Yankuna 5 da suka fi haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Da zarar damina ta fara kankama a Najeriya, wasu al'ummomi ke shiga cikin fargabar halin da matsugunansu ko gonakinsu za su kasance sakamakon yiwuwar ambaliyar ruwa da za ta iya afka musu a kowane lokaci.
Ba ruwan sama kaɗai ke haddasa ambaliya ba. Yanayin ƙasa, kusanci da manyan koguna da madatsun ruwa, sakin ruwa daga wasu madatsun da ke cikin Najeriya da ma na ƙasashe maƙwabta, da kuma matsalolin magudanan ruwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara jefa wasu yankuna cikin haɗari.
A 2024 an samu wata mummunar ambaliya a Maiduguri jihar Borno wadda ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Haka ma, a garin garin Mokwa da ke jihar Neja an samu irin wannan ibtila'i a 2025.
To amma waɗanne yankuna ne suka fi rayuwa cikin irin wannan barazana? Kuma me ya sa ambaliyar ke yawan komawa wuraren nan duk shekara?
A wannan rahoton, mun duba wasu daga cikin yankunan Najeriya da masana ke ganin sun fi fuskantar haɗarin ambaliya.
Waɗanne yankuna suka fi fuskantar ambaliya?
A daidai lokacin da ake cikin wannan fargaba, Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta sake yin gargaɗin cewa akwai yiwuwar wasu yankuna su fuskanci ambaliya tsakanin 14 zuwa 20 ga watan Yuli.
Hukumar ta ce hasashen da ta yi ya nuna cewa akwai wurare 16 da suke cikin haɗari, musamman waɗanda ke kusa da manyan koguna da rafuka.
Daga cikin wuraren da ta ambata akwai Saminaka da ke kusa da kogin Karam, yankin madatsar Waya da ke kogin Waya, da kuma Amber da ke kogin Amber.
Jihohin da NIHSA ta ce za su iya fuskantar matsakaicin haɗarin ambaliya sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Benue, Borno, Cross River, Edo, Enugu, Imo, Kaduna, Lagos, Neja da kuma Filato.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kariya ba, ambaliyar na iya shafar gidaje da makarantu da cibiyoyin lafiya da kasuwanni da kuma hanyoyin sufuri.
Saboda haka, ta buƙaci mazauna yankunan da aka fi fargabar ambaliya su koma wurare masu aminci idan buƙatar hakan ta taso, kuma su riƙa share magudanan ruwa, su guji ketare wuraren da ruwa ya mamaye, sannan su riƙa bibiyar sanarwar hasashen ambaliya da hukumar ke fitarwa.
Haka kuma NIHSA ta buƙaci gwamnatocin jihohi da hukumomin bayar da agajin gaggawa su riƙa gargaɗin al'umma, da kwashe jama'a daga yankunan da ke cikin wannan haɗari da kuma wayar da kan al'umma.
Akwai wasu yankuna da ake yawan samun ambaliyar ruwa saboda yadda suke kusa da manyan koguna da madatsun ruwa, ko kuma saboda ruwa da ake saki daga wasu manyan madatsun da ke cikin Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Waɗannan yankuna na daga cikin yankunan da ambaliya ke yawan addaba a duk lokacin damina.
Duk da yake a wasu lokutan hukumomi na bayar da shawarar su ƙauracewa irin waɗannan wurae, daga bisani a kan samu akasi har lamarin ya shafi wasu mazauna kuda da waɗannan wurare.
Yankunan da ke kusa da Madatsar Lagdo

Asalin hoton, Getty Images
Jihohin Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa da Kogi su ne ke fuskantar wannan ibrila'i, musamman idan aka saki ruwa daga madatsar Lagdo da ke ƙasar Kamaru.
Ruwan ya kan ci gaba da ratsawa har zuwa wasu yankuna kamar Anambra, Bayelsa, Delta, Edo, Rivers da wasu sassan Cross River.
Tun a shekarar 1982 aka kammala gina madatsar Lagdo domin samar da wutar lantarki da ruwan ban-ruwa a arewacin Kamaru. Sai dai idan ruwan ya yi yawa, hukumomin ƙasar kan saki wani ɓangare daga cikinsa, wanda ke ƙara yawan ruwan kogin Benue da ke ratsawa Najeriya.
Masana sun ce ɗaya daga cikin dalilan da ke sa matsalar ta ci gaba shi ne rashin kammala aikin Madatsar Dasin Hausa a jihar Adamawa, wadda aka tsara domin ta riƙe wani ɓangare na ruwan da ake saki daga Lagdo kafin ya bazu zuwa sauran jihohi.
Yankunan da ke gaɓar kogin Neja
Yankunan da kogin Neja ke ratsawa, musamman a jihohin Neja, Kwara da Kogi, na yawan fuskantar ambaliya.
Masana na danganta hakan da yawan ruwan sama da kuma kasancewar wasu manyan madatsun ruwa irin su Kainji da Jebba, waɗanda ke cikin kogin.
A farkon shekarar 2025, ambaliya ta lalata kusan eka 5,000 na gonakin shinkafa a ƙananan hukumomin Moro, Edu da Patigi na jihar Kwara.
Yankunan Maiduguri da Jere
A jihar Borno kuwa, al'ummomin Maiduguri da Jere na daga cikin wuraren da ake sa ido sosai idan damina ta yi ƙarfi.
A shekarar 2024 an samu wata mummunar ambaliyar bayan lalacewar wani ɓangare na Madatsar Alau, inda ta mamaye kusan kashi 40 cikin 100 na Maiduguri, kuma ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba dubban iyalai da matsugunansu.
Takum da Katsina-Ala da kewaye
Gwamnatin Najeriya ta gina Madatsar Kashimbila domin rage illar ambaliyar ruwa da kuma samar da lantarki, ruwan sha da na ban-ruwa ga al'ummomin yankin.
Sai dai al'ummomin da ke yankunan Takum a jihar Taraba da kuma wasu sassan da rafin Katsina-Ala ke ratsawa zuwa jihohin Benue, Kogi, Cross River da Delta na daga cikin wuraren da ake sanya ido a kai saboda haɗarin ambaliya.
Sai dai rashin kammala aikin madatsar baki ɗaya ya sanya har yanzu al'umma a wasu jihohin Najeriya na kasancewa cikin hatsarin ambaliya da zarar aka saki ruwa daga madatsar Lagdo da ke Kamaru.
Yankunan da ke kusa da rafin Kaduna
Wasu yankunan jihar Neja da ke kusa da Shiroro ma na fuskantar haɗarin ambaliya lokaci bayan lokaci.
Idan aka samu damina marka-marka, rafin Kaduna ya kan cika ya tumbatsa har ya kai ga haifar da ambaliya ga ƙauyukan da ke kusa da shi.
Me ya sa waɗannan yankuna suka fi fuskantar ambaliya?

Asalin hoton, Getty Images
A game da abin da ke faruwa daga madatsun ruwan har a samu ambaliya, BBC ta tattauna da Umar Ibrahim Muhammad, darakta-janar na hukumar NIHSA, inda ya ce yawanci madatsun ruwan Najeriya suna haifar da ambaliya idan idan sun cika, sun tumbatsa.
Ya ce, "abin da ke faruwa shi ne ba a so waɗannan madatsun ruwan su cika, har ya zama an saki ruwan zuwa koguna. Akwai abin da ake kira "dam management", akwai wani mataki da ba a ruwn ya wuce. Don haka idan ba a kula da waɗannan matakan, sai ruwan ya tumbatsa, da dole a sake shi ba tare da shiri ba."
Sai dai ya ce a kan samu matsala,"kamar irin ta bara a Maiduguri wanda masu kamun kifi suka buɗe wani waje a dam ɗim domin su yi kamun kifi. Wannan ɗan ɓulin ne da ruwan ya yi yawa, har ya rinjaye shi ya ɓalle ya yi ambaliya."
Ta wace hanya za a rage haɗarin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban hukumar ta NIHSA ya ce akwai matakan da suke ɗauka tare da ɓangaren kula da madatsun ruwa domin kiyaye aukuwar ambaliyar.
"Muna magana da su ne domin sanin matakin da ruwan ke ciki a madatsun ruwa, mu kuma muna faɗa musu matakin da kogunanmu suke ciki. Hakan zai sa a san yaushe ya kamata a sako ruwa da kuma lokacin da bai kamata ba. Hakan ya sa ake samun sauƙin sako ruwan domin ana yi a hankali."
Ya ce fitar da ruwan a hankali ne ke sa kogunan suke iya kwashewa suna tafiya da su cikin sauƙi ba tare da madatsun sun cika maƙil ba, ballantana ma su fi ƙarfin madatsun, har su yi ambaliya.
"Yanzu haka mun ce a riƙa sako ruwan kaɗan-kaɗan saboda kogunanmu ba su cika ba, kuma madatsun ruwan ma ba su cika ba. Ka ga tun yanzu ya kamata su riƙa sako mana ruwan a hankali suna tafiya ta kogunan."
Umar ya ce ko a bar ambaliyar da aka samu ba daga madatsun ruwa aka samu matsalar ba, domin a cewarsa, "madatsun ba su yi cikar da gagara ba har su sako ruwan."
Matakan kariya
Shugaban hukumar ta NIHSA ya ce duk matakan da ya kamata su ɗauka, sun ɗauka, "kamar wayar da kan al'umma a kan nisantar wuraren da aka hasashen ambaliya. Ka san duk matakan da aka ɗauka, dole a yi nisa saboda yanayin sauyin yanayi ya sa ba za mu iya cewa tabbas ba za a yi ambaliyar ba."
Sai dai ya ce ana aikin gina wasu madatsun ruwa da za su taimaka wajen tare ruwa daga manyan madatsun da suke jawo a ambaliyar a ƙasar.
"Akwai madatsun ruwan biyu a Benue da ɗaya a Adamawa sai wani a Kebbi, waɗanda aka tanada domin tare ruwa idan an sako su daga madatsun."











