Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Salah ko Messi, wane ne zai yi wasansa na ƙarshe a gasar bana?

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagaye na biyu
Argentina 0 , Egypt 0
Argentina
Masar
6 minutes , in progress

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi

  1. An fara wasa: Argentina 0-0 Masar, Argentina 0-0 Masar

  2. Ƴan wasan Argentina

    Argentina XI: Emiliano Martinez, Molina, Romero, Lisandro Martinez, Tagliafico, De Paul, Mac Allister, Paredes, Fernandez, Messi, Alvarez

  3. Ƴan wasan Masar

    Egypt XI: Shoubir, Hany, Ibrahim, Rabia, Hafez, Ashour, Attia, Lasheen, Hassan, Salah, Zico

  4. Salah ko Messi, wane ne zai yi rawarsa ta ƙarshe a gasar bana?

    Argentina za ta fafata da Masar a Atlanta a yau Talata don samun gurbi a wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya na 2026. Haka kuma karawa ce ta manyan ƴan wasa biyu.

    Messi, mai shekaru 39, da Salah, mai shekaru 34, dukkansu sun ɗauko gangara a lokacinsu na taka leda. Messi ya riga ya yi nuni da cewa wannan zai zama Gasar Cin kofin duniyarsa ta ƙarshe, kodayake Salah har yanzu yana fatan bugawa a 2030.

    Messi ya lashe kofin duniya a 2022, yanzu haka shi ne mafi yawan ƙwallaye a gasar, kuma a gasar bana yana kan gaba a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a gasar.

    Shi kuma Salah,labarinsa ya bambanta. Wannan shi ne gasar cin kofin duniya ta uku da ya ke buga wa Masar, amma wannan ne karo na farko da ya ke buga wasa a zagayen kifa-ɗaya-ƙwala inda da ƙasarsa ta kai zagaye na ƴan16 a karon farko.

    Masar ta sha kashi a wasan ƙarshe na gasar cin kofin ƙasashen Afirka a shekarar 2017 da 2021 a lokacin da ya ke cikin tawagar.

    Fanareti nau'in Panenka da ya buga ya taimaka wa ƙasarsa ta kafa tarihi ta hanyar yin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida a kan Australia a zagayen ƴan 32, kuma yana fatan ranar Talata za ta zama babbar nasararsa a gasar cin kofin duniya.

    Ko Argentina za ta iya kare kambunta?

    Kalmar da aka fi yawan ambata a Argentina a yanzu ita ce 'bicampeonato' (zama sau biyu a jere).

    Amma tambayar da kowa ke tunani, kuma babu wanda yake son ambata, shine 'me zamu yi idan Messi ya yi ritaya'?

    Duk wani sabon wasa da tawagar ƙasar za ta buga a gasar cin kofin duniya - kamar wasan da za ta yi da Masar a ranar Talata - wani mataki ne na haɓaka damar samun nasarar da wasu ƙasashe biyu kacal suka taɓa samu a baya (Italiya a 1934 da 1938; Brazil a 1958 da 1962).

    Duk da haka, kowane wasa kuma yana kawo mu kusa da ritayar fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina kuma kyaftin ɗin tawagar ƙasar, Messi.

    Ƙwallayen da ya ci a wannan gasa (bakwai), da sabbin tarihin da ya kafa (wasa a gasar cin kofin duniya karo na shida, da zura ƙwallo a wasanni takwas a jere), da kuma wasa mai ban mamaki kamar wasan da Cape Verde ta yi, sun sa ƙasar ta mai da hankali kan halin da ake ciki yanzu.

    Abin da ya ɗaure wa masharhanta kai shi ne , Messi yana wasa kamar yana da shekaru 25, ba mai shekaru 39 ba.

    Amma duk mun san cewa mutumin da ya jagorance su zuwa nasarar cin Kofin Duniya (Qatar 2022) da kofunan Copa America guda biyu (Brazil 2021 da Amurka 2024) yana rawarsa ta ƙarshe ne da bazar rigar Argentina.

    Salah abin alfahari ne ga ƴan Masar

    Salah ba ɗan wasan ƙwallon ƙafa ba ne kaɗai a Masar, babban abin alfahari ne shi da ya zama dalilin farin cikin da ƙwarin gwiwar ƙasa baki ɗaya.

    Yana ƙarfafa gwiwar miliyoyin ƴan Masar kowace rana. Labarinsa na yadda ya fito daga ƙaramin ƙauye a Nagrig zuwa manyan filayen ƙwallon ƙafa a duniya, abin alfahari ne da kowanne ɗan Masar.

    Yana nuna cewa idan har aka yi aiki tuƙuru, komai yana yiwuwa. Mutane suna ganinsa kuma suna yi wa kawunansu kyakkyawar zaton yin abin kirki, ba kawai a fagen ƙwallon ƙafa ba, har ma a rayuwa baki ɗaya.

    Mutanen Masar suna matuƙar kaunar Salah. Yakan haɗa kan al'ummar ƙasar. Idan yana buga wasa, za ka ji cewa ɗaukacin ƙasar na bayansa, suna alfahari da shi a duk lokacin da ya shiga filin wasa.

    Salah ba kawai babban ɗan wasan ƙwallon kafa ba ne, shi abin alfahari ga duk wani dan ƙasar Masar.

    Yadda wasannin suka kaya tsakanin ƙasashen biyu

    Wasan zagaye na ƴan 16 na gasar cin kofin duniya tsakanin Argentina da Masar a gasar bana zai kasance karo na biyu da Albiceleste da Pharaohs suka fafata a gasar ƙwallon ƙafa ta manyan ƴan wasa.

    Wasa ɗaya kacal da ƙasashen biyu suka fafata a baya ya zo ne a watan Maris na 2008, lokacin da wata tawagar Argentina ƙarƙashin jagorancin Alfio Basile ta yi tafiya zuwa filin wasan birnin Cairo don wasan sada zumunci da Hassan Shehata ta Masar, wanda Argentina ta lashe da ci 2-0.

    Lionel Messi bai buga wannan wasan sada zumuntar ba saboda raunin da yake fama da shi a lokacin, amma tawagar Argentina ta kasance tana da wasu manyan ƴan wasa da dama, kamar su Javier Zanetti da Javier Mascherano da Pablo Zabaleta.