El Clasico: Yadda Real Madrid ta doke Barcelona a Nou Camp

Real Madrid
An wallafa

Real Madrid ta doke Barcelona ci 1-3 wasan Clasico na farko da manyan ƙungiyoyin biyu suka fafata a La liga.

Real Madrid ta huce ne kan Barcelona bayan ta sha kashi a wasanni biyu biyu da ta buga kafin Clasico a hannun Cadiz a La liga da kuma Shakhtar Donetsk a gasar zakarun Turai ta Champions League.

Valverde da Ramos da Modric ne suka ci wa Real Madrid kwallayenta a ragar Barcelona.

Ansu Fati ya rama wa Barcelona ƙwallo ta farko da Valverde ya ci ana minti biyar da wasa.

Yanzu Real Madrid ta ba da tazarar maki uku a saman teburin La liga tsakaninta da Real Sociedad da ke matsayi na biyu kafin ta buga wasanta da Huesca a ranar Lahadi.

Barcelona yanzu tana matsayi na 12 da maki bakwai, tazarar maki shida tsakaninta da Real Madrid da ke saman teburin La Liga.

Barcelona ta sha kashi sau biyu a jere kenan a La liga bayan Getafe ta doke 1-0 a ƙarshen makon da ya gabata.

Yadda aka yi fafatawan Clasico

Modric sai da ya yanke gola ya jefa kwallo a ragar Barcelona ana dab da hure wasa
Bayanan hoto, Modric sai da ya yanke gola ya jefa kwallo a ragar Barcelona ana dab da hure wasa
A bugun fanariti Ramos ya ci kwallo ta biyu
Bayanan hoto, A bugun fanariti Ramos ya ci kwallo ta biyu
Yadda Ansu Fati ya ci wa Barcelona kwallo a ragar Madrid
Bayanan hoto, Yadda Ansu Fati ya ci wa Barcelona kwallo a ragar Madrid
Varlvade ya fara bude ragar Barcelona
Bayanan hoto, Valvarde ya fara bude ragar Barcelona
Messi
Bayanan hoto, Messi ya nemi fanariti bai samu ba