Za a fi mayar da hankali kan batun tsagaita wuta a Lebanon a tattaunawarmu da Amurka - Iran

Asalin hoton, IRNA
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce batun tsagaita wuta a Lebanon shi ne za a fi mayar da hankali a kai kuma zai fi ɗaukar hankali a tattaunawar da za a yi tsakanin Iran da Amurka a Switzerland.
Baghaei ya bayyana haka ne a gab da fara tattaunawar, inda ya zargi Amurka da kasa tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon, yana mai cewa wannan batu zai zama muhimmin abin da za a tattauna.
Ya kuma ce Amurka, a matsayinta na abokin tattaunawa, tana da alhakin tilasta Isra’ila dakatar da hare-haren da take kai wa Lebanon.
A cewarsa, Iran ta riga ta cika nauyin da ke kanta na yarjejeniyar, yana mai jaddada cewa kowane ɓangare ya kamata ya bi alkawuran da aka ɗauka.










