya ta ce kan kama iyalan mutumin da ake zargi
Masana shari'a na dokokin Najeriya na cewa dokar ƙasar ba ta bayar da damar kama dangin wanda ake zargi da aikata laifi ba.
Barista Hamza Nuhu Dantani, fitaccen lauya ne da ke fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam kuma masanin dokokin Najeriya ya shaida wa BBC cewa dokar Najeriya ba ta bayar da damar kama ɗan'uwan wanda ake zargi da aikata laifi ba.
''Ai a tsarin dokar Najeriya, ko shi wanda ake zargin ba a ɗaukar sa a matsayin mai laifi har sai kotu ta same shi da laifi, don haka ko shi yana da haƙƙokin da suka kamata hukumomi su kare masa'', in ji shi.
Masanin shari'ar ya kuma ce''sashe na 35 sakin layi na ɗaya na dokokin Najeriya ya ba shi damar walwala a cikin ƙasa, kuma babu wata doka da ta ce a tauye masa wannan ƴancin nasa'', in ji shi.
Barista Dantani ya ce duk mutumin da ya aikata laifi, to shi ake kamawa ba dangi ko ƴan'uwansa ba.
''Sashe na 36 na kudin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasar damar cewa shi ba mai laifi ba ne har sai kotu ta same shi da laifin'', in ji shi.
Sai dai lauyan ya ce ƴansandan za su iya kama wani ɗan'uwan wanda ake zargi da laifi, idan har bincikensu ya gano cewa ɗan'uwan nasa na da hannu a laifin da ake zargin sa da shi.
''Idan har a binciken ƴansandan suka gano cewa alal misali ɗan'uwan na da hannu a laifin da ake zargin mutumin ya aikata, ko tare suka aikata, ko ya taimake shi wajen aikata laifin to za su iya kama shi domin ci gaba da bincike'', in ji shi.
Fitaccen lauyan ya ce in dai ba haka ba, to babu inda dokar Najeriya ta ce a kama ɗan'uwan wanda ake zargi da laifi.
Me ya kamata mutum ya yi idan an kama shi kan laifin wani?
Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce duk mutumin da aka kama ba tare da laifinsa ba, ko kan zargin laifin wani akwai hanyoyin da zai bi wajen ƙwato haƙƙinsa.
''Na farko zai rubuta wa shugaban wannan hukuma wasiƙa, ya bayyana masa irin yadda aka kama shi, aka ci zarafin sa ba tare da laifinsa ba'', in ji shi.
Lauyan ya ce kodayake wanann wasiƙa ba za ta dawo masa da haƙƙinsa ba, amma dai ya nuna masa cewa an tauye masa haƙƙinsa.
Daga nan mutum zai iya samun lauya domin shigar da ƙara a gaban kotu don ƙwato masa haƙƙinsa da aka tauye.
Ya ƙara da cewa idan har kotu ta same su da laifi, za ta iya tilasta wajami'an tsaron su biya mutum diyya cin zarafinsa da aka yi ba tare da laifinsa ba.
Wane ne Prince Adeniyi Adeyemi?
Kafin yanzu babu wani cikakken bayani a bayyane game da Prince Adeniyi Adeyemi, in ban da kasancewarsa shugaban hukumar PFIPC da aka fi sani da kwamitin shugaban ƙasa kan shawarwarin bunƙasa tattalin arziki..
Hukumar ta ayyana kanta a matsayin cibiyar gwamnati a shafin Instagram wadda ke "aiwatar da haɗin gwiwa don janyo masu zuba jari daga ƙetare zuwa Najeriya''.
Bisa ga bayanan shafin na Instagram, an buɗe shi ne a 2025, kuma adireshin hukumar na yanar gizo: www.pfipc.gov.ng ba ya tafiya lokacin da muke haɗa wannan labari.
To sai dai wannan Adeniyi Adeyemi ba shi ne Prince Akeem Adeniyi Adeyemi, ɗanmajalisar wakilan Najeriya ba, suna dai da suna iri ɗaya ne.