Me ya sa yanzu ake yawan jin amon ƴan Kannywood a harkar siyasa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Me ya sa ƴan Kannywood ke tsoma kansu cikin siyasa?

Tallata ƴantakara ko yaƙin neman zaɓe, ginshiƙin ala'amari ne a kowane tsarin zaɓe.

Masu tallata ƴantakarar kan taka muhimmiyar rawa a nasararsu a zaɓukan.

Ƴansiyasa kan yi amfani da shahararrun mutane wajen tallata manufofinsu da jam'iyyunsu.

Don haka ne ƴan Kannywood ke bazama musamman idan lokacin zaɓe ya ƙarato wajen karɓo tallan ƴansiyasa daban-daban.

Hukumar zaɓen Najeriya ta saka watan Satumba domin fara yaƙin neman zaɓen 2027 a hukumance.

Tuni dai ƴanmasana'antar da ke shirya fina-finai a arewacin Najeriya suka bazama domin tallata ƴankararsa duk da cewa lokacin fara hakan bai yi ba a hukumance.

Fitattun da kawo yanzu aka ji sautinsu sun haɗa da:

Dauda Kahutu Rarara

Dauda Kahutu Rarara ya kasance jigo a tafiyar ƴan Kannywood da ke goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki.

A baya-bayan nan fitaccen mawaƙin siyasar ya mayar wa fitaccen mawaƙin Najeriya Davido martani kan bayyana da sunayen yara ɗalibai da aka sace a Oyo a bikin buɗe Gasar Kofin Duniya.

Rarara ya zargi Davido da kwance wa gwamnatin Tinubu zane a kasuwa, lamarin da ya janyo musayar martani tsakaninsa da Davido.

Mawaƙin ya riƙa jagorantar kafa ƙungiyoyin siyasa daban-daban a lokutan zaɓe domin gudanar da yaƙin neman zaɓe.

A 2023 ya kafa ƙungiyar 13x13 domin tallata ƴantakarar da suke goyon baya.

Haka kuma a yanzu ya jagoranci kafa ƙungiyar Triple R Kannwood da nufin tallata ƴansiyasa.

Ya yi waƙoƙi da dama da suka taimaka wajen tallata takarar Tinubu a 2023.

Haka kuma waƙarsa ta Omologo da ya yi wa Tinubu a wata ziyarar aiki da ya kai Katsina cikin shekarar da ta gabata na ci gaba da amo a fagen siyasar APC.

Musa Maisana'a

A baya-bayan nan Musa mai sana'a ya kasance ɗaya daga cikin ƴan Kannywood da suka fito ƙarara suna tallata ƴansiyasa.

Maisana'a wanda ya yi fice da iƙirarin tallata ayyukan mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu - a baya-bayan nan ya fito yana tallata Shugaba Tinubu na APC.

Tallar da Maisana'a ke yi na janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke sukarsa, da tallen da yake yi, duk kuwa da matsalar tsaron da arewacin Najeriya ke fuskanta.

To sai dai wasu na ganin abin da yake yi a masayin mafitarsa ta siyasa.

Sadiq Sani Sadiq

Ya kasance ɗaya daga cikin ƴan masana'antar da suka yi fice a sukar gwamnatin Shugaba Tinubu da yake zargi da gazawa a fannin yaƙi da matsalar tsaro.

Sadiq Sani Sadiq kan wallafa bidiyoyi a shafukansa na sada zumunta, inda yake kira ga al'ummar ƙasar su haɗa kai wajen kawar da gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.

Kodayake kawo yanzu Sadiq Sani Sadiq bai bayyana ɗantakarar da zai tallata a zaɓen 2027 da ke tafe ba, alamu sun nuna cewa yana tare da masu hamayya da Tinubu.

Tijjani Gandu

Ɗaya daga cikin ƴan Kannywood da ake ganin suna da tasiri a tallata ƴansiyasa shi ne Tijjani Gandu.

Fitaccen mawaƙin siyasar ya shahara ne da waƙar gwamnan jihar kano, Abba Gida-gida Abba, wadda ya yi a 2019.

Tun daga lokacin ne kuma ya ci gaba da yin tasiri a tallata ƴansiyasa musamman tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano.

Ko bayan da Gwamna Abba ya fice daga NNPP zuwa APC, ya yi wata waƙa mai take falle ɗaya ce, wadda ake ganin ta taimaka wajen tara wa Kwankwasiyya mabiya bayan ficewar Abba.

Tijjani Gandu ya yi matuƙar tasiri a tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya sa a yanzu haka Kwankwaso ya ba shi takarar majalisar wakilai na mazaɓar Dala.

Wace riba ƴan Kannywood ke samu da tallen?

Za a iya cewa suna samun gwaggwaɓar riba a wasu lokuta sakamakon tallata ƴansiyasar da suke yi.

Wasu daga cikinsu kan samu muƙamai idan aka kafa gwamnati, yayin da wasu kuma kan samu tallafi daban-daban.

Alal misali a Kano bayan tallata Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2023, gwamnan ya saka wa Abba El-Mustapha da muƙamin shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar.

Haka Shi ma Ali Nuhu bayan lokacin da ya kwashe yana tallen APC da Tinubu a zaɓen 2023, an saka masa da muƙamin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Bayan wanna an naɗa Nuhu Abdullahi Jagoran wata ƙungiyar gangamin wayar da kai game da shirin Shugaba Tinubu na Renew Hope, da ake kira Renew Hope Enlightment.

Rahama Sadau kuma ta samu shiga kwamitin bunƙasa zuba jari ta hanyar amfani da fasahar zamani wato Technical Committee of the Investment in Digital and Creative Enterprise programme (iDICE) wanda yake ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Shi ma fitaccen darakta a Kannywood, Sunusi Hafiz, wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya rabauta da muƙamin bai ba gwamnan Kano shawara na musamman a kan harkokin Kannywood.

Rabiatu Sulaiman Kurfi ita ce mai ba gwamnan Katsina, Dokta Dikko Raɗɗa shawara a kan kafofin sadarwa na zamani.

Bashir Lawandi Datti jarumi kuma furodusa a masana'antar Kannywood ya samu muƙamin kwamishinan albarkatun ruwa da makamashi.

Wanne tasiri Kannywood ke yi wajen tallata ƴansiyasa?

Tuni dai yanzu ƴan masana'antar suka bazama wajen tallata mutanen da suke goyon baya.

Ko a baya-bayan nan an ga wasu ƴan masana'antar a majalisar dokokin Najeriya, inda wasu ke ganin sun je ne da nufin nuna goyon bayansu ga jam'iyyar APC, kasancewar Rarara ne ya jagorance su.

Zuwan nasu ya janyo suka da dama daga wasu ƴan ƙasar, musamman a shafukan sada zumunta, inda suke zarginsu da goyon bayan APC, tare da watsi da halin rashin tsaro da ƙasar ke ciki.

To amma a wata hira da wata kafar yaɗa labarai, Rarara ya ce sun je majalisar ne domin zaburar da ƴan majalisar wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Wasu ƴan ƙasar da dama dai musamman masu amfani da shafukan sada zumunta na ganin cewa babu wani tasiri da tallar ƴan Kannywood ɗin za ta yi.

To amma Dr Kabiru Sufi, Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya ya ce ƴansiyasar ne ke ganin jaruman suna da tasiri a tallata su.

Ya ce kamar yadda a yanzu ta bayyana shafukan sada zumunta ke da tasiri sosai wajen tallata ƴansiyasa da ayyukansu, har ma suke naɗa mutanen da ke kula musu da shafukan, haka suka yanzu ƴan Kannywood ake ganin suna da tasiri.

''A yanzu ƴansiyasar sun yarda cewa mawaƙa da ƴan Kannywood na da tasiri wajen tallata ayyukansu da takararsu'', kamar yadda ya bayyana.

Dr Sufi ya ƙara da cewa hakan ne ya sa ƴan Kannywood ɗin suka bazama wajen karɓo tallace-tallacen ƴansiyasa.

Sai dai masanin siyasar kawo yanzu ba a gama tantancewa ko jaruman fina-finan za su yi tasiri wajen tallata ƴansiyasar ba.

''Amma dai batun waƙa an yarda tana tasiri, kuma duba da yadda ba a raba waƙa da wasan ƙwaiƙwayo, ya sa ake ganin za su yi tasirin, saboda su ƴan siyasar sun yarda da hakan'', kamar yadda ya bayyana.