Cutuka biyar da yawan kallon waya ke haifarwa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Na'urorin laturoni, kamar wayoyin hannu na shafar lafiyar jikinmu ta hanyoyi masu yawa ba tare da mun ankare ba, amma akwai matakan da za ku iya ɗauka domin kare kanku.

Idan za mu yi magana a kan yadda wayoyin hannu ke shafar lafiyarmu, to ƙwaƙwalwa ce farko.

Thomas Germain , wani ɗan jarida ya ce a baya-bayan nan ya lura da wani tabo a yatsarsa da yake amfani da shi wajen latsa wayarsa.

Lamarin ya ba shi mamaki, ''ta yaya wani sahe na jikina zai yi taba ta dalilin taɓa wayata?''

Ya tuntuɓi masana domin gano abin da ya same shi, amma amsar da ya samu ta ba shi mamaki.

Binciken masana a baya-bayan an ya gano cewa wayoyinku ka iya sauya halittar wuyanku, su kuma lalata ganinku, sannan su shafi yadda kuke tafiya tare da raunanan tsokokin jikinku.

Wasu daga cikin waɗannan matsaloli kan shafi raunin tunani ko haifar da matsalolin lafiya.

Idan ba ka so fasahar zamani ta yi muku illa a jikinku, akwai matakan da za ku domin kauce wa faruwar hakan.

Ciwon laka

Idan yanzu kuna karanta wannan labari, wataƙila ƙasa kuke kallo, kun sunkuya kan wayanku.

Ana kiran wannan yanayi da suna "head-scratching", kuma tana sanya nauyi mai yawa a kan ƙashin bayan wuya da na baya.

Idan wannan yanayi ya ci gaba na tsawon lokaci, zai iya haifar da lahani ga ƙashin baya, ya jefa gaɓɓai da tsokoki cikin matsananciyar aiki, sannan har ma ya rage ƙarfin huhu wajen ɗaukar iska.

Ana kiran wannan cuta da "tech neck," wato cutar da aka samu ta hanyar fasahar zamani.

Takan kuma sauya yanayin halittar jikinku. Akwai wasu nau'ikan motsa jiki da likitoci ke shawartar mutane su domin rage matsalar.

Haka kuma, akwai wasu dabaru da za ku iya yi a lokacin da kuke kallon wayar, kamar ɗaga wayar sama ta yadda za ku daina sunkuyar da wuya.

Wasu masana na bayar da shawarar ɗaukar hutu daga kallon waya.

Masanan sun ce a yi ƙoƙarin ɗaukar hutun minti 20 daga kallon waya bayan ka yi minti 30 kana kallonta.

Ƙaiƙayin fata da tamojin wuya

A baya-bayan nan, an fara nuna damuwa kan ko yawan amfani da na'urorin laturoni, musamman wayoyin hannu, na iya haifar da bayyanar takushewar fatar wuya ko ƙurajen fata a wuya.

Wasu masana na ganin cewa yawaita sunkuyar da kai na dogon lokaci yayin kallon waya ko kwamfuta na iya janyo fatar wuya ta riƙa lanƙwashewa akai-akai, lamarin da ka iya sa layukan tsufa su bayyana da wuri a wannan wuri.

Dokta Justine Hextall, ƙwararriyar likitar fata ya ce hakan abu ne mai yiwuwa.

Hextall ta kuma yi gargaɗin sayen magungunan da ake tallatawa a yanar gizo da ke ikirarin magance matsalar fatar wuya da aka samu sakamkon kallon waya.

Akwai kuma sauran matsalolin fata da aka tabbatar, musamman ga mutanen da ke sanya agogunan zamani na tsawon lokaci.

Dr Justine Hextall ta ce wurin da ake ɗaura agogon a hannu na iya bai wa ƙwayoyin cuta damar yaɗuwa, wanda kuma ka iya haifar da ƙuraje da matsalolin fata.

Shafar ƙarfin gani

A ƴan shekarun baya-bayan nan an samu gagarumar matsalar raguwar gani tsakanin mutane. Kuma ko shakka babu yawan kallon waya na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar.

A cewar Farfesa Donald Mutti, ƙwararren likitan ido hakan ka iya zama gaskiya, amma ba kamar yadda mutane ke tunani ba.

Mutti ya ce wani bincike da aka kwashe fiye da shekaru 20 ana yi ya duba yadda ganin idanun yara ke bunƙasa da kuma abubuwan da ke haddasa matsalolin gani.

Ɗaya daga cikin manyan tambayoyin da binciken ya mayar da hankali a kai shi ne gano alaƙar da ke tsakanin matsalar rashin ganin abubuwan da ke kusa (short-sightedness) da ayyukan da ake yi daga kusa, kamar karatu ko amfani da wayar hannu.

Sakamakon binciken bai tabbatar da alaƙa tsakanin matsalar rashin gani da kuma amfani da wayoyi.

Mutti ya ƙara da cewa fasaha ka iya shafar ganinku saboda tana sa mutane su ɗauki lokaci suna zaune su kaɗai cikin ɗakuna.

An yi imanin cewa hasken rana na ƙarfafa fitar wani sinadari da ake kira dopamine a bayan ido, wanda ke taimakawa wajen bunƙasa lafiyar ido da kuma ci gabansa yadda ya kamata.

Raunana hannaye

Ana ɗaukar ƙwarewar amfani da hannaye wajen aiwatar da ayyuka (manual dexterity) a matsayin wata muhimmiyar alama ta raguwar ƙarfin jiki gaba ɗaya.

A ƙasashe da dama, an lura cewa wannan ƙwarewa tana ci gaba da raguwa a tsakanin matasa, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin masana lafiya da masu bincike.

A cewar Farfesa Johannes Beller, wani ƙwararren masanin lafiya, ya ce raguwar ƙarfin jiki ga ƙananan yara ka iya zama gargaɗi ga makomar lafiyar ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa aikin ofis da yawan zama na taka muhimmiyar rawa wajen raguwar ƙarfin jiki, wanda zai shafi ƙarfin hannaye.

Ana shawarartar mutane to chichilla wasu ƙananan abubuwa kamar bal ɗin table tennis na tsawon sakan 15 zuwa 30.

Ido da aikin hannu

Kallon waya na da tasiri kan motsin hannaye da ke haɗa kwakwalwa da jiki wajen aiki tare.

Masana na ganin cewa yawan amfani da na'urorin zamani na iya sauya yadda hannu da yatsu ke motsi, lamarin da ka iya shafar wasu sassan jiki da ke buƙatar daidaituwa tsakanin tunani da motsin jiki.

Farfesa Sebastian Suggate, ƙwararren masanin ɗabi'un ɗan'adam ya ce yawan amfani da yawan na iya shafar motsin hannaye.

Suggate ya ce duk da cewa ba a haramta amfani da wayoyin ba, amma yana shawartar mutane su riƙa amfani da ita sannu-sannu, tare da surkawa da sauran ayyukan hannu.

Abubuwan da ya bayar da shawarar yi sun haɗa da saƙa da sana'o'in hannu da aikin katako da amfani da kayan kiɗa ko rubutu da sauransu.